Litinin 11 Mayu 2026 - 22:29
Yadda Mutum Ke Gurɓata Kansa da Zunubi ta Hanyar Ishara

Hauza/ Mai girma Ayatullah Jawadi Amuli ya jaddada cewa: "wani lokaci mutum kan fada cikin zunubi ba tare da ya furta wata magana ba, sai dai kawai ta hanyar ishara da alama.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran  Hauza, Ayatullah Jawadi Amuli a cikin wani bayani nasa ya yi magana kan batun “zunubi ta hanyar ishara”, inda ya bayyana cewa: “Wani lokaci mutum ba tare da ya yi magana ba, amma kawai ta yin ishara da alama, yana iya gurbata kansa da zunubi. Kamar yadda Alƙur’ani mai girma ya ce:  

"وَیلٌ لِکُلِّ هُمَزةٍ لُمَزَة"

‘Azaba ga duk wani mai zinɗe da yi wa mutane ba’a.’  (Suratul Humazah: 1)  

 Haka ma kallon da ake yi da gefen ido (ƙifce), na nuni da izgili ko raini, suna cikin wannan ma’ana. Manufar ita ce irin kallon da ake yi domin neman aibin mutane, ko wulakanta su, ko yi musu ba’a, ko nuna girman kai da alfahari, da makamantan haka.”

Ya kara da cewa: “Ishara mai haifar da zunubi ba ta takaita ga ido kadai ba. Isharori ta hanyar gira, leɓɓa, baki, hannu ko harshe ma na iya zama wata alama da ke jawo wa mutum zunubi.”

Tunatarwa!

Ishara ko magana ta hanyar alama tana zama abin ƙi ne ne kawai idan ta kai ga aikata zunubi; ba kowace ishara ko magana mai ɓoyayyiyar ma’ana ba ce mummuna. A zahiri, da yawa daga cikin maganganun hikima ana isar da su ne ta hanyar ishara da alama, kuma Alƙur'ani mai girma cike yake da ma’anoni da aka gabatar da harshen ishara da alama, domin masu tunani su fahimce su kuma su amfana da hikimominsa.

Madogara

Littafi: Saluni Qabla An Tafƙiduni (Tahrir Nahjul Balagha), juzu’i na 5, shafi na 37–38.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha