Jummaʼa 10 Yuli 2026 - 14:31
Tekun Jama'a a Jana'izar Jagoran Shahidi; Tsohon Mai Gabatar da Shirin CNN: Wannan Na Daya Daga Cikin Manyan Jana'izozi a Tarihi

Hauza/ Tsohon ɗan jarida kuma mai gabatar da shirye-shirye na tashoshin CNN da MSNBC, Rick Sanchez, ya bayyana cewa jana'izar Shahidin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci tana daga cikin manyan jana'izozi mafi girma a tarihin duniya, yana mai cewa al'ummar Iran sun nuna cikakken haɗin kai da ƙudurinsu.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa, a daidai lokacin da ake gudanar da gagarumar jana'izar Shahidin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, kalaman da tsohon fitaccen ɗan jaridar Amurka Rick Sanchez ya yi sun jawo hankalin kafafen yaɗa labarai da dama.

Rick Sanchez, tsohon ɗan jarida kuma mai gabatar da shirye-shirye na CNN da MSNBC, yayin da yake tsokaci kan hotunan taron jana'izar ya ce: "Wannan teku ce ta mutane. Wannan na ɗaya daga cikin manyan jana'izozi mafi girma a tarihi. Al'ummar Iran suna nuna ƙudurinsu da haɗin kansu. Ku yi tunani, waɗannan su ne mutanen da Netanyahu ya yi ƙoƙarin shawo kan Trump cewa gwamnatinsu tana gab da rushewa."

Ya ƙara da cewa: "Idan muka kalli waɗannan hotuna, taron ya yi girma matuƙa da har kafafen yaɗa labarai na Yamma ma ya zama dole su amince da hakan."

Wannan furuci na zuwa ne yayin da aka gudanar da jana'izar Shahidin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci tare da halartar miliyoyin al'ummar Iran daga sassa daban-daban na ƙasar, tare da baƙi da wakilai daga ƙasashe daban-daban, lamarin da ya samu gagarumar ɗaukar hankali a kafafen yaɗa labaran duniya.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha