A cewar rahoton sashen fassara na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Muhammad Al-Bayati ya jaddada cewa Amurka tana ci gaba da yaɗa barazana da nufin kakaba wa Iraki takunkumi, kamar yadda ta yi wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Ya bayyana cewa, sakamakon rashin amincewa da kwance damarar Makamai na Ƙungiyoyin Gwagwarmaya ko takaita su, batun makaman 'yan gwagwarmaya a yanzu yana tafiya ne zuwa ga tsara da sanya su cikin wani tsari na hukuma.
Al-Bayati ya bayyana a wata hira cewa ɓangaren Amurka yana barazanar kakaba wa Iraki takunkumi tare da dakatar da aika dalolin Amurka zuwa ƙasar. Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da ake samun tashin farashin canjin kuɗi a kasuwannin cikin gida, inda farashin dala 100 ya kai dinari 160,000 a cikin kwanakin baya.
Ya ƙara da cewa matakan da gwamnatin Iraki take ɗauka a cikin kwanakin nan na da nufin tabbatar da cewa kuɗaɗen waje da ake samu sun ci gaba da shigowa ƙasar. Hakan na faruwa ne yayin da Amurka ke ci gaba da yin barazana da kuma nuna niyyar kakaba wa Iraki takunkumi.
Al-Bayati ya kuma bayyana cewa Amurka tana matsa wa Iraki lamba domin cimma muradunta a cikin ƙasar.
Ya ce matsin lambar da ake yi domin kwance damarar Ƙungiyoyin Gwagwarmaya ya fuskanci rashin amincewa. Haka kuma, abin da ake kira “takaita makamai” shi ma an ƙi amincewa da shi.
Saboda haka, ya bayyana cewa a halin yanzu kwamitin da ke kula da wannan batu yana aiki ne kan tsara makaman Ƙungiyoyin Muƙawama, ta yadda za a sanya su cikin tsarin Sojin Iraki, Ma’aikatar Cikin Gida, ko kuma Hashdush Sha’abi, wadda ake kallonta a matsayin hukuma mafi kusa da Ƙungiyoyin na Gwagwarmaya.
Ra'ayinka