A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Ayatullahil Uzma Jafar Subhani ya bayyana hakan ne a taron buɗe sabuwar shekarar karatu na Makarantun Hauzar Qum a yau Asabar, 5ga watan Satumba 2026 a makarantar Faiziyya, Qum.
Ayatullah Subhani ya bayyana cewa Hauzar Qum ta shafe kusan ƙarni guda tana taka muhimmiyar rawa wajen koyarwa da yada ilimin addinin Musulunci, tare da samar da malamai da suka yi tasiri a cikin Iran da sauran ƙasashe.
Ya kuma yi kira da a ƙara mayar da hankali kan inganta tsarin karatun Hauza, tare da rage hutun karatu da kauce wa abubuwan da za su kawo cikas ga karatun ɗalibai.
Babban malamin ya jaddada cewa duk da bunƙasar darussan ƙwarewa, Fikihu da Usul ya kamata su ci gaba da kasancewa ginshiƙan karatun Hauza. Ya ba da shawarar gudanar da wasu darussan ƙwarewa da rana, yayin da ake ware safiya domin Fikihu da Usul.
A wani ɓangare na jawabinsa, Ayatullah Subhani ya bayyana cewa wa’azi da isar da saƙon addini na daga cikin muhimman ayyukan Hauza, domin masu wa’azi su ne hanyar da ake bi wajen isar da ilimin da malamai da masu bincike suka samar zuwa ga al’umma.
Ya kuma yi kira da a ƙarfafa ɓangaren wa’azi ta hanyar samar da tsari mai kyau, horar da masu wa’azi da kuma inganta shirye-shiryen da za su taimaka wajen isar da koyarwar addini cikin sauƙin fahimta.
Haka nan, ya jaddada muhimmancin ƙarfafa dangantakar ilimi tsakanin Hauzar Qum da jami’o’i, makarantun Hauza da cibiyoyin bincike na duniya, tare da gudanar da tarukan ilimi na ƙasa da ƙasa a kowace shekara.
A ƙarshe, Ayatullah Subhani ya ba da shawarar tattauna batutuwan ilimi da suka dace da malamai daga mazhabobin Musulunci daban-daban, kamar batutuwan “Rabb”, “Ilah”, ibada, bidi’a da hukunce-hukuncen tafiya, domin ƙarfafa bincike na haɗin gwiwa da tattaunawar ilimi tsakanin malaman Shi’a, Ahlus-Sunna da sauran masu bincike.
Ra'ayinka