A cewar wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Hauza daga Mashhad, Ayatullah Subhani ya bayyana hakan ne a zaman darasinsa na huɗu ga ɗaliban makarantar bazara ta “Darul-Ilm”, da ake gudanarwa a Makarantar Mirza Ja’afar, wadda ke ƙarƙashin Jami’ar Kimiyyar Musulunci ta Razavi.
Da yake ci gaba da bayanin darussan baya, Ayatullah Subhani ya ce a zaman ukun da suka gabata sun tattauna batun “Kubra”, wato mutane ne ya kamata su zaɓi matsayin wilaya da imamanci, ko kuma Allah ne Ya naɗa shi.
Ya bayyana cewa binciken siyasa da na cikin gida ya tabbatar da cewa wannan matsayi ya kamata ya kasance naɗaɗɗe daga Allah, ma’ana Allah Ya zaɓa kuma Ya tarbiyyantar da wani mutum domin ya ɗauki nauyin dukkan ayyukan da Manzon Allah (S.A.W.A.) yake da su. Ya ce wannan shi ne abin da ake kira “Kubra”. Amma batun wanda Allah Ya naɗa shi shi ne “Sugra”, kuma wannan yana buƙatar komawa ga hadisai da tarihi.
Ayatullah Subhani ya ƙara da cewa idan aka nazarci tarihin Musulunci tun daga lokacin da aka aiko Manzon Allah (S.A.W.A.) har zuwa yau, za a ga cewa tun ranar da aka sanar da manzancin Annabi (S.A.W.A.), an kuma fara bayyana matsayi da wilayar Ali bn Abi Talib (A.S.).
Kiran makusantan Annabi da kuma bayyana matsayin Imam Ali
Da yake ishara da ayar «وَأَنذِرْ عَشِیرَتَ الْأَقْرَبِینَ» “Ka yi wa danginka mafi kusa gargadi”, Ayatullah Subhani ya ce wannan aya ta sauka a shekara ta uku bayan fara wahayi. Allah Ya umarci Annabi (S.A.W.A.) da ya fara kiran makusantansa zuwa Musulunci.
Ya ce Manzon Allah (S.A.W.A.) ya gayyaci mutane kusan arba’in, sannan Imam Ali (A.S.) ya shirya musu abinci.
A rana ta farko, Abu Lahab ya faɗi wata magana da ta kawo cikas ga taron, don haka Annabi (S.A.W.A.) bai ci gaba da batun ba. Washegari kuma ya sake gayyatar su, sai suka zo ban da Abu Lahab.
Annabi (S.A.W.A.) ya bayyana musu cewa shi Manzon Allah ne da aka aiko domin shiryar da su, sannan ya tambaye su wanda zai taimaka masa a wannan lamari ya kasance ɗan’uwansa, wazirinsa da halifansa a cikinsu.
Ayatullah Subhani ya ce babu wanda ya tashi daga cikin waɗanda suke wurin, sai Imam Ali (A.S.), wanda a lokacin yana kusan shekara ashirin. Imam Ali (A.S.) ya ce: “Ya Manzon Allah.”
Ya bayyana cewa bayan Annabi (S.A.W.A.) ya maimaita tambayar har sau uku, a karo na uku ne ya bayyana cewa Ali (A.S.) ɗan’uwansa ne, wasiyyinsa, wazirinsa kuma halifansa a cikinsu.
Ya ce wannan ruwaya an kawo ta daga bangarorin Ahlus-Sunna da Shi’a wajen tafsirin ayar “Ka yi wa danginka mafi kusa gargadi”, kuma hakan yana nuna cewa sanar da manzancin Annabi (S.A.W.A.) ya zo tare da bayyana matsayin Ali (A.S.).
Hadisin Manzila da Hadisin Thaqalaini
Ayatullah Subhani ya kuma yi ishara da Hadisin Manzila, inda Annabi (S.A.W.A.) ya bayyana cewa matsayin Ali (A.S.) a gare shi yana kamar matsayin Haruna ga Musa (A.S.), yana mai cewa kamar yadda Haruna ya kasance wazirin Musa, haka Ali yake wazirin Annabi (S.A.W.A.).
Ya kuma kawo Hadisin Thaqalaini, inda Manzon Allah (S.A.W.A.) ya ce ya bar wa al’umma abubuwa biyu masu nauyi: Littafin Allah da zuriyarsa (Ahlul-Baiti).
Ghadeer: Babbar shaida kan wilayar Imam Ali
Ayatullah Subhani ya ce daga cikin manyan hujjoji akwai taron Ghadeer, inda Annabi (S.A.W.A.) ya bayyana cewa: “Duk wanda nake shugabansa, to Ali ne shugabansa.”
Ya bayyana cewa sahabbai 121 ne suka ruwaito wannan hadisi, yayin da kusan mutane 90 daga cikin Tabi’ai suka ruwaito shi. Haka kuma ya ce malamai sama da 360 na Ahlus-Sunna sun kawo wannan hadisi a cikin littattafansu.
Ya bukaci ɗaliban da su rubuta waɗannan hujjoji domin su kasance wani rubutu mai taken “Ka’idar Imamanci”, wanda zai ƙunshi bangarorin “Kubra” da “Sughra”.
Ash’ariyya da batun ɗora wa mutum abin da ba zai iya ba
Daga nan Ayatullah Subhani ya koma kan wani sabon batu da ya shafi ra’ayin Ash’ariyya, inda ya ce wasu daga cikinsu suna ganin cewa ya halatta Allah Ya ɗora wa mutum abin da ba shi da ikon aikatawa.
Ya bayyana cewa dalilin da ya sa ya kawo wannan batu shi ne domin nuna yadda koyarwar Shi’a take da tushe mai ƙarfi na hankali.
Ya yi ishara da ayar Alƙur’ani: «لَا یُکَلِّفُ اللَّهُ نَفْسًا إِلَّا وُسْعَهَا». “Allah ba Ya ɗora wa wata rai abin da ya fi ƙarfinta.”
Ya ce wasu malamai sun yi amfani da wasu ayoyi wajen kafa hujjar cewa ana iya ɗora wa mutum abin da ba zai iya ba yayin da suka yi kunnen uwar shegu da wannan ayar, alhali koyarwar Ahlul-Baiti (A.S.) ta tabbatar da muhimmancin hankali da hujja, wanda shi ya kara girman wannan makaranta.
Batun kafirai da umarnin yin imani
Ayatullah Subhani ya kawo ayar da take cewa:
«قُلْ لِلَّذِینَ کَفَرُوا سَتُغْلَبُونَ وَتُحْشَرُونَ إِلَیٰ جَهَنَّمَ وَبِئْسَ الْمِهَادُ».
“Ka ce wa waɗanda suka kafirce za a rinjaye ku, kuma za a tattara ku zuwa Jahannama.”
Ya bayyana tambayar da wasu suke kawowa: Ta yaya za a umarci waɗannan mutane da su yi imani, alhali Allah Ya riga Ya sanar da cewa za su ƙare a Jahannama?
Ya amsa da cewa an yi kuskuren haɗa matakai biyu ne. Akwai lokacin da mutum yake da damar yin imani, kuma a wannan lokacin ana wajabta masa imani. Amma idan mutum ya kai wani matsayi da ƙiyayya da kafirci suka mamaye zuciyarsa har ya rasa damar komawa zuwa gaskiya, to umarnin yin imani ba ya nan a kansa, duk da cewa hukuncin sakamakon ayyukansa yana nan.
Misalin mutumin da ya shiga gonar da aka kwace
Domin ƙarin bayani, ya kawo misalin fiƙihu na mutumin da ya shiga gonar da ba tasa ba ba tare da izini ba.
Ya ce a farko ana iya umartar mutum da kada ya yi kwace. Amma idan ya riga ya shiga tsakiyar gonar, kuma hanyar fita daga cikinta ita ce ya taka ƙasa har ya fita, ba za a iya cewa kada ya yi wani motsi ba, domin ba zai iya fita ba tare da motsawa ba.
A wannan yanayin, abin da ya rage shi ne ya fita daga gonar, duk da cewa laifin shigarsa cikin gonar tun farko yana nan.
Ya bayyana cewa wannan misali yana nuna cewa wani lokaci hukunci kan wani aiki na iya kasancewa ba zai yiwu a aiwatar da shi ba saboda yanayi, amma sakamakon laifin da mutum ya jawo wa kansa yana nan.
Batun Abu Lahab
Ayatullah Subhani ya kuma yi magana kan Abu Lahab da ayoyin Suratul Masad.
Ya bayyana cewa ana iya raba rayuwar Abu Lahab zuwa matakai biyu. A farkon matakin, bai kai matsayin tsananin ƙiyayya da adawa da Annabi (S.A.W.A.) ba, don haka yana cikin waɗanda ake kira zuwa ga imani.
Amma daga baya, ƙiyayya da adawarsa suka kai wani matsayi mai tsanani, har ya rasa damar karɓar gaskiya. A wannan matakin, ba a maganar umartar sa da imani kamar yadda ake yi wa wanda yake da damar karɓar gaskiya.
Ya jaddada cewa wannan ba yana nufin dukkan kafirai ba su da alhakin sauraron kiran Musulunci ba. A maimakon haka, akwai bambanci tsakanin wanda yake kafiri amma yana da damar karɓar gaskiya, da kuma wanda ƙiyayya da taurin kai suka rufe dukkan hanyoyin shiriya a zuciyarsa.
Manufar aiko Annabawa ita ce tabbatar da hujja
Ayatullah Subhani ya ce duk wanda hujjar Allah ba ta kai gare shi ba, dole ne a isar masa da ita, domin kada ya zo ranar Alƙiyama ya yi hujjar cewa ba a aiko masa da Manzo ba.
Ya kawo ayar da ke bayyana cewa da Allah Ya halaka mutane kafin Ya aiko musu da Manzo, da sun ce:
«وَلَوْ أَنَّا أَهْلَکْنَاهُمْ بِعَذَابٍ مِنْ قَبْلِهِ لَقَالُوا رَبَّنَا لَوْلَا أَرْسَلْتَ إِلَیْنَا رَسُولًا فَنَتَّبِعَ آیَاتِکَ مِنْ قَبْلِ أَنْ نَذِلَّ وَنَخْزَی»
“...Ya Ubangijinmu! Me ya sa ba Ka aiko mana da wani Manzo ba, domin mu bi ayoyinka?...”
Saboda haka, a cewarsa, wajibi ne a isar da saƙon Allah ga mutane gaba ɗaya domin a tabbatar da hujja.
Koyarwar Ahlul-Baiti (A.S.) da muhimmancin hankali
A ƙarshen bayaninsa, Ayatullah Sobhani ya jaddada cewa babban abin da yake son nuna wa ɗaliban shi ne muhimmancin sanin darajar mazhabar Shi’a da kuma matsayinta na hankali.
Ya ce a cikin Usulul-Kafi akwai babi mai suna “Littafin Hankali”, yana mai bayyana cewa Allah Ya ba wa mutane hankali kuma ya kamata a fahimci koyarwar addini ta hanyar hankali da hujja.
Ya yi gargadin cewa gabatar da ra’ayoyin da suka yi hannun riga da hankali na iya haifar da mummunan fahimta game da Musulunci, musamman a wajen waɗanda suke nazarin addinin daga waje.
Ya kuma kawo misalin mutanen Annabi Nuhu (A.S.), inda ya bayyana cewa su ma sun kasance cikin matakai daban-daban: a lokacin da suke da damar yin imani, ana umartar su da imani; amma bayan sun kai matsayin da suka rufe zukatansu ga gaskiya, wannan umarni ya gushe.
A ƙarshe, Ayatullah Sobhani ya bayyana dalilin da ya sa ya kawo wannan batu duk da cewa darasin yana kan Imamanci, inda ya ce manufarsa ita ce nuna cewa idan muka bi tafarkin Ahlul-Baiti (A.S.), irin waɗannan matsalolin tunani da ra’ayoyin da suka yi nisa da hankali ba za su taso ba.
Ra'ayinka