A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, yayin tunatarwar da ya gabatar bayan sallar Juma’a a Masallacin Fagge, Sheikh Sunusi Abdulƙadir ya yi magana kan halin da duniya da al’ummar Musulmi suke ciki, tare da bayyana nauyin da ya rataya a wuyan masu fafutukar tabbatar da addinin Allah.
Ya ce: “Yanzu lokacin nasara ne, lokacin fata ne, lokacin izza ne. Kai da kake da tunanin tabbatar da addini, ka yi ƙoƙari da dukkan ƙarfinka. Kai ne kake kan daidai, ko ba haka ba?”
Sheikh Sunusi ya kuma yi tsokaci kan yadda Amurka da Isra’ila suke nuna kansu a matsayin masu ƙarfin iko, yana mai cewa wannan ikirari ba ya nuna hakikanin ƙarfinsu.
Ya bayyana cewa: “Wannan birin-birin ɗin da Amurka da Isra’ila suka nuna na cewa sun fi kowa ƙarfi, wallahi ƙarya ce. An tona asirinsu, duk ƙarya ce.”
Ya ƙara da cewa abubuwan da suke faruwa a duniya suna nuna cewa yanayi yana sauyawa, kuma idan lokacin da ya dace ya zo, al’amura za su sauya.
Bayan kammala jawabin, mahalarta taron sun yi addu’o’i na musamman ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ƙasar Yemen, bisa matsayinsu na fuskantar matsin lamba da kuma abin da suke yi wajen tunkarar Amurka da Saudiyya.
Haka kuma, an yi addu’a ga Allamah Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) da dukkan ‘yan’uwa, tare da roƙon Allah Ya ba su nasara da ƙarfi wajen ci gaba da ayyukansu.





Ra'ayinka