Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito, ga cikakken sakon Ayatullah A‘arafi, shugaban Hauzozin Ilimi, na bayyana mubaya’ar Hauza da ‘yan Hauza ga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamenei:
بسم الله الرحمن الرحیم
"یَا أَیُّهَا الَّذِینَ آمَنُوا أَطِیعُوا اللَّهَ وَأَطِیعُوا الرَّسُولَ وَأُولِی الْأَمْرِ مِنْکُمْ"
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai
“Ya ku wadanda kuka yi imani! Ku yi biyayya ga Allah, ku yi biyayya ga ManzonSa, da kuma masu iko daga cikinku.”
Wilayatul Faqih itace bishiya mai albarka wadda ta ci gaba daga wilayar Ahlul‑Baiti (AS), wacce Imam mai girma na juyin juya hali ya gabatar da ita a sabon tsari da ya dace da bukatun shugabanci a wannan zamani. A tsawon kusan rabin karni ta kasance cibiyar jagorantar Juyin Juya Halin Musulunci.
Yayin da muke tunawa da shahidanmu masu daraja, musamman Imam Shahid Ayatullah al‑Uzma Khamenei (Q), muna kuma yi wa al’ummar Iran mai girma, rundunonin sojoji masu daraja, da kuma bangarorin gwagwarmaya (Axis of Resistance) fatan samun nasara a Yaƙin Ramadan. Haka kuma muna sake taya ku murnar zabenku a matsayin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, wanda ya zama sanyayar zuciya ga al’ummar da ke cikin jimami, kuma ya sake tayar da ruhin juyin juya hali a tsakanin jama’a.
Ina kuma mika sakon taya murna tare da bayyana biyayya da mubaya’a daga dukkanin rukunonin malamai da daliban Hauza, manyan mutanen Hauza, da cibiyoyin ilimi da na Hauza, tare da bin shawarwarin manyan Maraji’ai zuwa gare ku. Alhamdulillahi kuna da siffofi masu girma kamar ilimi, ijtihadi da hikima. Malaman Hauza za su kasance koyaushe a gaba wajen aiwatar da manufofin Juyin Juya Halin Musulunci da kuma bunkasa Hauza, bisa ga shawarwarinku, in sha Allah.
Ina rokon Allah Madaukakin Sarki ya kara muku nasara da taimako wajen jagorantar wannan tsari mai tsarki na Musulunci da kuma ciyar da manufofin Juyin Juya Halin Musulunci da burin Imam Khumaini (R) da Imam Shahid (R) gaba.
Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu
Alireza A‘arafi
Shugaban Hauzozin Ilimi.
Ra'ayinka