A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Mamba a Kwamitin Kimiyya na Cibiyar Ilimi da Bincike ta Imam Khumaini (r.a), yayin da yake fayyace manufar "Lissafin Ubangiji" (Muhasabatul Ilahiyya), ya bayyana cewa: "Lissafin Ubangiji yana nufin auna al'amura da tantance su bisa dokoki da sunnonin Allah tabbatattu kuma marasa sauyawa, wadanda Allah Ya shimfida a cikin halitta da kuma makomar 'yan'adam; lissafin da ya wuce ma'aunan abin duniya da na zahiri, wanda ya ginu a kan dalilai na ruhi kamar imani, takawa, juriya da kuma taimakon Allah, wanda ke tabbatar da alkawarin Allah na taimakon rundunar gaskiya."
Wannan malamin Hauza da Jami'a ya ƙara da cewa: "Lissafin Ubangiji yana nuni ne ga ka'idojin da ke tafiyar da tsarin halitta wadanda ke aiki da cikakken tsari ba tare da kuskure ko saɓawa ba, wadanda Alkur'ani ya kira su da 'Sunnonin Allah'. Bisa wannan tsari, kyawawa ko munanan ayyukan mutane a matakin daidaiku da na al'umma suna yin tasiri kai tsaye a kan makomarsu, kuma su ne ke zama silar samun rabauta ko taɓewa, da kuma nasara ko faɗuwa."
Ya fayyace cewa: "Lissafin Ubangiji yana aiki ga wata al'umma a lokacin da wannan al'umma ta yi aiki bisa sunnonin Allah marasa sauyawa kuma ta sanya su a gaba; a karkashin wannan ma'auni, karfi na hakika ba a auna shi da yawan kayan aikin yaki ko adadin kudaden waje da ke asusun ajiya, a'a, ana auna shi ne da girman riko da wadannan sunnoni."
Imani, Taƙawa Da Juriya Na Daga Cikin Ginshikan Karfin Al'umma
Hujjatul Islam wal Muslimin Baƙirzadeh, yayin da yake bayyana dalilan samun ƙarfi da nasarar al'ummomi, ya ce: "Alkur'ani mai girma da hadisai sun lissafa dalilai da dama na samun karfi da nasarar al'umma, wanda daya daga cikinsu shi ne ingantaccen imani da asalin dabi'ar Ubangiji (Hutiyya Ilahiyya)."
Ya ci gaba da cewa: "Wannan asali na Ubangiji yana samuwa ne ta hanyar imani, kuma karfin al'ummar da ta yi imani da alƙawuran Allah yana sauya dukkan ka'idojin lissafin abin duniya da aka saba da su."
Mamban Kwamitin Ilimi na Cibiyar Ilimi da Bincike ta Imam Khumaini (Q) ya bayyana taƙawa da tsoron Allah a matsayin wani babban jigo na karfi, inda ya ce: "Taƙawa ba kawai wata dabi'a ce ta mutum guda ba, a'a, tana nufin daidaiton dabi'u da kuma jajircewar al'umma baki daya wajen yin aiki da umarnin Allah. Alkur'ani ya sanya sunnarsa ta zamantakewa a kan cewa ƙarfin gaibi yana bayan duk wata al'umma mai taƙawa."
Haka zalika, ya bayyana hakuri da juriya a matsayin dalilan dorewar nasara, inda ya ce: "Tsayuwa kyam a kan imani da yin hakuri a kan matsaloli na daga cikin abubuwan da ke tabbatar da ɗorewar nasara, kuma al'ummar da ta yi juriya a gaban tsanani za ta zama al'umma mai imani da kuma ƙarfi."
Hadin Kai Da Taimakon Addinin Allah Na Daga Cikin Sharuddan Samun Nasarar Ubangiji
Hujjatul Islam wal Muslimin Baƙirzadeh ya bayyana hadin kai da nisantar sabani a matsayin wasu muhimman abubuwa na karfin siyasa, yana mai cewa: "Biyayya ga Allah da Manzonsa, hadin kai da dinke bakin al'umma da kuma nisantar rikice-rikicen cikin gida, Alkur'ani ya bayyana su a matsayin muhimman hanyoyin samar da ƙarfin siyasa."
Ya kuma bayyana cewa daya daga cikin manyan sharuddan samun nasara shi ne tabbatuwar taimakon Ubangiji (Nasrullah), inda ya kara da cewa: "Taimakon addinin Allah yana daga cikin hanyoyin samun taimakonSa; idan mutane suka taimaki addinin Allah, to tabbas Allah zai taimake su."
Karfin Ubangiji Makami Ne Na Tabbatar Da Gaskiya
Mamban Kwamitin Ilimi na Cibiyar Ilimi da Bincike ta Imam Khumaini (Q), yayin da yake kwatanta mahangar abin duniya da ta Ubangiji game da ƙarfi, ya bayyana cewa: "A mahangar abin duniya, tushen ƙarfi ya takaita ne kawai ga abubuwan zahiri kamar tattalin arziki, ilimi, ƙarfin soji da tasirin siyasa; yayin da a mahangar Ubangiji, ƙarfi na Allah ne shi kadai, kuma duk wani ƙarfi na daban wata alama ce ta nufinsa kuma yana dogara ne da Shi."
Ya kara da cewa: "Ma'aunin auna ƙarfi a mahangar abin duniya yana amfani da alamomi ne na lambobi da kididdiga kamar yawan abubuwan da kasa ke samarwa (GDP), yawan kayan aikin soji da kuma kuɗaɗen ajiya na ƙasashen waje; yayin da a mahangar Ubangiji, ma'aunai ne na cancanta da ruhi kamar imani, taƙawa, ikhlasi, juriya da kuma samun taimakon Allah ake amfani da su wajen aunawa."
Hujjatul Islam wal Muslimin Baƙirzadeh ya jaddada cewa: "A mahangar abin duniya, ƙarfi shi ne burin ƙarshe kuma ana amfani da shi ne domin danniya da nuna fifiko; amma a mahangar Ubangiji, ƙarfi wani makami ne na kafa gaskiya da tabbatar da bautar Allah."
Har ila yau ya bayyana cewa: "Ɗorewar ƙarfin abin duniya mai iyaka ce kuma yana iya karyewa a gaban karfin da ya fi shi; yayin da ƙarfin Ubangiji ba shi da iyaka kuma ya ginu a kan sunnonin Allah da ba sa sauyawa."
Wadanne Siffofi Ne "Iran Mai Karfi" Take Da Su A Lissafin Ubangiji?
Hujjatul Islam wal Muslimin Baƙirzadeh, yayin da yake nuni da siffofin "Iran Mai Karfi" daga mahangar lissafin Ubangiji, ya bayyana cewa: "Bisa abin da Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya bayyana a sakonsa na baya-bayan nan, 'Iran Mai Karfi' tana da muhimman siffofi a cikin tsarin lissafin Ubangiji."
Ya bayyana siffa ta farko da cewa ita ce "kulla alaƙa da dogaro da Iyalan Gidan Manzon Allah Tsarkaka (Ahlulbait A.S)", inda ya fayyace cewa: "Ƙasar da take ɗaukar kanta a matsayin mai alaƙa da Ahlulbait (A) kuma mafi yawan mutanenta suke ƙaunar su, tana da matsayi na musamman a cikin wannan lissafi."
Wannan malami na Hauza da Jami'a ya bayyana "shirye-shiryen tabbatar da gaskiya" a matsayin siffa ta biyu, yana mai cewa: "Al'ummar da ba ta da wani tsoro wajen 'tabbatar da gaskiya' da tsayuwa 'a gaban ƙarya da zalunci', ana daukarta a matsayin al'umma mafi ƙarfi a tsarin lissafin Ubangiji."
Mamban Kwamitin Ilimi na Cibiyar Ilimi da Bincike ta Imam Khumaini (Q) ya ci gaba da bayyana cewa: "Ana kallon al'ummar Iran a matsayin al'umma mai bin tafarkin Annabi (Nabawiyya), Imam Ali (Alawiyya) da kuma Alkur'ani, kuma wannan asali shi ne tushen ƙarfinta."
A karshe, Hujjatul Islam wal Muslimin Baƙirzadeh ya ambaci siffa ta hudu ta "Iran Mai Karfi" a matsayin "ƙarfin sadaukar da rayuwa na al'ummar Iran", inda ya kara da cewa: "Sanar da shirin miliyoyin 'yan kasar Iran na sadaukar da rayukansu a tafarkin manufofin Musulunci da kuma tsara rundunonin sa-kai na al'umma (Basij), wata alama ce karara ta ƙarfin ciki da na Ubangiji da wannan al'umma take da shi."
Ra'ayinka