Kamfanin Dillancin Labaran Hauza |
Ingancin Tsari A Gaban Tarin Barazanun Da Ba A Taba Ganin Irinsu Ba
Kun tabo batun ingancin tsari kuma. A mahangata, ana iya ganin ingancin tsarin Wilayatul Faƙih daidai a cikin wannan gaba cewa, ku duba wadanda a cikin wasu abubuwan da suka faru kwanan nan suke tunanin cewa za su iya durkusar da kasarmu a cikin kwanaki biyu ko uku, ba su yi nasara ba sam. Wato an tsara wannan tsarin ne ta yadda a cikin inuwar Wilayatul Faƙih, babu damar gudanar da irin wadannan kullace-kullace cikin sauki kwata-kwata.
Idan kuka dauki kowace kasa a kowane sashi na duniya kuka auna ta, da kowane nau'i na tsarin siyasa da take da shi, shin ta taba fuskantar irin wannan tarin makirci da kullace-kullace a tsawon shekaru arba'in da shida ko arba'in da bakwai? Ni a yanzu na aje dukkan matsalolin tattalin arziki da sauran wahahalun a gefe guda, kuma ina magana ne kawai akan abubuwan da suka faru a cikin shekara guda da ta gabata. Tun daga yakin kwanaki goma sha biyu har zuwa wannan yaki na baya-bayan nan wanda a yanzu muke gab da cika shekara guda da farawarsa, a cikin wannan shekara guda wane irin ƙulli ne aka tsara da kuma aiwatarwa a kanmu wanda ba a yi ba?
Sun kaddamar da manyan yake-yaken guda biyu a kanmu, sun bi diddigin wasu ayyuka na juyin mulki (Coup d'état), har ma sun nufi rayuwar Shugabanmu da kisa. Tabbas ba na musun wahahalun da matsaloli; a yanzu muna fuskantar matsaloli masu yawa, musamman ma a fagen tattalin arziki. Amma a lokaci guda, wannan tsari bai durkushe ba kuma bai girgiza ba sam.
Daga Mafarkin Kwanaki Uku Zuwa Juriyar Shekaru Takwas
Lokacin da Saddam ya aiwatar da yaki kan kasar Iran, a cikin wata hira ya kasance yana cewa: "Ku dakata na tsawon kwanaki kadan, nan da kwanaki uku zan yi tattaunawa da ku a birnin Tehran." Amma wadancan kwanaki uku sun juye sun koma shekaru takwas na yaki, kuma koda taki guda na kasar nan bai rage a hannun makiya ba a karshe.
Wannan tsari ya sami damar sake gina kansa da farfado da dakaru a kowane lokaci da kowane sakan ta yadda koda za a nufi kan tsarin da hari, za ku ga bayan wasu kwanaki kalilan tsarin ya sake komawa daidai kamar yadda yake da can kuma ya ci gaba da tafiyarsa.
Wannan yana nuna ma'anar cewa tsarin yana da inganci kuma mai amfani ne; yana da asali mai karfi, yana da karsashi kuma yana iya tsayuwa akan kafafunsa da kansa, koda kuwa a gaban tarin matsin lamba na barna da barazana da makiya ke amfani da su a kansa.
Yakin Da Har Yanzu Ba A Ba Da Labarinsa Daidai Ba
Ina ma a rika shirya wasu taruka na zama domin mu zauna mu tattauna tare da yin bayani na gaskiya akan ainihin wannan yakin da muka tsallake, akan wannan yakin guda daya kacal, mu yi bayani da bincike na kwarai a kansa.
Kukan da nake da shi na gaskiya kuma a duk inda na tafi nakan tattauna shi da abokaina — har ma na sha fada sau da yawa a gidajen rediyo da gidajen talabijin na kasar — shi ne cewa ku tafi kawai ku rika ba da labarin wannan yaki ga mutane.
A gaskiya mafi yawancin mutanenmu, a'a ma dai a mahangata mafi yawan mutane, har yanzu ba su fahimci daidai da wane bangare muka tsaya muna fuskantar juna ba. Tsayuwa a gaban Amurka ai ba abin wasa ba ne. Watakila yana bukatar tsawon shekaru masu yawa su shude kafin a fahimci fadin wannan lamari da kyau; domin mu zuwa wani mataki muna cikin inuwar kasancewa a daidai lokacin abin, kuma domin muna tsakiyar abin da ya faru, har yanzu ba mu fahimci zurfin abin da ya faru da gaske ba.
Isra'ila Tana Gab Da Rushewa baki daya
A mahangata, idan har aka ba da labarin wannan yaki daidai, a lokacin ne wannan hoto zai kafu a cikin tunanin daukacin mutane cewa aikin wadannan mutane ya zo karshe. Wannan surutu da Isra'ila ke yi a yau, a gaskiya tana fitar da sauti na karshe ne na rayuwarta. Ku a yau ba ku fuskanci Isra'ila ta shekarar 1967 ba; Isra'ilar yau ita ce Isra'ilar shekarar 2025 da 2026 Miladi. Wata daula ce wadda hatta a gaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ba ta da ikon nuna juriya ta dindindin.
Su da kansu sun fada cewa domin a ruguza kasar Isra'ila, kungiyar Hizbullah ta Lebanon ita kadai ta wadatar; balle kuma idan aka hada da Ansarullah ta kasar Yemen, Al-Hashdush Sha'abi ta kasar Iraki da sauran kungiyoyin gwagwarmaya na sahun gaba. A cikin irin wannan fage, asali watakila lokaci ba zai ma kai ga kasar Iran ta shiga ba sam.
Dole ne mutane su fahimci cewa ku a nan kuna fuskantar makiya ne kuma kuna cikin jihadi da fuskantar juna da shi. Wannan lamari yana bukatar bayani da ba da labari na kwarai. Idan har mu ba mu ba da labarin ba, tashoshin BBC, CNN da Reuters za su zo su bayar da nasu labarin; wani labari da za a tsara shi ta yadda za mu rika tunanin cewa lallai mun kasance masu rauni sosai, alhalin kuma ba haka ba ne sam.
Tabbas ina sake jaddada cewa mu tare da wuraren karfi, muna da wasu raunuka kuma har yanzu muna da su kuma dole ne mu gyara su; ko a fagen soja — wanda a dabi'ance ya fita daga kwarewarmu — ko kuma a sauran fage, kamar fagen gudanarwa da shugabanci, al'amuran al'adu, tattalin arziki da kuma manufofin ketare.
Juriya; Sirrin Nasara A Makarantar Imam Khumaini (Q)
Duk da haka, hakikanin gaskiya ita ce mu mun gwada karfi da karfin gangan na duniya kuma mun karya musu gwiwa mun kwantar da hannunsu. Shin an bayyana wannan gaskiya ga mutane daidai? Shin wannan hoto a yau ya kafu baki daya a cikin tunanin al'ummarmu? Musamman ma idan aka cire mutane, wani lokaci muna jin wasu kalamai daga bakin wasu shugabanni wadanda ke nuna cewa har yanzu shi kansa shugaban bai fahimci ainihin yadda lamarin yake ba daidai.
Imam Khumaini (R) ya koya mana wannan gaskiya cewa a gaban wadannan mutane dole ne a tsaya, kuma idan kuka tsaya, da iznin Ubangiji za ku durkusar da su baki daya. Wannan alkawari ne na Allah. Idan kuka nuna juriya, taimakon Ubangiji zai kasance tare da ku kuma Allah zai taimake ku.
Wadannan su ne jerin abubuwan da za a iya bayyanawa game da makarantar tunani ta Imam Khumaini (Q) da kuma tsarin da za a iya koya daga gare shi. Insha Allahu muna fatan mu samu damar gudanar da wadannan koyarwa a cikin fagen shugabancinmu na yau da kullum.
Ra'ayinka