A cewar rahoton sashen ƙasa da ƙasa na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Shaikh Zakzaky (H) ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 12 ga Satumba 2026, a yayin taron tunawa da cika shekaru 30 da Waki’ar Abacha, wanda aka gudanar a gidansa da ke Abuja.
A cikin jawabinsa, Jagoran Harkar Musulunci ya yi bitar tarihin Waki’ar Abacha da yadda ta faro, tare da bayyana cewa an shirya waki’ar ne a matsayin wani tsari na musamman da aka ƙulla da nufin kawo ƙarshen Harkar Musulunci a wancan lokaci.
Ya ce shirin ya fara ne da kama mambobin Harkar, sannan a murƙushe masu gudanar da muzaharori. Bayan an samu tsit, sai a aiwatar da kisa, da nufin kawo ƙarshen Harkar gaba ɗaya.
Sai dai Shaikh Zakzaky (H) ya bayyana cewa tsayuwar ’yan uwa, kiraye-kirayen jama’a daga cikin Najeriya da wajenta, da ci gaba da gudanar da muzaharori, tare da tunkarar zaluncin azzalumai duk da fuskantar muzgunawa da cutarwa, sun hana aiwatar da wannan mummunan shiri.
Ya yi nuni da cewa musamman tsayin daka da ’yan uwa da ake kira “Ƴan Caji-caji” suka nuna, na daga cikin abubuwan da suka taimaka wajen dakile shirin.
Jagoran Harkar Musulunci ya kuma bayyana tarihin abubuwan da suka faru a lokacin Waki’ar Abacha, da matakai daban-daban da suka biyo baya har zuwa ƙarshenta, da kuma sakamakon da waɗanda suka aiwatar da ita suka samu.
Ya jaddada cewa barazanar mahukunta ba za ta sa su bar gwagwarmayar tabbatar da addini ba, yana mai tabbatar da cewa ƙoƙarin kawo ƙarshen Harkar Musulunci ba zai yiwu ba.
A bana ne aka cika shekaru 30 da Waki’ar Abacha, wadda ta fara a ranar 12 ga Satumba 1996. A wannan shekara, an gudanar da tarukan tunawa da Waki’ar a ranakun Alhamis da Juma’a a garuruwan Zaria, Kaduna da Saminaka, kafin a gudanar da taron rufe bikin a ranar Asabar a Abuja.






Ra'ayinka