Jummaʼa 17 Yuli 2026 - 23:49
Ramuwar Jinin Shahidin Jagoran Juyin Juya Hali Shi Ne Ficewar Amurka Daga Yankin Gabas ta Tsakiya

Hauza/ A yayin hudubar sallar Juma’a mai cike da kalaman gargadi da suka kayyade makomar siyasar yankin, Hujjatul Islam Hajj Ali Akbari ya bayyana cewa, matakin ramuwar jinin Shahidin jagoran juyin juya halin Musulunci ba zai tsaya ba, har sai dakarun Amurka sun fice daga yankin gabas ta tsakiya, tare da kawo karshen mulkin sahayoniya.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, da yake jawabi ga dubban al’ummar da suka halarci sallar Juma’a a babban masallacin juma'a na Imam Khumaini (Q) da ke Tehran, Hajj Ali Akbari ya bayyana cewa, al’ummar Iran sun riga sun zama "waliyyan jinin" (magada ko masu ikon ramuwar) jinin jagoran nasu. A cewarsa, wannan ba wani abu ne na motsin rai ba, illa wani mataki na shari’a da kuma dabarun siyasa da aka gina kan ka’idojin da addini ya tanadar.

Ramuwa a matsayin mataki na shari’a da dabarun kasa

Hujjatul Islam Hajj Ali Akbari ya bayyana cewa matakan ramuwar jinin jagoran sun bayyana a fili. A matakin farko, ya jaddada cewa dukkan wadanda suka taka rawa wajen kai harin, ko masu umarni, ko masu aiwatarwa, ko masu bayar da tallafi, za su fuskanci hukunci mai tsanani. “A wajenmu, dukkan jami’an rundunar ta’addancin Amurka da ke yankin nan, suna karkashin hukunci daya,” in ji Hajj Ali Akbari. Ya kuma kara da cewa, a mataki na biyu, Iran za ta ci gaba da kai hare-hare kan sansanonin Amurka a yankin har sai an tabbatar da ficewarsu baki daya.

A bangaren diflomasiyya, limamin Juma'ar ya yi nuni da cewa kofofin tattaunawa da Amurka sun riga sun rufe bayan karya alkawuran da suka yi. Ya ce, dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu yanzu za ta kasance ne kawai a kan matakin karfi. Ya kuma bayyana cewa sarrafa mashigar Hormuz babban ginshiki ne na dabarun Iran, kuma a karkashin kowane hali, ba zai taba komawa yadda yake a baya ba.

Al'ummar Iran; babban jari na zamantakewa

Hujjatul Islam Hajj Ali Akbari ya yabawa al’ummar Iran kan yadda suka nuna jarumtaka a lokacin jana’izar jagoran nasu, wanda ya bayyana a matsayin “Imam mai nasara.” A cewarsa, wannan fitowa ta jama’a ta karya dukkan lissafin maƙiya da suka yi tunanin cewa juyin juya halin yana raguwa.

Ya kara da cewa, Shahidin jagora ya kasance misali na kwarai na bawan Allah mai takawa da kuma jagora mai kishin kasa. “Imam dinmu ya kasance kwamanda mai nasara wanda ya karya bayan zaluncin duniya da kuma tsarin tunani na maƙiya,” in ji shi.

Kira ga sauran kasashen yankin

A karshen hudubar tasa, Hajj Ali Akbari ya yi kira ga sauran gwamnatocin yankin da su yi amfani da wannan dama don kubuta daga dogaro da Amurka. Ya jaddada cewa yanzu ne lokacin da ya kamata kasashen yankin su rungumi hanyar yancin kai da kuma shiga jigon gwagwarmaya, domin kiyaye martabarsu da kuma tabbatar da tsaron kasashensu.

Da yake kammala jawabin nasa, ya jaddada cewa manufar Iran ita ce tabbatar da cewa mulkin sahayoniya ya gushe daga taswirar yankin, kuma wannan wani bangare ne na babban tsarin da al’ummar Iran suka sa a gaba na ramuwar jinin shahidansu.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha