Alhamis 19 Maris 2026 - 00:29
Saƙon Ta’aziyyar Shahadar Mujahidi Dr. Ali Larijani Daga Cibiyar Albasira  

Hauza/ Cibiyar Albasira Qom Karkashin Jagorancin Sheikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) ta mika ta'aziyyarta kan ziyarar Mujahidi Dokta Ali Larijani ta hannun mafi sharrin mutane, Amurka da Isra'ila.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Cibiyar Albasira Qom Karkashin Jagorancin Sheikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) ta fitar da sanarwar ta'aziyyar Shahadar Dr. Ali Larijani. Cikakkiyar sanarwar ita ce kamar haka:

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيمِ

إِنَّا لِلّهِ وَإِنَّا إِلَيْهِ رَاجِعُون

«ولاتَحسبَنَّ الّذینَ قُتِلوا فی سبیلِ‌اللهِ اَمواتاً بَل اَحیاءٌ عِندَ رَبِّهِم یُرزَقون»

Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai 

"Lallai daga Allah muke, kuma zuwa gare Shi ne za mu koma".

“Kada ka yi zaton waɗanda aka kashe a hanyar Allah sun mutu — a’a, suna raye wurin Ubangijinsu, Yana azurtasu.” (Ali Imran: 169)

Cibiyar Albasira Qom Karkashin Jagorancin jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), tana miƙa saƙon ta’aziyya da juyayi bisa shahadar zalunci ta Dr. Ali Larijani, gwarzon mujahidi kuma amintaccen mai bin tafarkin Imam da Jagora.

Muna miƙa wannan ta’aziyya ga Jagoran Musulmi na Duniya, Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamenei (D), iyalansa masu daraja, da kuma al’ummar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Shahadar wannan bawan Allah mai tsoron Allah alama ce cewa maƙiyan Juyin Juya Halin Musulunci har yanzu ba su fahimci zurfin imani da jajircewar mazajen wannan tafarki ba. Suna tsammanin ta hanyar kisan gilla da ta’addanci za su iya dakatar da tafarkin juyin juya hali, alhali kuwa jinin shahidai shi ke ƙara haskaka tafarkin gaskiya, kuma yake ƙarfafa juriya da wayewar al’umma.

Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) da mabiyan tafarkin gwagwarmaya a Nijeriya suna yin Allah wadai da wannan mummunan aiki, tare da gargaɗi ga masu girman kai da zalunci su sani cewa ba za a iya kashe muryar gaskiya da harsasai ba, domin shahadar mujahidai ita ce fitila da ke ƙara haskaka tafarkin gwagwarmayar al’ummar Musulmi.

Muna roƙon Allah Madaukaki Ya karɓi shahadar wannan bawanSa mai daraja, Ya ba shi matsayi tare da shahidai da salihai, kuma Ya tabbatar da tafarkin da ya sadaukar da rayuwarsa a kai.

Cibiyar Albasira Qom Karkashin Jagorancin Sheikh Ibraheem Zakzaky (H)

28 Ramadan 1447

18 Maris 2026

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha