Jummaʼa 26 Yuni 2026 - 14:46
Tafarkin Rayuwa | Makamin Da Ke Sa Ƙarfin Shaiɗan Ya Gaza

Hauza/ Sarkin Muminai Ali (A.S) a cikin littafin Nahjul Balagha, ya bayyana tsoron Allah (Taƙawa) a matsayin wani babban makami mai iko da ke rusa takama da makarkashiyar Shaiɗan su zama marasa amfani. Ya jaddada cewa taƙawa ba kariya ce kawai daga zunubai ba, a'a, tana tumɓuke asalin kurakurai ne tare da tseratar da ɗan Adam daga tarkon Shaiɗan.

A cewar rahoton sashi na musamman na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Sarkin Muminai Ali (A.S) ya bayyana kima da amfanin tsoron Allah kamar haka:

«اعْلَمُوا عِبَادَ اللَّهِ أَنَّ التَّقْوَی دَارُ حِصْنٍ عَزِیزٍ .... أَلَا وَ بِالتَّقْوَی تُقْطَعُ حُمَةُ الْخَطَایَا.»

"Ku sani, ya ku bayin Allah! Lallai taƙawa (tsoron Allah) wata katanga ce mai ƙarfi da ba ta faduwa... Ku saurara da kyau, ta hanyar kiyaye kai (tsoron Allah) ne ake iya yanke asalin jijiyoyin zunubai." (Nahjul Balagha, Huɗuba ta 157

Bayani Da Sharhi:

Kamar yadda ɗan Adam ke buƙatar sutura ta zahiri domin ya rufe jikinsa da al'aurarsa, haka ma yake buƙatar wata sutura ta musamman domin ya rufe munanan aibu na badini (na cikin zuciya). Tufafi na zahiri yana kare jiki daga sanyi da sauran lahani na fili, sannan yana zama ado na zahiri ga mutum. Amma kuma badinin ɗan Adam shi ma yana fuskantar haɗari na gaske, don haka yake buƙatar a suturta shi da siffofi na Ubangiji.

Ubangiji Maɗaukakin Sarki ya gargaɗe mu kan wannan haɗari a cikin Alƙur'ani mai girma, inda Yake cewa:

 «یَا بَنِی آدَمَ لَا یَفْتِنَنَّکُمُ الشَّیْطَانُ.»

"Ya ku ''yan Adam! Kada Shaiɗan ya rude ku (ya fitine ku)." (Suratul A'araf, Aya ta 27) 

Koda yake mu ba ma ganin Shaiɗan, amma shi yana ganin mu sosai. Yana lura da dukkan ayyukanmu na babba da na ƙarami dare da rana, kuma a koda yaushe yana neman wata dama ko wata kafa da zai shiga cikin ruhin ɗan Adam. Kamar yadda Alƙur'ani ya bayyana:

«إِنَّهُ یَرَاکُمْ هُوَ وَقَبِیلُهُ مِنْ حَیْثُ لَا تَرَوْنَهُمْ.»

"Lallai shi (Shaiɗan) da mukarrabansa suna ganinku ta inda ku ba kwa ganinsu."

A saboda wannan dalili ne Allah Maɗaukaki Ya ce:

«وَلِبَاسُ التَّقْوَی ذَلِکَ خَیْرٌ.»

"Kuma tufafin taƙawa (tsoron Allah) shi ne mafi alheri."

Wannan magana tana nuna cewa Allah Maɗaukakin Sarki Yana son Ya wadatar da ɗan Adam da wani makami a gaban Shaiɗan – wanda shi ne babban makiyinsa da ya yi rantsuwa a kansa – ta yadda shi da rundunarsa ba za su sami ikon shiga cikin rayuwar ɗan Adam ba.

Wannan shi ne makamin da Sarkin Muminai Ali (A.S) ya kira shi da "wata katanga mai ƙarfi da ba ta faɗuwa." Makamin da ke da ikon busar da dukkan tushen zunubai – waɗanda suke sanya mutum ya yi nisa da Mahaliccinsa.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha