A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Hujjatul Islam Muhammad Alamzadeh Nouri Ya bayyana cewa, bisa koyarwar Alƙur’ani mai girma, munafukai a kodayaushe suna ƙoƙarin bayyana kansu a matsayin muminai, masu kishin al’umma kuma masu son gyara, tare da amfani da kalamai masu jan hankali da kuma fitowa da fuskar da jama’a suka yarda da ita domin yin tasiri a kan ra’ayoyin jama’a.
Mataimakin Daraktan Harkokin Tarbiyya da Gyaran Halayen Makarantun Hauza ya ƙara da cewa gane munafukai da kuma tunkarar su ba abu ne mai sauƙi ba. Ya ce wasu lokuta irin waɗannan ƙungiyoyi kan samu karɓuwa da goyon bayan jama’a, don haka yin mu’amala da su ta hanyar da ba ta dace ba na iya cutar da haɗin kai da zaman lafiyar al’umma.
Hujjatul Islam wal Muslimin Alamzadeh Nouri ya bayyana jihadin bayyana gaskiya (Jihadut Tabyin) a matsayin ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin tunkarar masu yaudara, yana mai jaddada muhimmancin bayyana wa jama’a ainihin halaye da manufofin irin waɗannan ƙungiyoyi.
Ya kuma jaddada cewa haɗin kai da ɗorewar zumunci a tsakanin al’umma suna da matuƙar muhimmanci wajen cimma manufofin Musulunci. Ya ce fitintinu da jarabawoyi na iya zama wata dama ta gane muminai na gaskiya da kuma bambance su da masu tafiya a kan karkatacciyar hanya.
A ƙarshe, ya bayyana ranakun Fatimiyya a matsayin wata dama mai kyau ta yin bayani kan batun munafunci, nazarin misalansa na tarihi da kuma ƙara wayar da kan al’umma game da hanyoyin da masu yaudara ke amfani da su wajen yaɗa tunaninsu.
Ra'ayinka