A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza da aka samu daga shafin Ofishin Sayyid Zakzaky (H), yayin wannan ziyara, tawagar, ƙarƙashin jagorancin Shaikh Imam Rashid ta bayyana godiyarta ga Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya da kuma ƴan uwa bisa gudummawar da suka bayar wajen gudanar da jana'izar marigayi Shaikh Yahaya Masussuka, wanda ƴan ta'adda suka kashe makonni kaɗan da suka gabata.
Haka kuma, tawagar ta nuna godiya bisa saƙon ta'aziyyar da Shaikh Zakzaky ya gabatar, tare da wakilcin da ya aika zuwa taron zaman lafiya da aka gudanar.
A nasa jawabin, Shaikh Zakzaky ya yi musu bayani kan muhimmancin haɗin kan al'ummar Musulmi, tare da bayyana hanyoyin da ya kamata su bi wajen ci gaba da gudanar da Da'awah bisa koyarwar Alƙur'ani mai girma, ta hanyar da ta dace.
A ƙarshen ganawar, Jagoran ya miƙa wa Shaikh Imam Rashid da kuma Alaramma, wanda ke kula da tarba da baƙuncin baƙin marigayi Shaikh Masussuka, kyaututtuka biyu. Kyaututtukan sun haɗa da littafin Hikimomin Imam Ali da kuma Nahjul Balagha, sai kuma wani zobe wanda aka rubuta cikakken Alƙur'ani mai girma a jikinsa.
A ƙarshe, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi addu'ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya karɓi shahadar marigayi Shaikh Yahaya Masussuka, Ya kuma sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa.







Ra'ayinka