Talata 7 Yuli 2026 - 22:50
Rufe Zaman Makokin Shahadar Ayatullah Sayyid Ali Khamenei A Hussainiyyatu Aali Muhammad Da Ke Bauchi, Najeriya

Hauza/ An gudanar da taron kammala zaman juyayin shahadar Ayatullah Sayyid Ali Khamenei tare da halartar ɗimbin mabiya Sheikh Ibraheem Zakzaky a garin Bauchi na Najeriya, inda masu jawabi suka jaddada muhimmancin ci gaba da bin tafarkin jagoranci, tunani da kuma ƙimomin da wannan jagora marigayi ya tsaya a kansu.


A cewar rahoton wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, a yammacin ranar Lahadi, 5 ga Yuli, 2026, wanda ya yi daidai da 20 ga watan Muharram, 1448H, ƴan uwamusulmi mabiya Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) a garin Bauchi sun gudanar da taron kammala zaman makokin shahadar Ayatullah Sayyid Imam Ali Khamenei a Hussainiyyatu Aali Muhammad da ke rukunin gidajen Tafawa Balewa, Bauchi.

A wajen wannan taro, Sheikh Ahmad Yusuf Yashi, wakilin 'yan'uwan Harkar Musulunci a Najeriya na garin Bauchi da kewaye, ya gabatar da jawabin rufe zaman makokin.

A farkon jawabinsa, Sheikh Yashi ya miƙa ta’aziyya ga al’ummar musulmi a faɗin duniya, inda ya bayyana rashin Ayatullah Shahid Sayyid Ali Khamenei a matsayin babbar jarrabawa ga al’ummar Musulunci. Ya kuma bayyana shi a matsayin gwarzo, mai kishin addini, mai sadaukarwa kuma mai kare raunanan duniya.

Sheikh Yashi ya yi taƙaitaccen bayani kan rayuwa da gwagwarmayar Ayatullah Khamenei, sannan ya yi magana kan alaƙar tunani da ruhi da ke tsakanin marigayin da Imam Ruhullah Khumaini (QS), inda ya bayyana irin matsayin da Imam Khumaini ya bai wa Ayatullah Khamenei.

Ya kawo wani bayani daga Imam Khumaini (QS) cewa a wani lokaci lokacin da ake kai masa wasu batutuwa domin neman shawararsa, ya ce: “Idan a cikinku akwai mutane irinsu Sayyid Khamenei, to ba ku da wata matsala da za ta sa sai kun zo wajena.”

A cikin jawabinsa, Sheikh Yashi ya kuma yi magana kan ƙoƙarin wasu ɓangarori na haddasa rarrabuwa da fitina tsakanin musulmi, inda ya jaddada cewa bai kamata a yi amfani da sunan addini wajen ruɗar da mutane ko haifar da ƙiyayya a tsakaninsu ba.

Ya ƙara da cewa hatta wasu manyan malaman Saudiyya sun halarci zaman ta’aziyyar wannan babban rashi, kuma bidiyoyin hakan sun bazu, don haka ya kamata a guji yaɗa abubuwan da ke kawo rarrabuwa.

Sheikh Yashi ya bayyana takaicinsa kan rashin halartar wakilan gwamnatin Najeriya a irin waɗannan zaman ta’aziyya, yana mai cewa duk da kasancewar Najeriya ƙasar da ke da mafi yawan musulmi a nahiyar Afirka, rashin samun ko mutum guda daga jami’an gwamnati a wajen taron abun bakin ciki ne.

A ƙarshen jawabinsa, ya jaddada cewa rayuwar Ayatullah Sayyid Ali Khamenei tana ɗauke da darussa masu yawa waɗanda al’umma ya kamata su koya tare da amfani da su a rayuwarsu.

Kafin babban jawabin, an buɗe taron da karatun ayoyin Alƙur’ani mai girma wanda Alaramma Sagir Gwallaga ya gabatar. Daga bisani, ɗaliban Fudiyya sun gabatar da waƙoƙin Turanci na juyayin shahadar Imam Khamenei, sannan wasu ƙungiyoyi suka gabatar da shirye-shirye na musamman.

A ƙarshe, Sheikh Ahmad Yusuf Yashi ya gabatar da addu’ar rufewa, inda ya roƙi Allah Ya kai ladan wannan aiki ga ruhin Ayatullah Shahid Sayyid Ali Khamenei, albarkacin Annabi Muhammad (SAWA) da Ahlul Baiti (AS).

Rufe Zaman Makokin Shahadar Ayatullah Sayyid Ali Khamenei A Hussainiyyatu Aali Muhammad Da Ke Bauchi, Najeriya

Rufe Zaman Makokin Shahadar Ayatullah Sayyid Ali Khamenei A Hussainiyyatu Aali Muhammad Da Ke Bauchi, Najeriya

Rufe Zaman Makokin Shahadar Ayatullah Sayyid Ali Khamenei A Hussainiyyatu Aali Muhammad Da Ke Bauchi, Najeriya

Rufe Zaman Makokin Shahadar Ayatullah Sayyid Ali Khamenei A Hussainiyyatu Aali Muhammad Da Ke Bauchi, Najeriya

Rufe Zaman Makokin Shahadar Ayatullah Sayyid Ali Khamenei A Hussainiyyatu Aali Muhammad Da Ke Bauchi, Najeriya

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha