A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, a wani jawabi da ya yi, Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamene'i ya yi bayani kan fannoni daban-daban na azaba da kuma sakamakon rashin amfani da ni’imomin Allah yadda ya kamata.
Ya ce: “A lokacin da ya kamata mu yi amfani da ni’imomi yadda ya kamata, ba mu yi hakan ba. Yanzu kuwa dole ne mu ɗanɗana sakamakon abin da muka aikata!”
Lokacin da aka gabatar da kafirai ga wuta, za a ce musu:
«أَذْهَبْتُمْ طَیِّبَاتِکُمْ فِی حَیَاتِکُمُ الدُّنْیَا»
Ma’ana: "Shin Kun yi amfani da ni’imomin da aka ba ku a cikin rayuwar duniya?" (Ahƙaf: 20)
Saboda haka, yanzu da ranar hisabi da sakamako ta zo, za a yi muku irin wannan sakamako, wato wata azaba ta musamman wadda ita ce azabar wulaƙanci da ƙasƙanci.
To, saboda me ake yi musu wannan azaba?
A nan an ambaci abubuwa biyu: Na farko, sun kasance suna yin girman kai; na biyu kuma, «بِمَا کُنْتُمْ تَفْسُقُونَ» (Ahƙaf: 20), wato sun kasance masu saɓa wa umarnin Allah.
Ma’ana, akwai umarni da hane-hane na Allah, amma su suka kasance suna take su tare da yin watsi da su.
Amma dangane da abin da aka ce «عَذَابَ الْهُونِ» (Al-An’am: 93), dalilin haka shi ne akwai nau’o’in azaba daban-daban. Azaba ba wuta kawai ba ce. Ko da yake an yi bayanin wuta sau da yawa, amma ita kanta nadama babbar azaba ce. A can, wannan nadama ba za ta ƙare ba. Don haka, ɗaya daga cikin nau’o’in azaba shi ne wannan nadamar.
Wani nau’in azaba kuma shi ne tsangwama da ba’a. A cikin Suratul Dukhan an ce:
«ذُقْ إِنَّکَ أَنتَ الْعَزِیزُ الْکَرِیمُ»
Ana faɗin wannan magana ne a lokacin da mafi munin bala’i ya same shi. A zahiri, ana yi masa ba’a ne da wannan magana, tare da tsangwamarsa da wulaƙanta shi.
Wani nau’in azaba kuma shi ne tsoro. A duniya, ko da wane hali mutum yake ciki, yawanci akwai wata ƙaramar kofar fata; wato mutum yana iya cewa watakila mutuwa ta zo ko kuma yanayi ya sauya. Amma a can, babu irin wannan kofar fata, kuma wannan hali ba zai ƙare ba.
Saboda haka, akwai nau’o’in azaba daban-daban. A nan akwai azabar wulaƙanci, sannan akwai azabar tsangwama da ba’a, inda za a ce musu da irin wannan lafazi: “A lokacin da ya kamata ku yi amfani da ni’imomin Allah yadda ya kamata, ba ku yi hakan ba; yanzu ku ɗanɗana sakamakon abin da kuka aikata!”
Ra'ayinka