A Cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, babban Malamin addinin Musulunci, Ayatullah al-Uzma Wahid Khurasani, ya bayar da amsa kan tambayar da aka yi masa dangane da amfani da kuɗin Aro (Rance) a wani abu daban ba wanda aka ware shi domin sa ba.
Tambaya:
Shin ya halatta mutum ya yi amfani da kuɗin aro (rance) domin gina gida wajen wani abu daban? Ko kuma ya yi amfani da kuɗin rancen sayen mota wajen wani abu kamar sayen fili?
Amsa:
A'a, bai halatta ba. Dole ne a yi amfani da kuɗin lamunin ne a kan manufar da aka ware shi domin ta kawai.
Ra'ayinka