Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa, Ayatullah Nuri Hamedani ya fitar da saƙon ne bayan yanke hukuncin ɗaurin kurkuku da hukuncin kisa ga wasu malamai a ƙasashen yankin.
Ga fassarar cikakken saƙon nasa:
Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Ƙai.
Tare da miƙa ta’aziyya bisa zagayowar kwanakin shahadar Sayyida Fatima Zahra (AS).
“Malaman Shi’armu suna tsaye a matsayin masu gadin iyakar da ke fuskantar Iblis da aljanunsa. Suna hana su cutar da raunanan mabiya Shi’a, tare da hana Iblis da mabiyansa masu adawa da Ahlul Baiti mamaye su.”
Wannan magana mai haske tana tunatar da mu muhimmancin matsayin malamai wajen kare imanin mutane da tsayawa tsayin daka a kan tafarkin gaskiya, tare da fuskantar ɓangaren ƙarya.
Aikin malamai shi ne kare gaskiya, yaƙi da zalunci da danniya, da kuma kiyaye iyakokin aƙida. Saboda haka, duk inda aka aikata zalunci, wajibi ne malamai su ɗaga muryoyinsu wajen yin Allah-wadai da shi. Haka kuma, duk wani hari ko cin zarafi da aka yi wa malaman da suke ƙoƙarin kare aƙidar addini da haƙƙoƙin al’ummarsu abin Allah-wadai ne.
A ’yan kwanakin nan, wasu shugabannin ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya sun ɗauki matakin yanke hukuncin zalunci kan malamai, ciki har da ɗaurin kurkuku da hukuncin kisa, da nufin dakatar da muryar gaskiya da adalci.
Ya kamata a fahimci cewa irin waɗannan hukunce-hukunce ba za su iya daƙushe muryar gaskiya da adalci ba. Maimakon haka, za su iya zama sanadin faɗuwar waɗanda suka yanke su da kuma rasa mutuncinsu a idon al’umma.
Saboda haka, muna ba shugabannin waɗannan ƙasashe shawarar su daina irin waɗannan matakai na rashin hikima. Maimakon su yi fito-na-fito da malamai, ya kamata su haɗa kai da su wajen yaƙi da girman kai da danniyar manyan ƙasashe, da kuma Sahayoniyawa, waɗanda suke neman kawar da tushen Musulunci.
Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya ɗaukaka Musulunci, Ya ba wa malaman da ake zalunta nasara, kuma Ya kuɓutar da su daga hannun azzalumai.
Husaini Nuri Hamedani
6 ga Aban 1405 (28 Oktoba 2026)
Ra'ayinka