A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza da aka samu daga shafin Ofishin Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), a ranar goma ga watan Muharram, wato ranar Ashura, an gudanar da taron juyayin shahadar Shugaban Shahidai, Imam Hussain (A.S), tare da halartar masoya da mabiya koyarwar Ahlul Baiti (A.S) a gidan Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), da ke babban birnin tarayya Abuja.
Sheikh Ibraheem Zakzaky ya gabatar da jawabi ne ga yan uwa a yayin wannan taro, wanda yake matsayin cigaba da tarukan juyayi da aka shafe kwanaki ana gudanarwa a daruruwan birane da kauyukan Najeriya tun farkon watan Muharram har zuwa yammacin ranar Alhamis (10 ga Muharram, 1448 bayan hijira, wanda ya yi daidai da 25 ga watan Yuni, 2026).
Yayin da yake jaddada cewa kwanakin tarukan Ashura lokuta ne na daukar darasi, Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya ya bayyana cewa: "Tsayuwar Imam Hussain (A.S) da kin sallamawa azzalumai ta koyar da cewa ba a sallamawa azzalumai, kuma zama mai iko ko mulki ba shi ne ke mayar da mutum shugaba ba, ko wajabta yi masa biyayya."
A yayin da yake fashin baki kan irin rawar da juyin juya halin Karbala ya taka wajen kiyaye addinin Musulunci, ya ce: "Makarantar Imam Hussain ta sadaukarwa da fuskantar azzalumai ita ce ta wanzar da addini."
Daga nan sai Sheikh Zakzaky ya bayyana nasarar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayin misali na zahiri na riko da wannan koyarwa. Ya bayyana cewa wannan ita ce koyarwar addini ta tsayuwa kan gaskiya da kangarewa zalunci, wadda Ahlul Baiti (A.S) suka raya.
A karshen jawabinsa, Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya ya jaddada cewa wannan hanyar ta Imam Hussain (A.S), wato ta sadaukarwa ko da mene ne farashi, tare da jajircewa a kan turba, ita ce kadai mafitarmu duniya da lahira.







Ra'ayinka