Alhamis 8 Oktoba 2026 - 23:04
Tattaunawa (Munazara) | Musuluntar Wani Mai Musanta Samuwar Allah (Munkiri) bayan Tattaunawa da Hisham

Hauza/ Abdullah al-Daysani, daya daga cikin wadanda suka musanta samuwar Allah, bayan ya yi tattaunawa da Hisham kuma ya samu amsoshi masu gamsarwa da haske daga Imam Sadik (A.S) game da ikon Allah da tsarinsa, sai ya dawo ga imani da tauhidi.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito, littafin "Tattaunawa Dari da Daya Masu Ban Sha'awa da Karatu" wanda Muhammad Muhammadi Ishtihardi ya rubuta, ya tattara tattaunawa daban-daban kan al'amuran imani da addini, wanda za a rika bugawa a lokuta daban-daban.

Hisham ibn al-Hakam yana daya daga cikin hazikai kuma wayayyun daliban Imam Sadiƙ (A.S). Wata rana, daya daga cikin wadanda suka musanta samuwar Allah mai suna "Abdullah al-Daysani" ya hadu da Hisham kuma ya yi masa tambayar da a karshe ta sa ya musulunta.

Daysani: Ya Hisham, kana da Ubangiji?

Hisham: Eh.

Daysani: Shin Allahnka yana da iko?

Hisham: Eh, Shi mai iko ne kuma Yana da iko a kan komai.

Daysani: Shin Allahnka zai iya saka dukan duniya a cikin kwai, ba tare da duniya ta rage girma ba, ko kwai ya faɗaɗa ba?

Hisham: Ka ba ni lokaci don in amsa wannan tambayar.

Daysani: Zan ba ka wa'adin shekara guda.

Hisham ya hau dokinsa ya tafi wurin Imam Sadiƙ (A.S) ya ce: "Ya Dan Manzon Allah, Abdullah al-Daysani ya zo wurina ya yi mini wata tambaya wadda ban da wani makami ko mabuya da zan amsa ta sai Allah da kuma kai."

Imam Sadiƙ (A.S): Wace tambaya ce ya yi?

Ya ce: Shin Allah yana da ikon saka duniya da dukan fadin da take da shi a cikin kwai ba tare da duniya ta rage girma ba ko kwai ya girma ba?

Imam Sadiƙ (a.s): Ya Hisham, kana da sassan ji (senses) guda nawa?

Hisham: Ina da guda biyar: Ganin ido, dandana, ji, wari, da kuma taba (ji da fata).

Imam Sadiƙ (A.S): Wanne ne mafi kankanta a cikin wadannan guda biyar?

Hisham: Ganin ido.

Imam Sadiq (A.S): Girman kwayar idon mutum kamar yaya ne?

Hisham: Gwargwadon kwayar waken masar (lentil) ko ma ya fi ta kankanta.

Imam Sadiƙ (A.s): Ya Hisham, duba gabanka da kuma samanka. Gaya mini me kake gani?

Hisham ya duba ya ce: "Ina kallon sama, kasa, gidaje, fadoji, jeji, duwatsu, da kuma kogi."

Imam Sadiƙ (A.S): Allah da Ya iya saka duk wannan fadin duniyar da kake gani a cikin kwayar idonka, zai iya saka dukan duniya a cikin kwai ba tare da duniya ta rage girma ba ko kwai ya girma ba.

A nan take, Hisham ya sunkuya ya sumbaci hannu da kafafun Imam Sadiƙ (A.S) ya ce: "Ya Dan Manzon Allah, wannan amsa ta ishe ni."

Hisham ya koma gidansa. Washegari Abdullah ya zo wurin Hisham ya ce: "Na zo ne kawai don gaishe ka, ba don in karbi amsar tambayar ba."

Hisham ya ce: "Idan kana son amsar tambayar, ga amsar," sannan ya gaya masa amsar da Imam ya bayar.

Abdullah al-Daysani ya yanke shawarar ya je wurin Imam Sadiƙ (A.S) da kansa ya gabatar da wasu tambayoyi. Ya tafi gidan Imam Sadiƙ (A.S) ya nemi izinin shiga, aka ba shi izini. Ya shiga wurin Imam, ya zauna ya ce: "Ya Ja'afar dan Muhammad, shiryar da ni zuwa ga Ubangijina."

Imam Sadiƙ (A.S): Menene Sunanka?

Abdullah ya fita bai gaya masa sunansa ba. Abokansa suka ce masa: "Me ya sa ba ka gaya masa sunanka ba?"

Ya amsa: "Da na gaya masa sunana Abdullah (Bawan Allah), da ya tambaye ni: Wane ne wanda kake bauta masa?"

Abokan Abdullah suka ce: "Ka koma wurin Imam ka ce masa: 'Shiryar da ni zuwa ga Ubangijina amma kar ka tambaye ni sunana.'"

Abdullah ya koma ya ce wa Imam Sadiƙ (A.S): "Shiryar da ni zuwa ga Ubangijina amma kar ka tambaye ni sunana!"

Imam ya nuna wani wuri ya ce: "Zauna a nan." Abdullah ya zauna. A daidai lokacin, daya daga cikin yaran Imam ya shigo yana rike da kwai a hannunsa yana wasa da shi. Imam ya ce wa yaron: "Ba ni wannan kwan." Yaron ya ba wa Imam kwan. Imam ya karba ya juyo wurin Abdullah ya ce: "Ya Daysani! Kalli wannan kwan. Yana matsayin wani katanga da aka rufe, yana da kauri a waje, a karkashin wannan bawon akwai wani siririn bawon, a karkashinsa kuma akwai wani abu tamkar azurfa mai gudana (farin kwai), sannan akwai wani tamkar zinariya narke (kwanduwar kwai), wadannan biyun ba sa haduwa da juna; zinariya mai narkewa ba ta gaurayu da azurfa mai gudana ba, kuma azurfa ba ta gaurayu da zinariya ba. Haka suke a haka, babu wani mai tsara su da ya fito daga ciki ya ce 'Ni ne na yi su haka,' kuma babu wani mai lalata su da ya shiga ciki ya ce 'Ni ne na lalata su.'

Ba a kuma san ko an halicce shi ne don ya samar da ɗa namiji ko mace ba. Ba zato ba tsammani, bayan wani lokaci sai ya tsage, wani tsuntsu mai launi iri-iri kamar ɗawusu ya fito daga ciki!

Shin a ganinka, wannan tsari (mai kyau) ba shi da mai tsarawa?"

Abdullah al-Daysani ya sunkuyar da kansa na wani lokaci saboda wannan tambaya, sannan ya dago kansa yayin da hasken imani ya haskaka zuciyarsa ya ce: "Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah ɗaya, Shi kadai ne ba shi da abokin tarayya, kuma ina shaidawa cewa Muhammadu (S.A.W.A) bawan Allah ne kuma ManzonSa ne, kuma kai Imam ne kuma Hujja ne daga Allah a kan mutane. Na tuba daga mummunan aƙidata da abin da na aikata, kuma ina nadama."

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha