Asabar 10 Oktoba 2026 - 11:06
Ikhlasin Niyya Shi Ne Mafi Muhimmancin Ma'aunin Tafiya A Tafarkin Karatun Addini

Hauza/ Shugaban Makarantun Hauza na lardin Hamedan, yayin da yake jaddada muhimmancin ikhlasi a tafarkin karatun addini, ya bayyana cewa: "Dole ne dalibin ilimin addini ya sanya neman yardar Allah a matsayin babban burinsa wajen zabar salon rayuwa, neman ilimomin addini, karbar nauye-nauyen zamantakewa da kuma yada koyarwar Musulunci, sannan ya yi juriya a kan tsananin da ke cikin wannan tafarki."

Bisa rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza daga Hamedan, Ayatullah Musawi Isfahani, Shugaban Makarantun Hauza na lardin Hamedan , a yayin darasin tarbiyya da Akhlaƙ da aka gudanar a masallacin makarantar Hauzar Ayatullah Akhund (R), ya yi nuni da muhimmancin kyakkyawar niyya domin Allah a rayuwar dalibtar addini, yana mai cewa: "Karatun Hauza yana samun darajarsa ta hakika ne kawai a lokacin da mutum ya aiwatar da dukkan ayyukansa da kokarinsa domin neman yardar Allah, kuma wajen zabar tafarkin rayuwarsa ya fifita yardar Ubangiji a kan jin dadin kansa na kashin kai."

Ya ci gaba da cewa bayyanar dalibin addini a cikin al'umma sanye da tufafin malamantaka (kayan malanta) yana tattare da manyan nauye-nauye da ayyuka na musamman, inda ya kara da cewa: "Dole ne dalibin addini ta hanyar sanya tufafin malanta ya shirya kansa wajen amsa tambayoyin addini na mutane, bayyana hukunce-hukuncen shari'a, yada kyawawan dabi'u (Umarni da kyakkyawa) da kuma yakar miyagun ayyuka (Hani da mummuna). Yana yiwuwa a wannan tafarki ya fuskanci tsanani, zagi da kuma bakaken maganganu, amma idan manufarsa ita ce neman yardar Allah, to wadannan wahalhalu suna samun ma'ana mai kyau a tafarkin sauke nauyin da ya rataya a wuyansa."

Shugaban Makarantun Hauza na Hamedan ya kafa hujja da aya ta 69 a cikin Suratul Ankabut: «وَالَّذِينَ جَاهَدُوا فِينَا لَنَهْدِيَنَّهُمْ سُبُلَنَا» (Wadanda kuma suka yi fafutuka a tafarkinmu, lallai za mu shiryar da su hanyoyinmu), yana mai fayyace cewa: "Allah ya yi alkawarin cewa duk wadanda suka yi fafutuka da kokari a tafarkinsa zai shiryar da su zuwa ga hanyoyinsa. Dalibin da ya shiga Hauza da niyya ta Allah kuma ya jajirce a wannan hanya, ya wajaba a kansa ya kiyaye wannan kyakkyawar niyya a dukkan matakan karatu, wa'azi da hidimta wa al'umma."

Har ila yau, ya jaddada cewa bai kamata burin karatun addini ya takaita ga samun abin duniya ko mukami a cikin al'umma ba, inda ya bayyana cewa: "Wannan magana ba tana nufin rashin kula da bukatun rayuwa da neman abin dogaro da kai ba ne, a'a, ma'anarta ita ce kada al'amuran kudi da dukiya su zama babban burin mutum a tafarkin karatun Hauza. Ya kamata dalibi ya yi fafutukar kula da rayuwarsa, amma a lokaci guda ya kiyaye kada abubuwan duniya su rinjayi manufar ayyukansa ta neman yardar Ubangiji."

Ayatullah Musawi Isfahani ya kuma yi nuni da muhimmancin ikhlasi a cikin ibadoji da ayyukan addini, inda ya bayyana cewa: "Sallar jam'i, halartar sallar Juma'a da kuma ibadar i'itikafi duk dole ne a yi su da kyakkyawar niyya mai tsarki domin Allah. Ya kamata mutum ya kula kada halartar tarukan addini da gudanar da ibadoji su zama wata hanya ta neman jawo hankalin mutane zuwa gare shi a maimakon neman kusanci zuwa ga Allah."

Daga nan ya kafa hujja da aya ta 5 a cikin Suratul Bayyina: «وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ» (Ba a kuma umurce su da komai ba face su bauta wa Allah suna masu tsarkake addini gare shi), inda ya jaddada wajibcin tsarkake niyya domin Allah kaɗai, kuma ya bayyana littafin Arba'una Hadith na Imam Khumaini (Q) a matsayin daya daga cikin fitattun ayyukan tarbiyya da dabi'u masu kima wajen sanin kyawawa da munanan halaye da hanyoyin gyara zuciya.

Shugaban Makarantun Hauza na Hamedan , yayin da yake nuni da wahalhalun da ke tattare da tafarkin karatun addini da nauyin da ya rataya a wuyan malamai, ya bayyana cewa: "Idan mutum ya shiga wannan hanya da kyakkyawar niyya domin Allah, to ko wahalhalu ma suna samun wata ma'ana ta daban a gare shi. Hanyar Hauza hanya ce ta bin tafarkin Sayyidus-Shuhada (A.S), Amirul Muminina (A.S) da malamai na Ubangiji (Ulama'ur-Rabbaniyyun), wadanda ta hanyar kokarinsu da sadaukarwarsu suka taka muhimmiyar rawa wajen kiyayewa da yada ilimomin addini."

A karshe, Ayatullah Musawi Isfahani ya jaddada wajibcin kiyaye ikhlasi a ci gaban tafarkin juyin juya halin Musulunci da sauke nauye-nauyen addini da na al'umma, tare da nuna godiya ga mahalarta taron da jaddada wajibcin riko da manufofin Ubangiji da kuma juriya a tafarkin hidimta wa addini.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha