Litinin 21 Satumba 2026 - 19:27
Iran Ta Shirya Don Yaƙi Na Dogon Lokaci, Kuma Za Mu Sauya Yanayin Yaƙi Idan Aka Kai Mana Hari

Hauza/ Kakakin Rundunar Sojin Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran ya jaddada cewa ƙasar Iran a shirye take don fuskantar yaƙi na dogon lokaci, yana mai bayyana cewa idan aka sake kai mata hari, Iran za ta sauya yanayin yaƙin, ta yi amfani da sabbin makamai, tare da zaɓar wasu wurare daban a matsayin wuraren kai hari.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Janar Muhibbi ya bayyana hakan ne a wata hira da tashar talabijin ta Al-Alam, inda ya yi magana kan ra'ayin Rundunar Sojin Kare Juyin Juya Halin Musulunci game da yaƙin da Amurka da Haramtacciyar Kasar Isra'ila suka yi.

Ya yi iƙirarin cewa Amurka ta fuskanci rashin nasara a fannoni daban-daban na soja, leƙen asiri da dabarun yaƙi.

Kakakin Rundunar ya bayyana cewa Iran ta samu nasara a wannan yaƙi, yana mai cewa Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) ta shirya tsaf don fuskantar yaƙi na dogon lokaci, kuma idan aka ƙara tsananta hare-hare, za ta yi amfani da sabbin ƙarfinta na kariya da kai hari.

Janar Muhibbi ya kuma bayyana cewa Amurka ta yi kuskure wajen ƙididdige ƙarfin juriyar al'ummar Iran, tare da cewa ta yi mamakin ƙarfin makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa na Iran.

A wani ɓangare na jawabinsa, kakakin Rundunar ya bayyana cewa ƙungiyoyin gwagwarmaya da ke Yemen da Lebanon ba wakilan Iran ba ne, yana mai jaddada cewa ƙungiyoyin suna aiki ne bisa ga ƙudirinsu da shawarwarinsu. Ya kuma bayyana cewa Hizbullah za ta ci gaba da ƙarfafa ƙarfin kariyarta da sake gina ikonta.

A ƙarshe, Janar Muhibbi ya jaddada cewa Iran tana mutunta ƙasashen makwabta, yana mai cewa Tehran tana bambanta tsakanin ƙasashen yankin da sojojin Amurka da Haramtacciyar Kasar Isra'ila, kuma ba ta da niyyar kai wa maƙwabtanta hari.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha