Lahadi 30 Agusta 2026 - 19:18
Ranakun Mauludin Manzon Allah, Lokacin Sake Nazarin Matsayar Al'ummar Musulmi

Hauza/ Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gana da malamai da mahalarta taron Makon Haɗin Kan Musulmi da Harkar Musulunci ta shirya a Abuja, a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen bikin Mauludin Manzon Allah (S.A.W.A).

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gana da malamai da mahalarta taron Makon Haɗin Kan Musulmi a ranar Asabar, 16 ga Rabi’ul Awwal 1448, daidai da 29 ga Agusta 2026, a gidansa da ke birnin Abuja.

A yayin ganawar, Jagora (H) ya bayyana cewa lokacin Mauludi wata dama ce da ya kamata al’ummar Musulmi su yi amfani da ita wajen waiwayar kansu, tare da yin nazari kan irin matsayar da suka ɗauka wajen bin saƙon da Manzon Allah (S.A.W.A) ya zo da shi, da kuma tunani kan irin al’ummar da Manzon Allah (S.A.W.A) ya gina ya kuma bari a baya.

Ya ce bikin Mauludi bai kamata ya kasance kawai lokacin nuna farin ciki da tunawa da haihuwar Manzon Allah (S.A.W.A) ba, a maimakon haka ya kamata ya zama lokaci na sake duba rayuwar al’ummar Musulmi da kuma yadda suke aiwatar da koyarwar Manzon Allah (S.A.W.A).

Haɗin kan Musulmi

A ci gaba da jawabinsa, Jagora (H) ya jaddada muhimmancin haɗin kan al’ummar Musulmi, yana mai bayyana cewa haɗin kai ba yana nufin mutum ya yi watsi da fahimtarsa ta addini ya karɓi fahimtar wani ba.

A cewarsa, ma’anar haɗin kai ita ce girmama fahimtar juna, yin uzuri ga juna da kuma kusantar juna, duk da kasancewar akwai bambance-bambancen fahimta a wasu fannoni.

Ya bayyana cewa irin wannan haɗin kai zai taimaka wajen kawar da shingayen gaba, ƙiyayya da rashin fahimtar juna da maƙiya suka sanya tsakanin al’ummar Musulmi.

Ci gaba da taron Makon Haɗin Kai

Taron Makon Haɗin Kan Musulmi a Abuja ya shiga rana ta huɗu tun bayan fara shi, inda malamai daban-daban daga sassa daban-daban na al’ummar Musulmi suka halarta tare da gabatar da jawabai kan batutuwa daban-daban da suka shafi haɗin kan Musulmi da koyarwar addinin Musulunci.

An bayyana cewa za a gudanar da bikin rufe taron a ranar Lahadi, 30 ga Agusta 2026, da misalin ƙarfe 10:00 na safe a Abuja, inda kuma za a gudanar da gagarumin taron Mauludin Manzon Allah (S.A.W.A).

Taron na daga cikin shirye-shiryen tunawa da zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah (S.A.W.A) da kuma ƙarfafa ruhin haɗin kai, 'yan'uwantaka da fahimtar juna tsakanin al’ummar Musulmi.

Jagora (H) Ya Gana da Malamai da Mahalarta Taron Makon Haɗin Kan Musulmi a Abuja

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha