Laraba 25 Yuni 2025 - 22:13
Malamai da Fitattun Mutane a Duniyar Musulunci Sun Fitar da Sanarwar Allah-Wadai da Hare-Haren Isra’ila Kan Iran

Hauza/ Malamai da fitattun mutane a duniyar Musulunci sun fitar da sanarwar Allah-wadai da hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa da gwamnatin Isra’ila ta kai wa Iran, waɗanda suka yi sanadin shahadar manyan kwamandoji, masana kimiyya da fararen hula marasa laifi. Sun kuma yi kira ga haɗin kan al’ummar Musulmi.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, sanarwar ta ƙunshi Allah-wadai da hare-haren Isra’ila kan Iran, da kuma kiran haɗin kan al’ummar Musulunci. Ga fassarar cikakkiyar sanarwar:

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Ƙai.

الَّذِينَ آمَنُوا يُقَاتِلُونَ فِي سَبِيلِ اللَّهِ وَالَّذِينَ كَفَرُوا يُقَاتِلُونَ فِي سَبِيلِ الطَّاغُوتِ فَقَاتِلُوا أَوْلِيَاءَ الشَّيْطَانِ إِنَّ كَيْدَ الشَّيْطَانِ كَانَ ضَعِيفًا

Mu, malaman al’ummar Musulunci, muna bayyana matuƙar Allah-wadai da mamayar da gwamnatin Isra’ila ta kai kwanan nan kan ƙasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, da kai hare-hare kan manyan kwamandojin da ke kare tsaro da gwagwarmaya, da masana kimiyyar nukiliya, da kuma kashe fararen hula da mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba. Muna yin Allah-wadai da waɗannan ayyuka cikin matuƙar baƙin ciki da fushi.

1. Gwamnatin Isra’ila: Maƙiyiyar ɗan’adam da gaskiya

Hare-haren baya-bayan nan sun bayyana ainihin fuskar gwamnatin Isra’ila mai aikata laifuka. Wannan gwamnati ba maƙiyiyar Falasɗinu kaɗai ba ce, a’a, maƙiyiyar dukkan al’ummar Musulunci ce, har ma da adalci da mutuntaka a duniya.

Kai hari kan masana kimiyya da kwamandojin tsaron Iran wani yunƙuri ne na banza da ake yi domin dakatar da ci gaba da samun ’yancin kai a fannonin kimiyya da soja na al’ummar Iran.

2. Wannan yaƙi ne tsakanin Musulunci da kafirci

Muna bayyana cewa, abin da ke faruwa a yau fagen fafatawa ne tsakanin gaskiya da ƙarya, Musulunci da kafirci, da kuma zalunci da adalci.

Gwamnatin Isra’ila da masu mara mata baya suna cikin ɓangaren ƙarya, yayin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take a sahun gaba na al’ummar Musulunci wajen kare manufofin Alƙur’ani, Falasɗinu, gwagwarmayar adalci da mutuncin ɗan’adam.

3. Ya zama wajibi al’ummar Musulunci su tashi tsaye

Ya zama wajibi ga malaman addini, jami’an ilimi, fitattun masana da sauran al’ummar Musulmi su fita daga halin ko-in-kula da rarrabuwar kawuna, su tashi tsaye domin taimakon waɗanda ake zalunta ta hanyar haɗin kai, wayar da kai da ɗaukar matakan da suka dace.

A yau, kare Iran yana nufin kare Musulunci; kare tsaron Musulmi, mutuncin Qudus da kuma makomar al’umma guda ta Musulunci.

4. Busharar Allah game da nasarar gaskiya

Muna da imani da tabbatattun alkawuran da Alƙur’ani ya yi:

إِنْ تَنْصُرُوا اللَّهَ يَنْصُرْكُمْ وَيُثَبِّتْ أَقْدَامَكُمْ

Ma’ana: "Idan kuka taimaki (addinin) Allah, Shi ma zai taimake ku, kuma Ya tabbatar da didiganku." (Suratu Muhammad: Aya ta 7).

Nasarar ƙarshe za ta kasance ga masu imani. Halakar wannan gwamnatin da ta ƙwace ƙasa da masu mara mata baya na shaiɗanci wani alkawari ne na Allah, kuma lokacin cikar wannan alkawari yana gabatowa.

5. Neman tabbatar da adalci a duniya

Muna kira ga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da cibiyoyin kare haƙƙin ɗan’adam da su karya shirunsu na wulaƙanci, su rubuta waɗannan hare-hare a matsayin laifukan yaƙi, sannan su hukunta waɗanda suka aikata su ta hanyar doka.

Kai hari kan ƙasar da take da ’yancin kanta babban take haƙƙin Yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya ne da dokokin ƙasa da ƙasa.

A ƙarshe, yayin da muke addu’a da zuciya ɗaya domin Allah Ya ba wa masu gwagwarmayar kare gaskiya nasara, Ya kuma jiƙan shahidan gwagwarmaya, muna jaddada cewa jinin shahidai ba zai tafi a banza ba. A maimakon haka, zai kasance kamar fitila da za ta haskaka hanyar ’yantar da al’ummar Musulunci.

وَلَيَنْصُرَنَّ اللَّهُ مَنْ يَنْصُرُهُ ۗ إِنَّ اللَّهَ لَقَوِيٌّ عَزِيزٌ

"Lallai Allah zai taimaki wanda ya taimaki addininsa. Haƙiƙa Allah Mai ƙarfi ne, Mabuwayi." (Suratul Hajji: Aya ta 40).

Amincin Allah ya tabbata ga wanda ya bi shiriya.

Sunayen waɗanda suka sanya hannu kan sanarwar

Ayatullah Alireza A’arafi, shugaban Makarantun Hauza.

Hujjatul Islam wal Muslimin Shahriyari, Sakatare-Janar na Ƙungiyar Ƙarfafa Haɗin Kan Mazhabobin Musulunci.

Hujjatul Islam wal Muslimin Ghulam Ali Safa'i Bushahri, wakilin Waliyyul Faƙih a lardin Bushahr.

Sayyid Muhammad Muhammad Haidari, Limamin Juma’a na Masallacin Al-Khulani a Bagadaza.

Shaikh Khalid Al-Mulla, shugaban Ƙungiyar Malaman Iraki.

Hujjatul Islam wal Muslimin Sayyid Ali Qazi Askar, shugaban kula da Haramin Sayyid Abdul'azim Hasani.

Hujjatul Islam wal Muslimin Sa'id Reza Amili, shugaban Majalisar Sauyi da Ɗaukaka Ilimin Bil’adama.

Hujjatul Islam wal Muslimin Muhammad Qumi, shugaban Hukumar Yaɗa Addinin Musulunci.

Hujjatul Islam wal Muslimin Ali Abbasi, shugaban Jami’ar Al-Mustafa ta Duniya.

Hujjatul Islam wal Muslimin Mustafa Rustami, shugaban Cibiyar Wakilcin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci a Jami’o’i.

Sayyid Muhammadi Abu Saleh Abdulqadir Al-Hasani Al-Alusi, shugaban Majalisar Malaman Ƙungiyar Al-Ribat Al-Muhammadi.

Shaikh Muhammad Nimr Ahmad Zaghmut, shugaban Majalisar Musulunci ta Falasɗinu a Lebanon da sauran ƙasashen waje.

Sheikh Hassan Abdullah, shugaban Ƙungiyar Malaman Musulmi ta Lebanon.

Sheikh Ghazi Hanine, shugaban kwamitin amintattu na Ƙungiyar Malaman Musulmi ta Lebanon.

Dakta Hussain Muhammad Qasim, shugaban Majalisar Malaman Falasɗinu.

Dakta Muhammad Saleh Al-Maw’id, mai magana da yawun Majalisar Malaman Falasɗinu a Lebanon da ƙasashen waje.

Sheikh Zuhair Al-Ja’id, babban mai tsara ayyukan Ƙungiyar Gwagwarmayar Musulunci.

Sheikh Abdulmun’im Al-Zain, daraktan Cibiyar Zamantakewar Musulunci a Senegal.

Sheikh Abdullah Al-Daqqaq, shugaban Makarantar Hauza ta Bahraini a Qum.

Sheikh Samih Uthman Sulaiman Muhammad, malami daga Jami’ar Al-Azhar kuma limami a Ma’aikatar Awƙaf ta Masar.

Imam Muhammad Al-Asi, Limamin Juma’a a Washington.

Mamosta Mulla Qadir Qadiri, Limamin Juma’a na Pawa.

Sheikh Muhammad Al-Za’abi, shugaban Ofishin Wa’azi na Ƙungiyar Tauhidi ta Musulunci a Lebanon.

Sheikh Abu Bakr Mishlawi, mamba a jagorancin Ƙungiyar Gwagwarmayar Musulunci a Lebanon.

Dakta Sheikh Saleh Al-Kashif, mai kula da hulɗa da jama’a na Taron Masu Wa’azin Falasɗinu.

Sheikh Sa'id Qasim, shugaban Hukumar Musulunci ta Falasɗinu.

Sayyid Murtadha Murtadha Amili, mamba a Babbar Majalisar Ƙungiyar Ahlul Baiti.

Sheikh Muhammad Qadura, daraktan Cibiyar Badr Al-Kubra.

Dakta Salman Al-Audi, sakataren Taron Masu Wa’azin Falasɗinu.

Dakta Umar Abdullah Al-Shalah, mukaddashin mai kula da ayyukan Taron Masu Wa’azin Falasɗinu a Turkiyya.

Ridwan Al-Muhya, shugaban Ƙungiyar Musulunci ta Shafi’iyya a Yemen.

Dakta Abdulrahman bin Ali Al-Dala’ Al-Hasani Al-Hashimi, shugaban Cibiyar Bincike da Nazarin Haɗin Kan Musulunci a ƙasashen Sham.

Sheikh Ahmad Gharib, shugaban Hukumar Aiki domin Haɗin Kai da Sauyi.

Sheikh Mustafa Milas, shugaban Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasa a Lebanon.

Sheikh Al-Sharif Walid Al-Idrisi, mataimakin Mufti na yankin Volgograd a Rasha.

Sayyid Muhammad Al-Fadhil Hamadoush.

Hujjatul Islam wal Muslimin Sayyid Mufid Kouhsari, mataimakin hulɗa da ƙasashen waje na Makarantun Hauza.

Maulawi Habiburrahman Motahari, shugaban Makarantar Addinin Ahnaf ta Khaf.

Muhammad Saleh Ansari, malamin Hauza.

Sheikh Kifah Muhammad Batta, Mufti na yankin Volgograd kuma mataimakin Mufti na Ƙungiyar Addinin Musulman Rasha.

Sheikh Hussain Shuraid Al-Shuli, mamba a babban kwamitin Ƙungiyar Malaman Musulmi.

Sheikh Adel Al-Turki, shugaban Ƙungiyar Taron Haɗin Kai domin Haɗin Kan Zamantakewa da Ayyukan Alheri.

Sayyid Ahmad Shahata Al-Hasani Al-Azhari, daraktan Riwaƙin Imam a Masar.

Ahed Mustafa Al-Atawi, shugaban Gidauniyar Nazari a Indonesia.

Fatima Al-Sumadi, mai bincike kuma malamar jami’a.

Farfesa Hussein Al-Dairani, wakilin Majalisar Ƙasa da Ƙasa ta Ahlul Baiti (AS) a Australia.

Sayyid Fadi Al-Sayyid, shugaban Cibiyar Al-Umma Al-Wahida ta Nazarin Tunani da Dabarun Aiki.

Hassan Qana’atli, shugaban Ƙungiyar Ƙungiyoyin Ahlul Baiti a Turkiyya.

Sayyid Haidar Aftab Rizvi, mai gabatar da huɗubar Juma’a a Cape Town.

Sheikh Suhaib Habli, shugaban Ƙungiyar Ulfa.

Sheikh Khalil Rizq, mai kula da hulɗar ƙasa da ƙasa na Hizbullah.

Sayyid Izzuddin Bal’id Al-Shaikhi Al-Idrisi Al-Hasani, shugaban ƙungiyar zuriyar Ahlul Baiti a Libya.

Sheikh Mazen Al-Sharif, masanin dabarun siyasa daga Tunisiya.

Mazen Al-Zaidi, daraktan Cibiyar Al-Masar ta Iraki domin Nazari.

Sheikh Tawfiq Hassan Alawiyya, marubuci kuma mai binciken ilimin Musulunci, mamba a Ƙungiyar Malaman Musulmi a Lebanon.

Dakta Muhammad Hisham Sultan, malamin Akida da Falsafa, tsohon mataimakin shugaban Jami’ar Ahlul Baiti a Jordan.

Sayyid Adnan Ahmad Yahya Al-Junaid, mamba a babbar hukumar Ƙungiyar Malaman Yemen kuma shugaban Taron Tasawwuf na Musulunci a Yemen.

Sheikh Shafiq Jeradi, shugaban Cibiyar Al-Ma’arif Al-Hikmiyya kuma babban mai kula da shafin Iqtida’ Al-Muqawama.

Sheikh Maher Hammoud, shugaban Ƙungiyar Malaman Gwagwarmaya ta Duniya.

Sheikh Tariq Rashid, mai kula da Taron Masu Wa’azin Falasɗinu a Lebanon.

Sayyid Muhammad Baqir Al-Qabanchi, shugaban Jami’ar Imam Mahdi (AS) a Najaf.

Sheikh Mustafa Hussein Abu Rumman, limami kuma mai gabatar da huɗuba a wani masallaci a Amman, Jordan.

Sheikh Nizar Sa’id, shugaban Ƙungiyar Cibiyoyin Al’adu na Imam Khumaini (RA) a Lebanon.

Sayyid Shafqat Hussein Shirazi, mai kula da harkokin ƙasashen waje na Jam’iyyar Majalisar Haɗin Kan Musulmi ta Pakistan.

Sheikh Raja Nasir Abbas Ja’fari, shugaban Jam’iyyar Majalisar Haɗin Kan Musulmi kuma mamba a Majalisar Dattawan Pakistan.

Sheikh Qadir Akars, shugaban Majalisar Malaman Ahlul Baiti kuma daraktan Cibiyar Al-Kawthar a Turkiyya.

Hujjatul Islam Sayyid Jawad Wahidi.

Dakta Ansiyeh Khazali, malamar Hauza da jami’a.

Sheikh Hussein Al-Daihi, mataimakin babban sakataren Ƙungiyar Al-Wefaq ta Ƙasa ta Musulunci a Bahrain.

Salman Al-Husseini Al-Nadwi, shugaban Ƙungiyar Haɗin Kan Indiya.

Sheikh Muhammad bin Hamouda, daga Tunisiya.

Mamosta Iqbal Bahmani, mamba a Majalisar Kwararrun Jagoranci.

Sheikh Muhammad Zaman Zamani, Limamin Juma’a na Oz.

Hujjatul Islam Sayyid Fadhil Mousavi Jabiri, malamin manyan darussa a Makarantar Hauza ta Najaf.

Mahdi Ghulamali, sakataren Majalisar Tsare-tsaren Makarantun Ilimin Addinin Ahlus-Sunna.

Sheikh Muhammad Ali Amini, shugaban Makarantar Addini ta Bastak.

 Hujjatul Islam wal Muslimin Hujjat Gonabadi Nejad, shugaban Hauza.

Akhund Qurban Muhammad Onq, Limamin Juma’a na Bandar Torkaman.

Sayyid Mukhtar Hashemi, mai fafutukar al’adu daga Ahlus-Sunna.

Sheikh Khalil Afra, shugaban Hukumar Fatawa ta Ahlus-Sunna a lardin Bushehr.

Maulawi Yahya Fazeli, shugaban Hauzar Darul-Ulum.

Mamosta Dakta Muhammad Amin Rasouli, malamin Hauza.

Hujjatul Islam wal Muslimin Mahdi Farmanian, malamin Hauza.

Ali Yeral, wanda ya kafa kuma shugaban Gidauniyar Ahlul Baiti ta Alawi a Turkiyya.

Abdussalam Imami, Limamin Juma’a na Mahabad.

Hujjatul Islam Muhammad Baqir Farzaneh, shugaban Babbar Majalisar Hauza ta Khorasan.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha