Asabar 18 Yuli 2026 - 23:53
Darasin Akhlaƙ | Shahidin Jagora: Neman Mulki; Farkon Halaka

Hauza/ Wasu mutane suna bin kowace hanya domin su mallaki kujerar shugabanci; alhali kuwa ba su sani ba cewa wani lokaci wannan kujerar ita ce takan zama matattakalar halakar kansu da ta sauran mutane.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa, Shahidin Jagora a cikin wani darasin Darsul-Kharij dinsa, yayin da yake sharhin wani hadisi daga Imam Ja'afar as-Sadiƙ (A.S.), ya bayyana haɗarin neman shugabanci da kuma mummunan sakamakonsa ga mutum da al'umma.

Rubutun Hadisin:

Imam Ja'afar as-Sadiƙ (A.S.) ya ce:

«إِیَّاکُمْ وَهَؤُلَاءِ الرُّؤَسَاءِ الَّذِینَ یَتَرَأَّسُونَ، فَوَاللَّهِ مَا خَفَقَتِ النِّعَالُ خَلْفَ رَجُلٍ إِلَّا هَلَکَ وَأَهْلَکَ.»

"Ku nisanci waɗannan shugabannin da suke neman shugabanci domin kansu. Na rantse da Allah, babu wani mutum da takalma suka riƙa dukan bayansa (wato mutane suka riƙa binsa saboda shugabanci), face ya halaka kuma ya halakar da wasu." (Usulul-Kafi, Juzu'i na 2, shafi na 297).

Sharhin Hadisin:

Ku yi hattara da waɗannan shugabannin da suke neman shugabanci, wato waɗanda suke neman shugabanci domin kansu.

Wani lokaci mutum shugaba ne a dabi'a. Misali, ku ɗauka ayari ne yana tafiya a cikin hamada. Wanda ya fara tashi da sassafe fiye da kowa, ya tashi sauran daga barci, ya shirya abin hawansa, ya taimaka wajen ɗaure kayan sauran mutane, da makamantan haka; wannan mutum shugaba ne a dabi'a.

A wani lokaci, a cikin wani jawabi a gaban Imam Khumaini (R.A.), na bayyana wannan ma'ana. Na ce: Ba wanda ya zaɓi Imam ya zama shugaba; shi shugaba ne a dabi'a. Shi ne ya fara farkawa kafin kowa, ya fara fahimta kafin kowa, ya fara ɗaukar nauyin wannan hanya kafin kowa. Bai gaji ba, kuma duk lokacin da sauran suka gaji, shi ne yake ƙarfafa su.

Amma wani lokaci mutum yana neman shugabanci ne, alhali ma ba shugaba ba ne. Yana ɗaukar kamannin shugabanci ko kuma yana bin shugabanci da gudu. Saboda haka Imam ya ce: "Ku yi hattara." Dole ne mu yi taka-tsantsan.

Ba a taɓa samun wani mutum yana bala'in neman mulki ba, face ya halaka kuma ya halakar da wasu. Wato, shugabanci da kansa yana cikin haɗarin halaka da kuma halakar da wasu.

Wasu mutane suna shiga ruwa da wuta saboda neman shugabanci. Ban fahimci wane irin alheri ne a cikinsa ba. Wace fa'ida ce a cikin wannan shugabancin da mutum zai kai kansa gare shi ta hanyar ɗaukar zunubai masu yawa, yin maganganun ƙarya, aikata ba daidai ba, da kuma tilasta wa wasu su aikata abin da bai dace ba?

Wannan yana nuna rashin fahimtar hakikanin wannan duniya.

Hikima ita ce ganin hakikanin wannan duniya a zahiri, kamar yadda wannan hadisi ya bayyana. Sai dai abin takaici, mu kan yi sakaci da waɗannan hakikanin, kuma mu kan kasance cikin gafala game da su.

Madogara: Sharhin Hadisi daga Shahidin Jagora Ayatullah Khamene'i (R.A.), a gabatarwar Darasin Darsul-Kharij Kharij, 27/07/1388 (19/10/2029).

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha