A cewar rahoton sashen fassara na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Ayatullah al-Uzma Sheikh Muhammad Ishaƙ Fayyadh ya riga mu gidan gaskiya ne yana da shekaru 96 a duniya a daya daga cikin asibitocin babban birnin kasar Iraki, wato Bagadaza.
Hazrat Ayatullah Fayyadh (wanda aka haifa a shekarar 1930 a kasar Afganistan), yana daya daga cikin manyan maraji'an taƙalid na mabiya mazhabar Shi'a Imamiyyah, kuma babban malami mai koyar da karatun koli na "Darsul-Kharij" a makarantar Hauzar Najaf mai alfarma, sannan ya kasance daya daga cikin almajiran fitaccen malami marigayi Ayatullah al-Uzma Sayyid Abul Qasim al-Khu'i.
Ra'ayinka