A cewar wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Ayatullah Najmuddin Tabasi ya bayyana hakan ne a wajen taron tunawa da Hujjatul Islam wal Muslimin Sayyid Hassan Nasrullah (R.A), wanda aka gudanar a makarantar Hauzar Alawi da ke birnin Qum karkashin taken "Mutumin babu kamar sa a tarihin Sham," inda ya jaddada bukatar rubutawa da kuma gabatar da gadon tunani, al'adu, da siyasa na wannan babban jagora.
Ya kamata kowa ya ɗauki alkalami domin bayyana Shahid Sayyid Hassan Nasrullah
Ayatullah Tabasi ya bayyana cewa: "Bai kamata bayyana irin wannan mutum da ba a cika samun kamarsa ba ya takaitu ga gudanar da bukukuwan zagayowar ranar tunawa da shi ko wasu lokuta na musamman ba; maimakon haka, ya kamata a samar da ayyukan rubutu masu dorewa da za su zama abin tunawa game da shi, ta yadda tsararraki masu zuwa za su san shi."
Sayyidul Muƙawama mai biyayya ga Jagoranci (Wilaya)
Memba a kungiyar malaman makarantun Hauzar Qum, ya yi nuni da biyayyar Shahid Sayyid Hassan Nasrullah ga Wilaya, inda ya ce: "Shahid Nasrullah yana da kauna ta musamman ga Imam Shahid, kuma yana tafiya ne bisa tafarkin Wilaya."
Ya ba da wani labari game da Sayyid Hassan Nasrullah (R.A) inda ya ce: "A daya daga cikin tarukan ƙasashen Musulunci da aka gudanar a Tehran, bayan jawabin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Sayyid Hassan Nasrullah ya matsa ta cikin taron jama'a ya isa wurin Jagora kuma ya sumbaci hannunsa."
Ayatullah Tabasi ya ci gaba da cewa: "Sayyid Hassan Nasrullah ya taba cewa, yayin da mutane daga kasashen Larabawa da na Turai suke yin layi domin gaisawa da shi ko daukar hoto, shi (Sayyid) ya je ne domin sumbatar hannun Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, domin duniya ta san daga ina wannan ƙarfi da girman da yake da shi yake fitowa."
Karfin Sayyid Nasrullah ya samo asali ne daga makarantar Imam Khamene'i
Ayatullah Tabasi ya jaddada cewa Shahid Sayyid Hassan Nasrullah yana ganin ƙarfinsa yana da nasaba da Juyin Juya Halin Musulunci da Wilayatul Faƙih. Ya ce: "Sayyidul Muƙawama yana ganin wannan ƙarfi a matsayin wani abu da ya samo asali daga makarantar Imam Khamene'i (R.A), kuma yana da kula ta musamman ga lamurran Iran da makarantun Hauza."
Shahid Nasrullah ya sauya Lebanon
Game da rawar da Shahid Sayyid Hassan Nasrullah ya taka wajen sauya Lebanon, Ayatullah Tabasi ya ce: "Ayyukan Jagoran Muƙawama ba su takaitu ga bangaren soja ba, har ma da bangaren al'adu, inda aka tsara shirye-shirye masu fa'ida, kuma Hizbullah ta ba da kulawa ta musamman ga ayyukan al'adu da tarbiyya."
Ya ambaci kafa makarantun ilimi, makarantun boko, horar da malaman addini, da kuma shirya tarukan makokin Imam Husaini (A.S) a matsayin wasu daga cikin ayyukan da aka gudanar a wannan tafarki.
Tasirin Shahid Nasrullah ga tafarkin gwagwarmaya (Muƙawama)
Game da tasirin Shahid Nasrullah ga tafarkin gwagwarmaya, ya ce: "Ayyukan Shahid Nasrullah ba su takaitu ga Lebanon ba, har ma sun yi tasiri a kan tafarkin muƙawama a yankin." Ya kara da cewa wannan alaƙa ta al'adu da imani ta ƙarfafa hadin kai tsakanin ƙungiyoyin gwagwarmaya daban-daban da kuma al'adun Ahlulbaiti (A.S).
Makarantun Hauza sun tsaya ko da yaushe a gaban maƙiya
A wani bangare na jawabinsa, Ayatullah Tabasi ya ce: "Makarantun Hauza sun kasance ko da yaushe a kan gaba wajen faɗa da maƙiya, kuma malamai masu daraja a tarihinmu sun yi sadaukarwa domin kare addini da tafarkin Ahlulbaiti (A.S)."
Ƙarfin Iran a yakin da aka tilasta mata yana komawa ga tsare-tsaren Imam Shahid
A ƙarshe, Ayatullah Tabasi ya ce: "Maƙiya sun yi tunanin za su iya aiwatar da makarkashiyar da suka yi a Iraki ko Venezuela a cikin Iran, amma lissafinsu bai yi daidai ba game da Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Wannan ƙarfi da muke da shi sakamakon tsare-tsare ne na Imam Shahid (R.A), wanda ya riga ya tanadi komai kafin shahadarsa."
Ayatullah Tabasi ya sake jaddada buƙatar yin rubutu domin bayyana shaksiyyar Imam Shahid, yana mai cewa: "Dole ne a ɗauki alkalami a yi rubutu game da Imam Shahid, domin shi mutum ne na musamman da ba a cika samun kamarsa ba a wannan zamanin namu."
Ra'ayinka