Jummaʼa 16 Oktoba 2026 - 21:24
Laburaren Fatimiyya Na Yin Hidima Ta Musamman Ga Makafi

Hauza/ Laburaren Makafi na Haramin Sayyida Fatima Ma’asuma (SA) yana da littattafai sama da 270 da aka rubuta da haruffan Braille, waɗanda suka ƙunshi batutuwa daban-daban da suka haɗa da Alƙur’ani, addu’o’i, ziyarce-ziyarce, tarihin rayuwar Ahlul Baiti (AS), waƙoƙi, hukunce-hukuncen addini, aƙida da labarai. Ana ba wa maziyarta makafi damar amfani da littattafan ba tare da yin rajista ba.,

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya rawaito cewa, Laburaren Fatimiyya da ke Haramin Sayyida Fatima Ma’asuma (SA), domin samar da hidima ga dukkan masu ziyara, ya kafa wani sashe na musamman ga makafi a Riwaƙin (ɗakin) Allama Majlisi, wanda yake a gefen arewacin harabar filin taron Imam Khumaini (RA).

Wannan sashe na musamman yana da littattafai sama da 270 da aka rubuta da haruffan Braille, waɗanda suka ƙunshi batutuwan Alƙur’ani, tarihin rayuwar Ahlul Baiti (AS), addu’o’i, ziyarce-ziyarce, waƙoƙi, hukunce-hukuncen addini, aƙida, labarai da sauran fannoni.

Daga cikin littattafan da ake da su a wannan sashe akwai cikakken littafin Nahjul Balagha mai juzu’i 10, kwafi uku na Alƙur’ani mai girma, kowannensu yana da juzu’i 10, inda aka haɗa kowane juz’i uku a cikin littafi guda. Haka kuma, akwai littafin Mafatihul Jinan, zaɓaɓɓun addu’o’i daga Mafatihul Jinan, littafin gabatarwa kan Usulud Din, littafin ƙwarewar sadarwa mai inganci bisa koyarwar Imam Rida (AS), tarihin rayuwar Imam Husaini (AS), da kuma littafin Durrul Isma, wanda ya ƙunshi taƙaitaccen bayani kan tarihin rayuwar Sayyida Fatima Ma’asuma (SA), da sauran littattafai.

Amfani da littattafan Braille da ke wannan sashe ba ya buƙatar yin rajista. Masu ziyara za su iya karanta littattafan a cikin laburaren da kansa, ko kuma su karɓi littattafan aro domin amfani da su a wajen laburaren.

Haka kuma, an gudanar da wasu sauye-sauye a tsarin wurin laburaren domin faɗaɗa sararin da ake da shi da kuma inganta yanayin da masu amfani da shi suke karatu.

Hukumar laburaren ta bayyana cewa, waɗanda suke son bayar da gudummawar littattafai za su iya ba da littattafan da aka rubuta da haruffan Braille ga sashe na musamman na makafi, baya ga littattafan da suke bayarwa ga babban Laburaren Fatimiyya.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha