Asabar 29 Nuwamba 2025 - 05:51
 Idan Kana So Ɗanka Ya Samu Tarbiyya, Farko Ka Inganta Uwar

Hauza/ A tarbiyyar ɗan shekara huɗu, rawar da "Uwa Mai Ilimin Tarbiyya" ke takawa ita ce ginshiƙi, kuma Uba ya kamata ya mara mata baya, ba wai ya yi mata adawa ba. Idan Uwa tana da basira da ilimin da ya dace, shugabantar ɗan zai yi tasiri. Uba yana kiyaye darajar koyarwar ta - ga yaran, ya saukake hanyar haɗuwa da ita - don inganta tarbiyyar, kuma haɗin kai tsakanin iyaye shi ne mabuɗin nasarar tarbiyya.

A cewar Kafar watsa Labaran ta Hauza, Hujjatul Islam wal-Muslimin Sayyid Ali Reza Tarashiyoun, gwani a fannin iyali da tarbiyyar yara, a cikin tambayoyi da amsoshi, ya yi bayani kan batun "Tarbiyya Mai Tasiri tare da Uwa" wanda ake gabatar wa gare ku masu ilimi.

Tambaya: Muna da ɗa mai shekara huɗu. Don tafiyar da lamarin tarbiyyar sa, ni da matata ba ma cimma matsaya. Kullum duk abin da ya dame ni, a wurin matata ba ya haifar da maslaha - gyara, kuma hakan ya sa ɗanmu ba ya jin maganar ko ɗayanmu. Don Allah a ba ni shawara.

Amsa: Iyaye maza bai kamata su tsoma baki da yawa a cikin harkokin tarbiyya ba. Bayanin da nake son nakawo shi ne cewa, a tarbiyya, muna buƙatar “Uwa Mai Ilimi” kuma Uba ya zama yana tare da uwa Mai Ilimi - kan aikin tarbiyya.

Amma menene ma'anar “Uwa Mai Ilimi”? wata- Uwa ce da ta san dukkanin fannukan tarbiyyar ta, ta ɗaukaka matakin iliminta, ta ƙarfafa basirarta, kuma tana da isasshen iko da ya dace don tarbiyyar ɗa. Wannan Uwa tana taka rawar shugabar tarbiyya.

Bari in ba da misali don bayyana batun: Ka yi tunanin a makaranta, ni, a matsayina na Shugaba, ina son ci gaba da sukar malami ko in yi adawa da kowane jumla.

A irin wannan yanayin, yara ba za su ƙara sauraron malamin ba kuma ba za su girmama ni, ni Shugaban ba. Me ya sa? Domin darajar malamin a idon ɗalibin ta ragu.

Haka ma ke faruwa a zmantakewar iyali: Idan Uba ya rage darajar Uwa a idon ɗa, ɗan ba zai ƙara jin maganar Uwa ba kuma ba zai yi koyi da Uba ba.

Yara suna gani cewa manyan kansu ba su warware matsalolinsu ba, kuma saboda haka, matakan tarbiyyar da suka ɗauka don ɗan ba su da wani tasiri.

Don haka, aikinmu shi ne farko mu ɗaukaka matakin ilimin iyaye mata a tarbiyyar yara.

Manufar wannan shiri da kwasa-kwasan shi ne mayar da Uwa zuwa "Uwa Mai Ƙarfi": Uwa mai ilimin tarbiyya, wadda ta samu basirar da ta dace kuma tana da cikakkiyar masaniya.

Wannan Uwa ce ke shiga fagen tarbiyya kuma ta ɗauki tako a rawar shugabanci.

Me Uba ya kamata ya yi a cikin wannan tsari? Uba ya kamata ya mara wa Uwa mai ilimi baya, ba wai ya tsoma baki ko ya yi adawa da ita ba.

Goyan bayan Uba yana sa ɗa ya karɓi koyarwa da - bin shugabanci mafi kyau, kuma tarbiyyar ta kasance mai tasiri.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha