A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, jerin darussan sanin Mahdawiyya ƙarƙashin taken "Zuwa Ga Al'umma Mai Manufa", da nufin yaɗa koyarwa da ma'arifofin da suka shafi Imam Zaman (A.F), ana gabatar muku da shi:
Haihuwar Sa
Imami na ƙarshe na mabiya mazahabar Shi'a, kuma magaji na sha biyu na Manzon Allah (S.A.W.A), an haife shi ne a wayewar garin Jumma'a, tsakiyar watan Sha'aban, shekara ta 255 Bayan Hijira [868 Miladiyya] a garin Samarra, ɗaya daga cikin biranen ƙasar Iraƙi.
Iyayen Sa
Mahaifinsa mai girma shi ne jagora na sha ɗaya na mabiya Shi'a, Hazrat Imam Hassan al-Askari (A.S). Mahaifiyarsa kuma wata mace ce mai daraja mai suna "Narjis", wadda akwai ruwayoyi daban-daban game da asalinta. A cewar wata ruwaya, ita ɗiyar "Yashu'a" ce, ɗan sarkin Roma, kuma mahaifiyarta ta fito ne daga zuriyar "Sham'un" (Simon), wasiyyin Annaba Isa (A.S). A bisa wannan ruwayar, Narjis ta musulunta ne bayan wani mafarki mai ban mamaki, kuma ƙarƙashin jagorancin Imam Askari (A.S), ta sanya kanta a cikin dakarun Roma da suka fita yaƙi da musulmai, inda ta zama fursuna. Imam Hadi (A.S) ya aika aka sayo ta aka kawo ta Samarra.
Akwai wasu ruwayoyin kuma, amma abin da yake da muhimmanci shi ne cewa Hazrat Narjis (S.A) ta zauna na wani lokaci a gidan Hakima Khatun (S.A) — ɗaya daga cikin yayun Imam Hadi (A.S) — inda ta sami tarbiya da koyarwa a hannunta, kuma tana samun girmamawa sosai daga gare ta.
Hazrat Narjis (S.A) ita ce matar da Manzon Allah (S.A.W.A), Amirul Muminina (A.S), da Imam Sadiq (A.S) suka yaba mata tun shekaru da dama kafin a haife ta, kuma aka ambace ta a matsayin fiyayyar bayi kuma shugabarsu.
Haka kuma, an kira mahaifiyar Imam Zaman (A.F) da wasu sunaye kamar: Sawsan (Susan), Rayhana, Malika (Mulaika), da Saiqal (Saqil).
Suna, Alkunya, da Laƙabi
Sunan Imam Zaman (A.S) da kunyarsa iri ɗaya ne da na Manzon Allah (S.A.W.A). A wasu ruwayoyin, an hana ambatar sunansa na asali har sai lokacin bayyanarsa.
Fitattun laƙabobinsa sumni: Mahdi, Qa'im, Muntazar, Baqiyyatullah, Hujjat, Khalaf-us-Salih, Mansur, Sahibul Amr, Sahibul Zaman, da Waliyyul Asr. Wanda aka fi sani a cikinsu shi ne "Mahdi".
Kowane ɗaya daga cikin waɗannan laƙabobi yana ɗauke da sako na musamman:
- Ana kiran sa "Mahdi" domin shi wanda aka shiryar ne mai kiran mutane zuwa ga gaskiya.
- Ana kiran sa "Qa'im" domin zai tashi don tsayar da gaskiya.
- Ana kiran sa "Muntazar" domin kowa yana jiran bayyanarsa.
- Ana kiran sa "Baqiyyatullah" domin shi ne ragowar hujjojin Allah kuma ma'ajiyar Ubangiji ta ƙarshe.
- "Hujjat" na nufin shaidar Allah a kan halitta, kuma "Khalaf-us-Salih" na nufin magaji nagari na waliyan Allah.
- Shi "Mansur" ne domin Allah yana taimakonsa, kuma "Sahibul Amr" ne domin shi ke da alhakin kafa gwamnatin adalci ta Ubangiji.
- "Sahibul Zaman da Waliyyul Asr" kuma na nufin shi ne shugaba kwaya daya rak kuma mai mulkin wannan zamani.
Rayuwar Imam Mahdi (A.S) ta kasu kashi uku:
1. Zamanin Ɓuya (Ikhtifa): Wannan shi ne rayuwar sa ta ɓoye tun daga lokacin haihuwarsa har zuwa lokacin shahadar mahaifinsa Imam Askari (A.S).
2. Lokacin Ghaiba: Wannan lokacin ya fara ne tun daga lokacin shahadar Imami na sha ɗaya (A.S), kuma zai ci gaba har zuwa duk lokacin da Allah ya nufi bayyanarsa.
3. Zamanin Bayyana: Bayan ƙarewar lokacin gaiba da kuma nufin Mahaliccin duniya, Imami na sha biyu (A.S) zai bayyana, kuma zai cika duniya da alkhairai da kyawawa. Babu wanda ya san lokacin bayyanar wannan alkawari da ake jira (Muntazar), kuma an ruwaito daga Imamul Asr (A.S) cewa: "Waɗanda suke ƙayyade lokaci na musamman don bayyanarsa, maƙaryata ne."
Wannan tattaunawa za ta ci gaba...
An ciro daga littafin "Negin-e Afarinesh", tare da ɗan gyara kaɗan.
Ra'ayinka