Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa idan muka dubi tarihin rayuwa (sira) da maganganun Jagoranmu Shahidi da zurfin tunani, tare da nazarin kalamansu, lalle ɗaya daga cikin muhimman ginshiƙai a cikin shawarwarinsu na kullum shi ne jaddada riƙe bege (fata) a cikin al’umma ta hanyar ƙarfafa dogaro da kan ƙasa.
Haka kuma, halayensu da aikinsu sun yi matuƙar tasiri wajen ƙarfafa bege da ɗaga al’adar dogaro da kai a ƙasarmu, ta yadda abokai da maƙiya ma sun amince da wannan.
Wajibcin tsayin daka cikin mutunci a fuskantar maƙiyi
Hujjatul Islam Habib Baba’i, mai aikin al’adu kuma mai bincike a Hauza, ya ce: “Iran mai ƙarfi tana samuwa ne ta hanyar dogaro da kai da kuma ƙarfafa bege, kuma in sha Allah a gaba ma wannan zai haifar da manyan sauye-sauye.” Ya bayyana cewa Jagoranmu Shahidi kullum yana jaddada muhimmanci da larurar ƙarfafa al’adar dogaro da kai da bege ga gaba. A ganinsa, ƙasar da ba ta da mutunci da dogaro da kai za ta tilasta ta miƙa wuya a gaban barazana da matsin lamba na maƙiya. Tarihin bil’adama cike yake da labarin al’ummai da gwamnatoci da suka mika kai saboda rashin ƙwarin gwiwar ƙasa, daga ƙarshe kuma suka fada cikin mulkin mallaka da dogaro da wasu.
Ya ƙara da cewa: “Da taimakon Allah, a ƙarƙashin jagorancin hikima na jagororin Juyin Juya Hali, mutanen ƙasarmu ba su kasance haka ba.” Ya ce gaskiyar magana ita ce al’ummar Iran a tsawon tarihi sun tsaya cikin mutunci da imani a fuskantar Rasha da Ingila, a gaban mamayar Mongol da Iskandar, kuma a zamani na yau a gaban Amurka, Isra’ila da Saddam. Musamman bayan nasarar Juyin Juya Halin Musulunci, wannan tsayin daka ya ƙara bayyana, kuma a “yaƙe-yaƙen tilas” da aka sha, an ga wannan a fili; har ma ’yantattun mutane a duniya sun yaba.
Me ya sa har yanzu muke buƙatar ƙarfafa bege?
Hujjatul Islam Baba’i ya ce: “Iran mai ƙarfi ana gina ta ne ta hanyar dogaro da kai da ƙarfafa bege.” Duk da wasu matsaloli da ƙaranci, bai kamata su sa mu manta da imani da ƙwarewarmu ba. Ya ce: "idan muka rubuta jerin nasarorin Jamhuriyar Musulunci a cikin shekaru 47 da suka wuce—duk da barazana, takunkumi, matsin lamba da yaƙe-yaƙe—lalle jerin zai yi tsawo sosai, kuma wannan nasarori shaida ce ta babbar damar al’ummar Iran. Amma har yanzu domin cimma manufofinmu da gina Iran mai ƙarfi da ɗaukaka, muna buƙatar kula da ginshiƙai biyu tare, ƙarfafa dogaro da kai da ƙara bege a cikin al’umma."
Ya tunatar da cewa Jagoranmu Shahidi a cikin Bayanan Mataki na Biyu na Juyin Juya Hali ya jaddada cewa akwai tazara tsakanin halin da ake ciki da manufa ta ƙarshe. Sun ce dole ne matasa muminai masu ƙwazo su cike wannan tazara; daga cikin sharuddan cimma hakan akwai sanin maƙiyi, riƙe bege da samar da bege, dogaro da kai, da aiki tukuru har sai an kai ga kololuwar ɗaukaka. Kuma a sarari: da imani ga Allah Madaukaki, dogaro da ƙwarewarmu, tare da aiki ba tare da kasala ba, za mu kai ga manyan manufofi da izinin Allah.
Bukatar amsa tambayoyi da damuwar sabon ƙarni
Dr. Mona Jami-Pour, mamba a kwalejin jami’ar Hazrat Ma’asuma (AS), ta ce: "a shekarun baya-bayan nan ɗaya daga cikin manyan dabarun yaɗa labaran maƙiyi shi ne rage ruhin fata a cikin jama’a, musamman a tsakanin matasa." Ta ce: "daga cikin muhimman abubuwan da Imam Shahidi ya kula da su a cikin Bayanan Mataki na Biyu—kuma yanzu gadon tunani da ruhi ne a gabanmu—shi ne ƙarfafa fata da gina ruhin fata a cikin al’umma; har ma sun kira “jihadin samar da fata” a matsayin jihadi na farko kuma mafi tushen gaske a wannan zamani."
Ta ƙara da cewa: "domin ƙarfafa fata ga gaba, dole ne a saurari maganganun matasa da buƙatunsu na gaskiya, musamman matasan da suka yi karatu kuma masu baiwa. Akwai tambayoyi da ruɗani a zuciyar sabon ƙarni da ya kamata a yi bayani a sarari game da su. A nan ne kafafen yaɗa labarai ya kamata su aiwatar da aikin wayar da kai da zama gada tsakanin jama’a da masu alhaki—kuma muhimmin ɓangare na “jihadut tabyiin” ya shafi haka.
Dole a yi amfani da ƙarfin kafafen yaɗa labarai yadda ya dace
Ta ce ya zama dole a yi amfani da damar kafofin watsa labarai na ƙasa yadda ya kamata domin gyara ra’ayoyi da aka kafa bisa kuskure, waɗanda galibi suna ƙarƙashin tasirin shisshigi da shigar da tunani na kafafen maƙiya.
Ta ƙara: "babu shakka kafafen watsa labarai na yammacin duniya da masu adawa da ƙasar Iran suna yin zaɓen labarai da juya alkibla, suna mai da hankali kan wasu batutuwa bisa tsari da aka riga aka tanada." Ta ce bayan fara “Yaƙin Ramadan” ya bayyana cewa yawancin abin da suke yaɗawa ƙarya ce, ba bayyana gaskiya ba.
Ta tunatar: "a wannan lokaci mai sarkakiya, muna matuƙar buƙatar gabatar da nasarori da ci gaban ƙasa tare da bayyana raunana da gibba. Ta ce abin takaici, sabuwar ƙarni ba su da isasshen sani game da manyan ci gaban kimiyya a ƙasar; alhali a wasu fannoni yanzu muna cikin ƙasashe 5 ko 10 na farko a duniya, kuma abin takaici ne idan ba a isar da wannan ga jama’a—musamman matasa—ta hanyar da ta ja hankali da salo na fasaha ba.
Imani da yadda Imam Shahidi ya yarda da basirar matashin Iran
Ta bayyana cewa Imam Khamene’i (Shahidi) yana da zurfin imani da basira da ƙwarewar matasan Iran, kuma ya yi imanin cewa matasa suna da ƙarfi na musamman a fannin ilimi, fasaha, da imani da ƙima—ya kamata a yi anfani da su sosai. Haka kuma masa'ulai ya kamata su samar da yanayi da zai sa waɗannan damar su bayyana a aikace.
Ta ƙara da kawo maganarsa: “Ƙasa ana iya gyara ta da yaƙi, da siyasa, da tattalin arziki da al’adu; amma abin da yake da matuƙar muhimmanci, kuma ni kullum ina tunani a kai, shi ne yadda za mu sa matasa su kasance masu fata da ƙwazo.”
Wannan, in ji ta, yana nuna yadda tsarinsa ya kasance na ba da fata da dogaro ga sabuwar ƙarni.
A ƙarshe ta ce: ya jaddada tarbiyya ta gari da koyarwa bisa imani, wanda hakan ke taimaka wa matasa su ci gaba a ilimi kuma su bunƙasa a ɗabi’a da ruhaniya.
Rahoto: Sayyid Muhammad Mahdi Mousavi
Ra'ayinka