A cewar rahoton sashen fassara na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Sheikh Maher Hammoud, Shugaban Kungiyar Malaman Gwagwarmaya ta Duniya, a yayin wani zama mai taken "Tabbatuwa da Biyayya" wanda aka gudanar a ofishinsa da ke birnin Saida domin tunawa da cika shekaru uku da fara Ɗufanul Aƙsa, ya bayyana cewa: "Muna sake jaddada cewa dukkan Yahudawa, walau 'yan Sahyoniya ko wadanda ba 'yan Sahyoniya ba, sun yi imani da tabbatuwar rugujewar kasarsu, kuma sun kayyade mata tsawon shekaru tamanin; wannan al'amari a bayyane yake a rubuce-rubucen Ben-Gurion wanda ya kafa har zuwa kan Ehud Barak."
Ya kara da cewa: "Muna gaskata ruwayoyin Yahudawa saboda akwai cikakkun bayanai a cikinsu; misali, an ambata a cikin littattafansu cewa rundunar da za ta shiga Labanon za ta tsaya ne a kauyen 'Sultan Yaqub' da ke tsakiyar kwarin Bekaa; wani karamin kauye da mutane da kyar suka san sunansa, kuma wannan shi ne ainihin abin da ya faru a shekarar 1982. Saboda haka, insha Allahu ruwayoyin Yahudawa a wannan fanni gaskiya ne, kuma suna kara karfafa yaƙininmu kan abin da ya zo a cikin Alkur'ani mai girma da hadisan Annabi."
Shugaban Kungiyar Malaman Gwagwarmayar ya ci gaba da cewa: "Wajibi ne a yi tir da kafafen yada labaran da ke ta maimaita cewa kungiyar gwagwarmaya ce ke da alhakin barnar da aka yi a kudancin Labanon (kamar yadda suke dora mata alhakin barnar da aka yi a Gaza); domin wadannan kafofin yada labarai tamkar suna neman kare laifukan 'yan Sahyoniya ne na cin zarafin bil'adama, barna da kisan kiyashi."
Sheikh Hammoud ya ci gaba da cewa: "Kishin kasar Labanon bai kamata ya zama mallakin wani bangare kadai ba; suna ikirarin cewa goyon bayan Gaza yana cin karo da kishin Labanon, alhali wannan ikirari ya saba wa mafi saukin ka'idojin dan'adamtaka da na kasar Labanon kanta."
Har ila yau ya kara da cewa: "Muna sukar wadanda ke bikin cika shekaru dari da tsara kundin tsarin mulki amma suka manta da rubuce-rubucen 'Michel Chiha' wanda ya yi tir da Sahyoniya. Chiha ya jaddada cewa idan har aka kafa kasar Sahyoniya a Falasdinu, to kasar Labanon ma ba za ta iya wanzuwa ba; saboda an kafa kasar Sahyoniya ne a kan aƙidar nuna wariyar launin fata, alhali kuwa Labanon za ta iya dorewa ne kawai ta hanyar maslaha da fahimtar juna tsakanin bangarori da mazhabobi daban-daban."
A wajen taron, sauran masu jawabi sun kuma jaddada cewa al'amuran 7 ga Oktoba sun cimma manufofi da dama a matakin duniya; mafi muhimmanci daga ciki shi ne farkawar al'ummomin duniya da dama game da muhimmancin batun Falasɗinu da kuma ta'addancin Sahyoniya. Wannan lamari ya sa Netanyahu ya fuskanci korafe-korafe a bangaren shari'a da na dan'adamtaka a duniya, ya fallasa makirce-makircen gwamnatocin da ke hada baki da 'yan Sahyoniya, ya ruguza shirye-shiryen kulla alaka da su (Normalisation), sannan ya bar su ba tare da wata kariya ba a gaban fushin al'ummomi, musamman dangane da abin da ake kira da "Addinin Ibrahimiyya".
A karshe, an bayyana cewa ba a auna nasara a yake-yake da adadin asarar da aka yi ba, a'a, ana auna ta ne da sakamakon da aka cimma da kuma yadda aka kammala wani mataki na yakin.
Ra'ayinka