Asabar 24 Oktoba 2026 - 20:35
Ta Yaya Za a Sake Bayyana Sirar Sayyida Fatima (S) a Matsayin Abin Koyi ga ’Yan Mata da Mata a Yau?

Hauza/ Babu shakka, sira da rayuwar Sayyida Faɗima Zahra (AS) su ne mafi kyawun abin koyi wajen juriya da tsayin daka ga al’ummar bil’adama a fannoni na rayuwar mutum da zamantakewa, musamman ga mata da ’yan mata.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya rawaito cewa, muna cikin kwanakin tunawa da shahadar cikin zalunci ta Sayyida Fatima Zahra (AS), shugabar matan talikai. A bisa wannan dalili ne muka gudanar da wata tattaunawa da Dakta Ma’asuma Nasiri, malama kuma mai bincike a fannin ilimin kafofin watsa labarai. Ga cikakkiyar tattaunawar kamar yadda ta zo a ƙasa:

Tambaya: A zamanin da al’adun son amfani da kayayyaki fiye da buƙata da nuna kai a kafafen yaɗa labarai suka yaɗu, ta yaya za a sake bayyana sirar Sayyida Fatima Zahra (AS) a matsayin abin koyi da zai gina asalin mutuntaka da sanin kai ga ’yan mata da mata na yau, domin su samu rabauta a duniya da lahira?

Amsa: Kun taɓo wani muhimmin batu ta hanyar wannan tambaya. Haƙiƙanin magana ita ce, muna rayuwa a wani zamani da, abin takaici, ake kallon mace a matsayin wani abu da ake amfani da shi. Wannan batu ya ƙara samun muhimmanci da ma’ana a wannan zamani da ake yaɗa al’adun son amfani da kayayyaki fiye da buƙata.

Sai dai ina so in bayyana cewa, ni ba na goyon bayan a taƙaita magana kan sirar Sayyida Fatima (AS) ga rayuwarta ta sauƙin kai da sauƙin rayuwa kawai. A maimakon haka, ya kamata mu kalli sirar wannan babbar baiwar Allah, wadda take Sayyidatu Nisa’il Alamin (Shugabar Matan Talikai), a matsayin ginshiƙi da tsarin tunani na mazhabar Shi’a. Ya kamata mu yi nazari kan muhimman abubuwan da suka ƙunshi wannan sira, sannan mu bayyana su yadda ya kamata ga dukkan al’ummar bil’adama, ba ga al’ummarmu kaɗai ba.

Tabbas, idan muka kalli wannan babbar halitta ta tarihi, addini da ɗan’adam ta wannan fuska, za mu samu hanya mafi dacewa da inganci wajen gabatar da misalan rayuwa da za su taimaka wa mata wajen fahimtar asalinsu da matsayin kansu. Wannan zai taimaka mana wajen cimma manufarmu.

Abin da yake tabbatacce shi ne, Sayyida Fatima (S) tana da fannoni daban-daban na rayuwa mai nasara ta fuskar zamantakewa, al’adu da tarbiyya. A ganina, ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da za a iya mayar da hankali a kansu domin gina abin koyi ga mata shi ne fahimtar yanayi da matsayi, sanin lokacin da ya dace a ɗauki mataki, da kuma ayyana rawar da mutum zai taka a cikin al’umma ta wata hanya daban da ra’ayoyin da suka zama ruwan dare a cikin al’umma.

Sayyida Fatima Zahra (S) ta kula da waɗannan batutuwa a zamaninta, kuma ta taka wannan muhimmiyar rawa da ta zama abin koyi.

Ya kamata mata da ’yan matanmu su fahimci cewa, ba lallai ba ne duk abin da ya mamaye kafafen yaɗa labarai ko ya zama ruwan dare a salon rayuwar mutane ya kasance daidai. A yau, muna kiran wannan yanayi da sunan son amfani da kayayyaki fiye da buƙata da kuma nuna kai a kafafen yaɗa labarai.

Ina ganin cewa, idan muka yi nazari mai zurfi kan rayuwar Sayyida Fatima (AS), za mu ga cewa ta tsaya tsayin daka wajen fuskantar munanan al’adun da suka mamaye al’umma a zamaninta. Ta yi ƙoƙarin tsara rayuwarta da ɗabi’unta bisa hanyar bautar Allah, tabbatar da gaskiya da kare Wilaya.

Idan muka iya gina ƙarfin zuciya da jajircewa a cikin ’yan matanmu, ta yadda za su fahimci cewa ba lallai ne abin da ake tilasta musu ko ake gabatar musu da shi a matsayin abin da ya dace ya zama gaskiya ba, za mu taimaka musu wajen zaɓar hanyar rayuwa mafi kyau. Haka kuma, za su iya kauce wa faɗawa ƙarƙashin tasirin tunani da ra’ayoyin da suka mamaye al’ummarsu a kowane zamani.

A ganina, wannan yana daga cikin hanyoyin da za a bi wajen sake bayyana sirar Sayyida Fatima (S) ga matan yau.

Saboda haka, taƙaita sirar Sayyida Fatima (SA) ga sauƙin rayuwa kawai yana nufin rage girman matsayinta da dimbin abubuwan da rayuwarta ta ƙunsa. Domin tana da fannoni daban-daban na ɗabi’a, halayya, ruhaniya da ma’anoni masu zurfi a tunaninta. Ya kamata a bayyana waɗannan muhimman abubuwa yadda ya kamata, cikin harshen da ya dace da zamaninmu, domin jama’a su fahimce su, musamman mata da ’yan mata.

Tambaya: Ta yaya za a sake bayyana sirar Sayyida Fatima (S) ga mata da ’yan mata na yau?

A cikin sirar Sayyida Zahra (S), ana iya kallon ma’anar haya (kunya) a matsayin wani abu da ya wuce batun tufafi, wato wata ginshiƙiyar ɗabi’a da take fitowa daga cikin mutum. A ra’ayinki, ta yaya wannan ɗabi’a za ta iya zama garkuwa wajen kare mata daga rikicin rasa asalin mutuntaka da rugujewar ƙimomi a duniyar intanet da kafafen sada zumunta?

Amsa: Duba, batun kunya ko kamun kai yana da alaƙa da sutura, amma ya kamata a fahimci cewa, kasancewar mutum yana sanya sutura mai rufe jikinsa ba yana nufin cewa lallai yana da kunya ko kamun kai ba. A nan ne tambayar take tasowa: Ta yaya ake haɗa waɗannan abubuwa biyu?

Amsar ita ce, hakan yana samuwa ne daga tsarin tarbiyya da ginshiƙin ɗabi’a ta cikin mutum, wadda ta samo asali daga koyarwar tarbiyya. Wato mutum yana suturta jikinsa, kuma a lokaci guda yana da kamun kai da kunya. Wannan muhimmin batu ne da ya kamata mu kula da shi.

Batun kamun kai da kunya, tare da sutura, yana da alaƙa da yadda mutum ya gina darajar kansa a cikin zuciyarsa. A nan muna magana ne musamman kan mata. Tambayar ita ce: Ta yaya mutum zai gina ingantacciyar darajar kansa? Wannan darajar kai ce, idan aka haɗa ta da kunya, kamun kai da sutura, za ta iya zama garkuwa kuma wani muhimmin ginshiƙi wajen tunkarar sabbin ra’ayoyin da kafofin watsa labarai suke ƙirƙirawa dangane da asalin mutuntaka. Sai dai a nan, zan ƙetare batun kawar da asalin mutuntaka.

A yau, duniyar intanet ta zama wani wuri ko alamar da ake ganin yaɗuwar halaye marasa kamun kai da kuma ayyukan da suke raunana kunya. A ganina, idan muka tsaya tsayin daka wajen ƙarfafa darajar kai, a matsayin wani muhimmin tunani na ilimin halayyar ɗan’adam, tare da ƙimomin kamun kai, sutura da kunya, za mu iya sarrafa tasirin sabbin siffofin asalin mutuntaka da kafafen watsa labarai suke ginawa, waɗanda suke adawa da tsarin ƙimominmu.

Tambaya: A ra’ayinki, ta yaya za a yi amfani da tsarin ɗabi’a na Sayyida Fatima (AS) wajen fuskantar ƙalubalen rayuwa, domin ƙarfafa juriyar zamantakewa a tsakanin matasa? Haka kuma, wane irin salo ya kamata a bi wajen gina ra’ayoyin kafafen yaɗa labarai da yaɗa su, musamman wajen bayyana wannan tunani bisa koyarwa da salon rayuwar Fatimiyya?

Amsa: Amsar da ta zo mini a wannan tambaya ita ce, Sayyida Fatima Zahra (AS) cikakkiyar abin koyi ce ta gwagwarmaya da tsayin daka. Wannan gwagwarmayar tana samuwa ne daga wani ginshiƙi na tunani da tarbiyya, tare da tabbataccen imani da ke cikin zuciya.

Tabbas, ita ’yar Manzon Allah ce, Annabin da ya zo da addini kuma ya kafa shi. Sayyida Fatima (AS) ta kasance a tsakiyar muhimman al’amura da abubuwan da suka faru a tsawon rayuwar siyasa ta mahaifinta, Manzon Allah na ƙarshe (SAWA), kuma ta fuskanci waɗannan al’amura kai tsaye.

A rayuwarta tare da Imam Ali (AS), da kuma lokacin fuskantar maƙiyan Musulunci da Wilaya waɗanda, abin mamaki, wasu daga cikinsu suna cikin tsarin Musulunci da kansa ko kuma aƙalla suna nuna kamannin Musulunci a zahiri, mun ga yadda ta nuna juriya a fannoni daban-daban na rayuwa. Hakan ya bayyana a cikin al’amura da dama, kamar batun Fadak da Saƙifa da sauransu.

A waɗannan abubuwa, muna ganin juriya a rayuwar zamantakewa, rayuwar iyali, har ma da fannin tattalin arziki.

Saboda haka, ya kamata matanmu su fahimci tsarin rayuwar Sayyida Fatima (AS) ta hanyar nazari mai zurfi. Musamman, ya kamata su san cewa idan mutum yana son ya bar abin tunawa mai ɗorewa a tarihi, dole ne ya kasance mai juriya. Wannan juriya ce take sa mutum ya zama abin tunawa a cikin al’umma.

A ganina, idan mata suka fahimci wannan batu, za su fi fahimtar irin rawar da za su iya takawa a cikin al’umma. Wannan tsarin tarbiyya ne wanda ya samar da manyan mutane kamar Imam Hasan (AS), Imam Husain (AS) da Sayyida Zainab Kubra (SA), waɗanda aka gabatar wa al’ummar bil’adama a matsayin fitattun misalai.

Saboda haka, wannan tsari cikakke ne kuma an tsara shi bisa hikima. Gwagwarmaya tana nufin tsayawa kan ƙa’idoji, bin hanyar gaskiya da tabbatar da haƙiƙa. Wannan tsayin daka na Sayyida Fatima (AS) ne a ƙarshe ya kai ga shahadarta cikin zalunci.

Abu mafi muhimmanci shi ne, ya kamata mu bayyana fannoni daban-daban na sira da rayuwar Sayyida Fatima (S), tare da yin bayani kan tasirin juriya da take ɗorewa na dogon lokaci ga mata a cikin al’umma.

Ya kamata mu yi bayani kan yadda mace, a matsayinta na mace, za ta iya amfani da gwagwarmaya wajen gina al’umma mai gwagwarmaya da kuma iyali masu gwagwarmaya. Haka kuma, ya kamata a fahimci yadda mace za ta iya yin amfani da sanin yanayin tarihi da matsayin da take ciki wajen gina matsayi mai ƙarfi da muhimmanci a cikin al’umma.

A ganina, ba mu yi isasshen aiki a wannan fanni ba. Sayyida Fatima (S) tana daga cikin mata kaɗan da suka kasance masu hangen nesa da ɗaukar mataki a tarihin ɗan’adam.

A lokacin da aka samu abin da ake kira karkatar da ra’ayin jama’a zuwa ga yin shiru (Spiral of Silence), inda aka yi ƙoƙarin mayar da mutane yin shiru game da Imam Ali (AS), Musulunci da Wilaya, Sayyida Fatima (S) ta tsaya tsayin daka kuma ta karya wannan shirun.

A wuraren da ake buƙatar ɗaukar mataki a aikace, ta ɗauki mataki. A wuraren da ake buƙatar yin bayani da fayyace gaskiya, ta yi hakan. A wuraren da ake buƙatar yin shiru bisa ilimi da hikima, ta yi shiru. Ta sauke nauyin da ke kanta da kuma abin da ya wajaba a gare ta yadda ya kamata kuma cikin cancanta.

Saboda haka, fahimtar yanayi da matsayin da take ciki na iya taimaka mana matuƙa wajen amfani da rayuwarta a matsayin abin koyi mai amfani wajen gina al’umma.

Mai Tattaunawa: Sayyid Muhammad Mahdi Musawi

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha