A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, ana gabatar da jerin darussan Mahdawiyya mai taken “Zuwa ga Al’umma Mai Manufa”, domin yaɗa koyarwa da ilimin da suka shafi Imam Mahdi (Allah Ya gaggauta bayyanarsa), ga masu neman ilimi da masu karatu.
Wasu daga cikin ayoyin da suka shafi Imam Mahdi (AS) da juyin juya halinsa na duniya:
Aya ta uku
﴿وَعَدَ اللَّهُ الَّذینَ آمَنُوا مِنْکُمْ وَ عَمِلُوا الصَّالِحاتِ لَیسْتَخْلِفَنَّهُمْ فِی الْأَرْض کَمَا اسْتَخْلَفَ الَّذینَ مِنْ قَبْلِهِمْ وَ لَیمَکِّنَنَّ لَهُمْ دینَهُمُ الَّذِی ارْتَضی لَهُمْ وَ لَیبَدِّلَنَّهُمْ مِنْ بَعْدِ خَوْفِهِمْ أَمْناً یعْبُدُونَنی لا یشْرِکُونَ بی شَیئاً وَ مَنْ کَفَرَ بَعْدَ ذلِکَ فَأُولئِکَ هُمُ الْفاسِقُونَ﴾
“Allah Ya yi wa waɗanda suka yi imani daga cikinku kuma suka aikata ayyukan ƙwarai alkawarin cewa lalle Zai sanya su magada a bayan ƙasa, kamar yadda Ya sanya waɗanda suka gabace su magada. Kuma lalle Zai tabbatar musu da addininsu wanda Ya yarda musu da shi, kuma lalle Zai sauya musu tsoro da aminci. Za su bauta Mini ba tare da sun haɗa Ni da wani abu ba. Kuma wanda ya kafirta bayan haka, to waɗannan su ne fasiƙai.” (Suratul Nur, aya ta 55)
A cikin ayoyin da suka gabaci wannan aya, an yi magana ne kan biyayya da miƙa wuya ga umarnin Allah da Manzonsa (SAWA). A wannan ayar kuma, an ci gaba da bayanin sakamakon wannan biyayya, wanda shi ne samun mulkin duniya gaba ɗaya.
Wannan aya tana nuna cewa Allah Ya yi wa wani rukuni na musulmi masu imani da ayyukan alheri alkawuran abubuwa uku:
1. Za su zama magada da masu mulki a bayan ƙasa;
2. Yaɗuwar addinin gaskiya a duniya;
3. Ƙarewar abubuwan tsoro da rashin tsaro.
Saboda haka, mutane a wannan zamani za su bauta wa Allah cikin cikakken ’yanci, su bi umarninsa, ba za su yi masa abokin tarayya ba, kuma za su yaɗa tauhidi na gaskiya a ko’ina.
Abubuwan lura:
1. Su waye waɗanda suka gabaci musulmi kuma suka samu mulki a bayan ƙasa?
Bisa ga wannan aya, akwai wasu mutane da suka kasance kafin musulmi waɗanda suka samu matsayin shugabanci a bayan ƙasa. Wasu malaman tafsiri sun ce ana nufin Annabi Adam (AS), Annabi Dawuda (AS) da Annabi Sulaiman (AS).
Domin Allah Ya ce game da Annabi Adam (AS):
﴿إِنِّی جاعِلٌ فِی الْأَرْضِ خَلِیفَة﴾
“Lalle Ni Zan sanya magaji a bayan ƙasa.” (Suratul Baƙara, aya ta 30)
Game da Annabi Dawuda (AS), Allah Ya ce:
﴿یا داوُدُ إِنَّا جَعَلْناکَ خَلِیفَةً فِی الْأَرْض﴾
“Ya Dawuda! Lalle Mun sanya ka wakili a bayan ƙasa.” (Suratus Sad, aya ta 26)
Haka nan Annabi Sulaiman (AS) ya gaji mulkin Annabi Dawuda (AS), kamar yadda aya ta 16 a Suratul Naml ta nuna.
Sai dai wasu malaman tafsiri, kamar Allama Tabataba’i (RA), sun nuna wannan fahimta ba ta da ƙarfi, domin kalmar “waɗanda suka gabace su” ba ta dace da Annabawa ba. A ganinsa, wannan kalma tana nufin al’ummomin da suka gabata waɗanda suka kasance masu imani da ayyukan ƙwarai kuma suka samu mulki a bayan ƙasa.
Wasu kuma sun ce wannan aya tana nufin Bani Isra’ila, domin bayan zuwan Annabi Musa (AS) da rushe ƙarfin Fir’auna, sun samu mulki a bayan ƙasa.
Allah Ya ce:
﴿وَ أَوْرَثْنَا الْقَوْمَ الَّذینَ کانُوا یسْتَضْعَفُونَ مَشارِقَ الْأَرْضِ وَ مَغارِبَهَا الَّتی بارَکْنا فیها﴾
“Mun gadar wa raunanan mutane gabashi da yammacin ƙasar da muka albarkata.” (Suratul A’araf, aya ta 137)
Haka kuma Allah Ya ce:
﴿وَ نُمَکِّنَ لَهُمْ فِی الْأَرْض﴾
“Mun yi nufin mu ba wa raunana damar samun iko a bayan ƙasa.”
2. Su wanene alkawarin Allah ya shafa?
A cikin wannan aya, Allah Ya yi alkawarin mulki a bayan ƙasa, ɗaukakar addini da cikakken tsaro ga wani rukuni na muminai da salihai. Amma malamai sun yi saɓani kan waɗanda ake nufi.
Wasu sun ce wannan aya tana nuni ne da gwamnatin Imam Mahdi (AS), wadda za ta mamaye gabas da yammacin duniya, addinin gaskiya zai yaɗu ko’ina, tsoro da yaƙe-yaƙe za su ƙare, kuma za a bautawa Allah ba tare da shirka ba. (Tafsirin Al-Mizan, juzu’i na 15, shafi na 218)
Babu shakka, wannan aya tana iya shafar musulman farko da kuma gwamnatin Imam Mahdi (AS). Bisa ga akidar musulmi gaba ɗaya, ‘yan Shi’a da Ahlus-Sunna, Imam Mahdi (AS) zai cika duniya da adalci bayan ta cika da zalunci, kuma shi ne cikakken misalin wannan aya.
Sai dai hakan ba ya hana ayar samun ma’ana mai faɗi.
Wasu suna cewa kalmar “ƙasa” tana nufin duk duniya kuma wannan aya ta musamman ga gwamnatin Imam Mahdi ce. Amma wannan bai dace da kalmar “kamar yadda Ya sanya waɗanda suka gabace su” ba, domin mulkin waɗanda suka gabata bai mamaye duniya gaba ɗaya ba.
Haka kuma dalilin saukar ayar yana nuna cewa wani misali na wannan mulki ya samu a zamanin Annabi Muhammad (SAWA), ko da yake a ƙarshen rayuwarsa.
A ƙarshe, cikakken sakamakon ƙoƙarin Annabawa da kira zuwa ga tauhidi, tsaro da bautar Allah zai bayyana ne a lokacin bayyanar Imam Mahdi (AS). (Tafsirin Nemune, juzu’i na 14, shafi na 530–532)
Wannan bayani ba yana nufin ayar ta takaita ga wannan ma’ana ɗaya ba ne, sai dai yana bayyana mafi cikar misalin ta.
An ruwaito daga Abu Basir daga Imam Sadiƙ (AS) cewa game da wannan aya ya ce:
«نَزَلَتْ فِی الْمَهْدِیِّ عَلَیْهِ السَّلَامُ»
“An saukar da wannan aya ne game da Mahdi (AS) da mabiyansa.” (Sheikh Tusi, Kitabul Ghaiba, shafi na 177)
Allama Tabataba’i (RA) ya rubuta cewa: “Wannan al’umma mai tsarki da kyawawan siffofi ba ta taɓa samuwa a duniya ba har zuwa yanzu. Idan za a samu irin wannan al’umma, to za ta kasance ne a zamanin Imam Mahdi (AS), saboda hadisai masu yawa daga Manzon Allah (SAWA) da Ahlul Baiti (AS) sun yi bayanin samuwar irin wannan al’umma.”
Ya ƙara da cewa wannan fahimta tana nufin salihar al’umma ce, ba wai mutum ɗaya kaɗai ba.
A cikin Majma’ul Bayan, an ambata cewa malaman tafsiri sun yi saɓani kan ma’anar “waɗanda suka yi imani daga cikinku”, kuma an ruwaito daga Ahlul Baiti (AS) cewa ana nufin Imam Mahdi daga zuriyar Annabi Muhammad (SAWA).
An ruwaito daga Imam Ali Zainul Abidin (AS) cewa: “Wallahi! Su ne mabiyanmu Ahlul Baiti. Allah Zai cika wannan alkawari ta hannun wani mutum daga gare mu, wanda shi ne Mahdin wannan al’umma.”
Kuma an kawo makamancin wannan ruwaya daga Imam Baƙir da Imam Sadiƙ (AS). (Majma’ul Bayan, juzu’i na 7, shafi na 52)
Wannan tattaunawa za ta gaba ...
An samo daga littafin “Darsname Mahdaviyyat” na Khodamurad Salimiyan, tare da ɗan gyara kaɗan
Ra'ayinka