Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa, ga cikakkiyar fassarar rubutun wasikar godiyar Ayatullah Muhsin Araki, memba a Majalisar Manyan Malaman Hauza kuma memba a majalisar shugabannin Majalisar Kwararrun Iran, dangane da matsayar jarumtar Fafaroma Leo na XIV, babban jagoran cocin Katolika:
Bismillahir Rahmanir Rahim
Mai girma Fafaroma Leo na XIV
Jagoran babbar cocin Katolika
Tare da girmamawa mai yawa, ina rubuto wannan wasiƙa gare ku a yayin da muryarku mai ƙarfi wajen kare zaman lafiya da adalci ke haskakawa tamkar fitila a cikin duhun masu haddasa yaƙi da masu neman iko.
A cikin duniya da karfin iko ya maye gurbin tattaunawa, kuma barazanar hallakar al’adu ta zama ruwan dare a siyasar shugaban ƙasar Amurka mai girman kai da zalunci, ku kun tsaya tare da miliyoyin marasa gata, waɗanda yaƙi ya rutsa da su, ‘yan gudun hijira da uwa-uba da suka rasa ‘ya’yansu a harshen bama-bamai, kuna magana don kare su.
Lokacin da kuka bayyana barazanar “hallaka wata al’ada gaba ɗaya” da “hari kan wasu ƙasashe” a matsayin “ba abin yarda ba”, ba magana ta siyasa ba ce kawai, sai dai kira ga lamirin ɗan adam ne. Kun nuna cewa bin Injila yana nufin tsayawa gaban ruɗin ƙarfin girman kai wanda shi ne tushen yaƙe‑yaƙe da rashin tsaro.
Yada hoton bogi na Trump cikin surar Annabi Isa (AS) aiki ne na kafirci da kaskanci ga al’adun addinai gaba ɗaya, kuma hari ne ga akidar biliyoyin Kiristoci da Musulmai a duniya. Kun yi gargaɗi da kyau cewa “bai kamata a yi amfani da sakon Injila don ruɗaɗɗiyar manufa ba.” Wannan lamari yana nuna yadda wasu masu mulki za su iya kai wa ga karkatar da gaskiya da cin zarafin abubuwa masu tsarki don jan hankalin jama’a. Amma gaskiya ba ta ɓoyuwa da ƙarya da cin zarafi.
Mai girma; kun tabbatar cewa jagorancin coci ba ya durƙusawa a gaban masu zalunci kuma ba ya yin shiru saboda muradun siyasa. Cin mutunci da barazanar da Trump ya yi ba su rage matsayin ku ba, sai dai sun ƙara daraja da tsarkin matsayinku. Tarihi zai tuna da mutane masu son zaman lafiya, ba da waɗanda suka bar abin kunya da wulakanci ta hanyar cin mutunci ga abubuwa masu tsarki da barazanar lalata al’adu ba.
Cin mutuncin Trump ga jagoran Kiristocin Katolika na duniya, a hakikanin gaskiya, cin mutunci ne ga miliyoyin mutane masu neman rayuwa cikin zaman lafiya. Yana zato cewa da furucin zagi za a iya kashe muryar lamiri; alhali kuwa wannan cin mutunci hujja ce ta fasadi da lalacewa da ƙasƙantar mutuncin wanda ya aikata shi.
A ƙarshe, muna sake nuna godiya ga wannan matsayi mai ƙima naku, tare da roƙon Ubangiji Mai Girma ya tabbatar da adalci da zaman lafiya a ko’ina cikin duniya.
Muhsin Araki
Ra'ayinka