Jummaʼa 4 Satumba 2026 - 22:42
Ƙungiyoyin Gwagwarmayar Iraki Sun Gargadi Amurka Gabanin Wa’adin Ficewarta

Hauza/ Ƙungiyoyin gwagwarmayar Musulunci a Iraki sun yi gargaɗi mai ƙarfi kan kasancewar sojojin Amurka a ƙasar, yayin da ranar 30 ga Satumba ke gabatowa, wadda aka sanya a matsayin wa’adin ficewar dakarun Amurka daga Iraki.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Ƙungiyoyin gwagwarmayar sun bayyana cewa ba za su amince da ci gaba da kasancewar sojojin Amurka ko amfani da sararin samaniyar Iraki wajen kai hare-hare ga ƙasashe makwabta ba. Sun kuma danganta batun mika makamai ga gwamnatin Iraki da cikar wasu sharuɗɗa, musamman ficewar Amurka gaba ɗaya daga ƙasar.

Daga cikin sauran buƙatunsu akwai ƙarfafa cikakken ikon gwamnatin Iraki kan ƙasa, teku da sararin samaniya, ƙarfafa tsarin tsaron sararin samaniya na ƙasar, da kuma kawo ƙarshen kasancewar sojojin Turkiyya da ƙungiyoyin da ke amfani da yankin Iraki wajen kai hare-hare.

A nasa martanin, Sheikh Akram al-Ka’abi, babban sakataren ƙungiyar Nujaba, ya ce ƙungiyoyin gwagwarmaya suna jiran ranar 30 ga Satumba, yana mai cewa idan sojojin Amurka ba su fice gaba ɗaya daga Iraki ba, za su kasance cikin shirin fuskantar sabon yanayi na faɗa.

Rahoton ya ce wannan matsaya ta ƙara nuna rashin amincewar ƙungiyoyin gwagwarmayar Iraki da duk wani shiri da za a yi na ci gaba da kasancewar sojojin Amurka a ƙasar, musamman yayin da ake tattauna batun kwance damarar ƙungiyoyin makamai.

Haka kuma, rahoton ya danganta shirin ficewar Amurka da yanayin siyasar cikin gida na Amurka, yana mai cewa ana iya amfani da shi wajen gabatar da ƙarshen aikin yaƙi da ƙungiyar Da'ish a matsayin wata nasara ta siyasa ga gwamnatin Donald Trump.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha