Laraba 4 Nuwamba 2026 - 12:31
Manyan Ginshiƙai Huɗu na Alƙur’ani Wajen Gina Ra’ayin Jagoranci a Duniyar Musulunci

Hauza/ A zaman share fage na taron ƙasa da ƙasa mai taken "Duniyar Musulunci da Buƙatun Gina Ra’ayin Addini da Al’adu a Zamanin Yanzu", wanda aka gudanar a ranar Talata, 12 ga watan Aban 1405 (03/11/2026), Hujjatul Islam wal Muslimin Ahmad Mabalighi, mamba a Majalisar Kwararru ta Jagoranci a Iran kuma shugaban Majalisar Ilimin Binciken Addini ta Ƙasa, ya yi bayani kan tushen gina ra’ayi bisa Alƙur’ani da rawar da al’ummar Musulmi za ta taka a duniyar yau.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, a zaman share fage na taron ƙasa da ƙasa mai taken "Duniyar Musulunci da Buƙatun Gina Ra’ayin Addini da Al’adu a Zamanin Yanzu", wanda aka gudanar a ranar Talata, 12 ga watan Aban 1405 (03/11/2026), Hujjatul Islam wal Muslimin Ahmad Maballighi, mamba a Majalisar Kwararru ta Jagoranci a Iran kuma shugaban Majalisar Ilimin Binciken Addini ta Ƙasa, ya yi bayani kan tushen gina ra’ayi bisa Alƙur’ani da rawar da al’ummar Musulmi za ta taka a duniyar yau.

Da yake dogaro da aya ta 143 a cikin Suratul Baƙara, Mabalighi ya bayyana manyan ginshiƙai huɗu na gina ra’ayi a duniyar Musulunci kamar haka:

1. Ginawa da ƙarfafa asalin al’umma: Al’ummar Musulmi wajibi ne ta kiyaye asalinta na musamman tare da ƙarfafa wayewa da ɗaukar nauyin da ya rataya a kanta, domin taka rawar gani a fagagen zamantakewa da na duniya.

2. Samar da daidaito: Ma’anar kasancewa "Ummatan Wasaɗan" tana nufin samar da daidaito cikin hikima tsakanin haƙƙoƙi, ƙimomi da nauyin da ke kan al’umma, ba wai kawai tsayawa a tsakiyar ra’ayoyi biyu ba.

3. Ƙarfafa haɗin kai: Haɗin kai da haɗa ƙarfi tsakanin Musulmi, duk da bambancin mazhabobi da al’adu, na daga cikin muhimman abubuwan da ke ƙara ƙarfin al’ummar Musulmi da tasirinta. Saɓani da rikice-rikicen cikin gida kuwa na iya raunana wannan matsayi.

4. Samar da ma’anoni masu ma’ana ga kowa: Gina ra’ayi ya kamata ya dogara da abubuwan da suka haɗa ɗaukacin bil’adama, kamar adalci, kyautatawa da yaƙi da zalunci, domin saƙon Musulunci ya kasance mai sauƙin fahimta da karɓuwa ga al’ummomin duniya.

Hujjatul Islam Maballighi ya kuma jaddada cewa bai kamata asalin Musulunci ya zama sanadin killace kai ko nisantar sauran al’ummomi ba. Maimakon haka, ya kamata a gina shi bisa koyarwar Manzon Allah (SAWA), neman adalci, zaman lafiya da kyakkyawar hulɗa da sauran al’ummomin duniya. Ya bayyana gabatar da kyawawan koyarwar Ahlul Baiti (AS) a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin sadarwa masu tasiri da sauran al’ummomi.

A wani ɓangare na taron, Ayatullah Payman, babban sakataren Ƙungiyar Nazarin Shi’a ta Duniya, ya yi nuni da irin gudummawar da Majalisar Masu Binciken Addini ta Ƙasa ta bayar wajen bunƙasa bincike da ayyukan ilimi a makarantun Hauza. Ya kuma bayyana ci gaban da aka samu a fannonin ilimi, koyarwa da faɗaɗa sabbin batutuwan Fiƙihu.

Haka kuma, Hassan Nourbakhsh, shugaban sashen Addini da Nazarin Duniya na Sakatariyar Masu Binciken Addini ta Ƙasa, ya bayyana cewa duniyar yau fagen fafatawar ra’ayoyi ne, yana mai cewa samun matsayi mai tasiri ga duniyar Musulunci a wannan fage yana buƙatar ingantaccen tushen ilimi, tunani da bincike.

An gudanar da wannan zama ne domin nazarin hanyoyin ƙarfafa ra’ayin addini da al’adu, tare da samar da damar da duniyar Musulunci za ta taka rawar gani ta fuskar ilimi da tunani a matakin ƙasa da ƙasa.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha