Alhamis 11 Yuni 2026 - 13:13
Shin Mamata Suna Zuwa Ziyartar Iyalansu a Ranakun Alhamis?

Hauza/ A cewar wannan masanin addini, yadda mamata suke da ikon dubawa ko ziyartar iyalansu ya danganta da matsayinsu da darajarsu a duniyar barzahu, don haka ba za a iya yanke hukunci guda ɗaya ga kowa ba.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa, Hujjatul Islam wal Muslimin Rida Muhammadi ya yi bayani a yayin ba da amsa ga wata tambaya game da ikon mamata na ziyartar ‘yan uwansu. Ya yi nuni da cewa matsayi da darajojin mutane a duniyar barzahu sun bambanta, saboda haka wannan damar ma tana bambanta daga mutum zuwa mutum.

Tambaya:
Shin mutanen da suka rasu suna samun ‘yanci a ranakun Alhamis su je su ziyarci danginsu?

Amsar Hujjatul Islam wal Muslimin Rida Muhammadi:

Mutanen da suka rasu suna da yanayi mabambanta gwargwadon matsayinsu da darajarsu a duniyar barzahu. Wasu daga cikinsu ana ba su damar su rika duban iyalansu a duniya kowace rana. Wasu kuma ana ba su wannan dama bayan kwana biyu-biyu, wasu kuma sau ɗaya a mako.

Ya ce, duk yadda matsayin mamaci ya fi girma, to haka damar da yake da ita na dubawa ko ziyartar iyalansa take ƙaruwa. Saboda haka ba zai yiwu a bayar da hukunci ɗaya tak ga kowa ba.

Ya ƙara da cewa a ranakun Alhamis da Juma’a, dukkan mamata suna samun ƙarin ‘yanci fiye da sauran ranaku. Sai dai yadda wannan ziyara ko dubawar take kasancewa, yana ci gaba da danganta ne da matsayinsu da darajarsu a barzahu. Duk wanda matsayinsa ya fi girma, to damar da yake da ita ma ta fi yawa.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha