A cewar rahoton Sashen Fassara na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Hujjatul Islam Wal Muslimin Sheikh Na'im Qasim, Babban Sakataren Hizbullah, ya bayyana hakan ne a cikin jawabin da ya gabatar yayin tarukan jama'a da aka gudanar a Lebanon da wasu ƙasashe a daidai lokacin jana'izar shugaban raunana (Mustad'afin), Ayatullah al-Uzma Shahid Sayyid Ali Khamene'i (QS)". Ya jaddada cewa yarjejeniyar tsarin (Framework Agreement) da gwamnatin Lebanon ta ƙulla "gaba ɗaya tana amfanar Isra'ila ne." Ya ƙara da cewa: "Da Isra'ila ita kaɗai ce za ta rubuta wannan yarjejeniya, da ba za ta iya aiwatar da ita ba sai da haɗin gwiwar Amurka da gwamnatin Lebanon."
Ga cikakken jawabin:
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Ƙai. Tsarki da godiya sun tabbata ga Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin halitta Annabinmu Muhammadu (SAWA), da Alayensa tsarkaka, da sahabbansa nagari har zuwa ranar sakamako.
Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuhu.
Mun taru ne domin halartar jana'izar Ayatullahil Uzma, Shahidin Jagora Imam Khamene'i (QS). Ku tsaya saboda Allah, domin wannan jana'iza tsayuwa ce, motsi ne kuma juyin juya hali ne. Allah Madaukakin Sarki Ya ce:
﴿وَالَّذِينَ آمَنُوا بِاللَّهِ وَرُسُلِهِ أُولَٰئِكَ هُمُ الصِّدِّيقُونَ ۖ وَالشُّهَدَاءُ عِندَ رَبِّهِمْ ۖ لَهُمْ أَجْرُهُمْ وَنُورُهُمْ ۖ وَالَّذِينَ كَفَرُوا وَكَذَّبُوا بِآيَاتِنَا أُولَٰئِكَ أَصْحَابُ الْجَحِيمِ﴾
"Waɗanda suka yi imani da Allah da ManzanninSa, su ne masu gaskiya kuma shahidai a wurin Ubangijinsu. Suna da ladansu da haskensu. Amma waɗanda suka kafirta kuma suka ƙaryata ayoyinMu, su ne ma'abota Jahannama."
Muna yin jana'izar shugaban Mustad'afin; Imamin da ya yi shahada tare da wasu daga cikin iyalansa. Muna miƙa ta'aziyya ga Sahibuz-Zaman (AF), ga iyalansa masu daraja, ga dukkan masoyansa, saboda shahadarsa, shahadar iyalansa, da shahadar dukkan kwamandoji, jami'ai da al'ummar Jamhuriyar Musulunci ta Iran waɗanda suka sadaukar da rayukansu domin kusantar Allah. Haka kuma muna taya al'ummar Musulmi da ma duniya baki ɗaya murnar wannan matsayi mafi girma; shahadar da ke ɗaukaka daraja kuma take zama haske ga al'ummomi masu zuwa.
Mun ba da ladan karatun Suratul Fatiha tare da salati ga Muhammadu da Alayensa ga ruhin Jagoran Shahidi da dukkan shahidan da suka yi shahada tare da shi.
Imam Khamene'i (QS) mutum ne da ba shi da tamka a zamaninsa. Jagora ne na musamman, Waliyul Amr ga al'umma, kuma mataimakin Imami Ma'asumi, Imam Mahdi (AF). Faƙihi ne cikakke mai sharuddan wilaya da marja'iyya, Ayatullahil Uzma, mai hangen nesa a fannoni daban-daban kuma wanda ya kafa tubalan wayewar Musulunci ta wannan zamani. Jagora ne, mai tarbiyya ne, mai shiryarwa ne. Kwamanda ne da ke tafiya tare da al'umma yana fitar da su daga bautar son zuciya da gumakan duniya. Shi abin koyi ne, mai kirkira ne, masani ne mai fahimtar siyasa da al'amuran duniya gaba ɗaya. Shi ne wanda ya koya mana tsayin daka, ƙarfin guiwa, ɗaukaka da tawakkali ga Allah.
Allah Madaukakin Sarki Ya ce:
﴿الَّذِينَ يُبَلِّغُونَ رِسَالَاتِ اللَّهِ وَيَخْشَوْنَهُ وَلَا يَخْشَوْنَ أَحَدًا إِلَّا اللَّهَ ۗ وَكَفَىٰ بِاللَّهِ حَسِيبًا﴾
"Waɗanda suke isar da saƙonnin Allah, suna tsoronSa, kuma ba sa tsoron kowa face Allah. Kuma Allah Ya isa Mai yin hisabi."
Ya Shugabana Imam Shahidi Khamene'i! Ya shugabana kuma kwamandana! Ka kasance abin ƙauna a zuciyata har soyayyarka ta cika raina. Kalmominka haske ne ga tafiyata zuwa ga Allah. Ganawa da kai taska ce mara ƙarewa, kuma shawarwarinka fitila ce da ba ta mutuwa.
A cikin jagorancinka na ga amanar Manzon Allah (SAWA), adalcin Amirul Muminin Ali (AS), tsayin dakan Imam Husain (AS), da kuma hanyar Imam Khumaini (QS) mai raya addini da ƙarfafa raunana.
Ina tuna wasiƙarka da ka aiko mini ranar 09/10/2024, kwanaki goma sha biyu bayan shahadar Sayyid Hasan Nasrullah (RA), da kwanaki shida bayan shahadar Sayyid Hashimi (RA), lokacin da aka zaɓe ni Babban Sakataren Hizbullah. A cikin wasiƙar ka rubuta mini:
"Kamar yadda na kasance ina goyon bayan shahidinmu Sayyid Hasan, haka nan zan kasance ina goyon bayanka."
Na karanta wannan jimla sau da dama. Imam mai girma yana cewa: "Ina tare da kai. Zan tallafa maka. Duk abin da kuke buƙata ku nema, zan tsaya tare da ku da dukkan ƙarfina. Kada ku ji tsoron ko da duniya baki ɗaya ta haɗu a kanku. Ni, muminai, mujahidai, Allah da Mala'iku muna tare da ku."
Wannan babbar ni'ima ce. Wannan goyon baya, goyon bayan tafarkin gwagwarmaya ne.
A duk tsawon wannan lokaci har zuwa shahadarsa, Imam bai taɓa neman wani abu daga gare mu ba. A koyaushe yana tambaya: "Me suke buƙata? Ku ba su duk abin da suke so. Kada ku hana waɗannan jarumai komai."
Shi bai taɓa neman wani abu daga gare mu ba, amma mu mun nemi komai kuma mun samu duk abin da muka nema.
Na faɗi lokacin shahadar Sayyid Hasan cewa: "Ruhinsa yana raye." Yau kuma muna maimaita wannan magana gare ka: Kai ma kana raye a cikinmu kuma za ka ci gaba da rayuwa a cikin zukatanmu har abada.
Ya shugabana! Za mu ci gaba da wannan tafarki tare da Waliyul Amr, Ayatullah Sayyid Mujtaba (Dama Zilluhu). Mun ji kasancewarsa kamar yadda muka ji kasancewarka. Wannan shi ne tafarkin waliyyai, tafarkin salihai, tafarkin ɗaukaka.
Mun ga miliyoyin mutane a Iran da Iraki. Tarihi bai taɓa ganin irin wannan taro ba: miliyoyin mutane a Tehran, Qum, Najaf, Karbala da Mashhad. Wannan alama ce ta imani, ƙauna da sadaukarwa ga wannan tafarki. Wannan ya nuna cewa tsarin Musulunci na Iran tsarin jama'a ne, tsarin mutunci da rayuwa ne.
Ina gaishe da wannan babbar al'ummar Iran. Kun kare mana mutunci kuma kun tabbatar wa duniya cewa kun cancanci irin wannan jagoranci. Muna son ku, za mu kasance tare da ku, kuma za mu kasance hannu ɗaya wajen fuskantar girman kai, Isra'ila da azzaluman duniya.
Shahada rayuwa ce, tashi tsaye ce, kuma tashi tsaye ɗaukaka ce. Shahadarka, ya shugabana, farkon sabon juyin juya hali ne wanda zai sauya daidaiton yankin.
Allah Ya ce:
﴿وَلَا تَقُولُوا لِمَنْ يُقْتَلُ فِي سَبِيلِ اللَّهِ أَمْوَاتٌ ۚ بَلْ أَحْيَاءٌ وَلَٰكِنْ لَا تَشْعُرُونَ﴾
"Kada ku ce ga waɗanda aka kashe a tafarkin Allah matattu ne. A'a, rayayyu ne, amma ku ba ku sani ba."
Imam Khumaini (QS) ya ce: "Ku kashe mu; al'ummarmu za ta ƙara wayewa."
An kashe Imam Husain (AS), sai aka haifi tafarkin Husaini. An kashe Imam Khamene'i, sai aka haifi tafarkin Khamene'i.
Mayakan Hizbullah a Lebanon masoya shahada ne kuma masoya wilaya. Sun yi jihadi nagari kuma suka zama abin koyi ga duniya.
Al'ummarmu mai gwagwarmaya ta koyi haƙuri, jihadi, juriya da sadaukarwa daga gare ka. Ba za ta taɓa karɓar ƙasƙanci ba. Wannan al'umma ba za ta taɓa shan kashi ba saboda tarbiyyar wilaya ce: "Hayhat minnaz zilla."
Imam Khamene'i (QS) ya jagoranci al'umma bisa ginshiƙai guda biyar:
1. Gina ƙasa da al'umma.
2. Goyon bayan gwagwarmaya da mamaya da girman kai.
3. Haɗin kan ƙasa, Musulmi da bil'adama.
4. Mai da alkiblar gwagwarmaya zuwa 'yantar da Falasdinu.
5. 'Yanci da rashin dogaro da wasu.
Harin Amurka da Isra'ila kan Iran hari ne na duniya baki ɗaya kan ƙasa mai cin gashin kanta. Amma Iran ta tsaya tsayin daka, ta karya manufofin maƙiya, kuma ta fito da ƙarfi da mutunci.
Iran tana da haƙƙin mallakar ƙarfi, makamashin nukiliya na zaman lafiya, da kuma tsara hulɗarta da sauran ƙasashe yadda take so.
Muna gode wa Iran ta Musulunci. Ita ce ta tsaya tare da mu. Ita ce ta tabbatar da batun tsagaita wuta a Lebanon yayin tattaunawarta da Amurka. Ta dage cewa ba za ta ci gaba da yarjejeniya ba sai an aiwatar da tsagaita wutar a Lebanon.
Muna gode wa jagoranci, gwamnati, IRGC, rundunar soji, al'umma da masana na Iran. Kun ba mu ƙarfi, goyon baya da ɗaukaka. Kun ba mu damar samun 'yanci da yi wa al'umma hidima. Da ba don Iran ba, da ba a samu tsagaita wuta ba.
Tsayin dakan gwagwarmaya shi ne ginshiƙi na farko, sannan goyon bayan Iran shi ne ginshiƙi na biyu. Mun rungumi wannan zaɓi domin ya tabbatar mana da amfani da ƙarfi.
Dole ne dukkanmu mu yi aiki domin kawar da ikon Amurka daga Lebanon. Amurka mai yaudara ce kuma mai mulkin mallaka ce. Tana matsa wa Lebanon lamba domin biyan bukatun Isra'ila.
Wasu suna tambayar me ya sa muke hulɗa da Iran. Ni kuma ina tambaya: me ya sa kuke hulɗa da Amurka alhali tana wulaƙanta ku, tana kwace dukiyoyinku kuma ba ta ba ku komai?
Yarjejeniyar da gwamnatin Lebanon ta ƙulla gaba ɗaya tana amfanar Isra'ila. Da Isra'ila ita kaɗai ce za ta rubuta ta, ba za ta iya cimma hakan ba sai da taimakon Amurka da gwamnatin Lebanon.
Ina kira ga gwamnati ta janye daga wannan yarjejeniya, domin ta haɗa kan mutanen Lebanon maimakon raba su.
Muna goyon bayan tattaunawa ta kai tsaye ba tare da mika wuya ba. Babu mafita sai ficewar Isra'ila gaba ɗaya daga yankunan Lebanon, girke sojojin Lebanon zuwa kudu da kogin Litani, dakatar da dukkan hare-hare ta sama, ƙasa da ruwa, sakin fursunoni, sake gina yankunan da aka lalata da kuma dawo da mazauna ƙauyukansu.
Za mu ci gaba da tafiya tare da fahimtar juna tsakanin Iran da Amurka muddin tana kare muradun Lebanon. Ba za mu miƙa wuya ba. Kamar yadda muka rusa shirin kawo ƙarshen gwagwarmaya, haka nan za mu ci gaba da tsayawa tare da al'ummarmu har sai an 'yantar da ƙasarmu baki ɗaya, in sha Allah.
Allah Ya yi rahama ga Imam ɗinmu kuma jagoranmu, Imam Shahid Khamene'i (QS), da iyalansa, da dukkan masoyansa da shahidan da suka yi shahada tare da shi.
Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuhu.
Ra'ayinka