Lahadi 28 Yuni 2026 - 16:16
 Dole Ne A Hukunta Waɗanda Suka Aikata Laifin Yaki Na Minab Da Lamerd A Kotunan Cikin Gida Da Na Kasa Da Kasa

Hauza / Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, a cikin wani sako da ya aike na taya murnar makon ma'aikatar shari'a, ya jaddada cewa: "Daga jinin shahidai wadanda aka zalunta a yakin danniya na biyu da na uku, har zuwa ga raunuka da asarar jiki, ta hankali, ta dukiya, da ta ruhi da aka yi wa kasarmu mai daraja da kowane mutum daya daga cikin al'ummar Iran da aka zalunta a ciki da ma wajen kasar; daga kisan yara da laifukan yaki da ba a taba ganin irinsu ba a Minab da Lamerd har zuwa harin da aka kai wa cibiyoyin lafiya da na hidima; daga kisan jarirai 'yan kwanaki kalilan a duniya har zuwa ga manyan tsofaffi masu daraja; kuma a saman dukkan wadannan, shahadar fitaccen shugaba, jauhari mara tamka kuma wanda ba shi da tsara a wannan zamani, jagoran mayaka mai girma (Allah Ya daukaka matsayinsa mai tsarki), kowannensu ya kafa fayil guda daya daga cikin daruruwan, face ma dubun-dubatar fayilolin shari'a masu muhimmanci wadanda dole ne a bi daddale su da dukkan gaske a kotunan shari'a na cikin gida da na kasa da kasa."

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza daga Tehran, an wallafa cikakken sakon Ayatullah Sayyid Mujtaba Hussaini Khamenei, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, da ya aike na taya murnar makon ma'aikatar shari'a da kuma zagayowar ranar shahadar Ayatullah Beheshti da waɗanda suke tare da shi.

Fassarar cikakken sakon nasa shi ne kamar haka:

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai

Ina mika ta'aziyyar kwanakin masifar iyalan gidan Manzo (A.S) da shahadar Sayyidush-Shuhada (A.S) da sahabbansa masu mubayi'a ga daukacin al'ummar Iran da al'ummar Musulmi baki daya. Yunkuri da juyin juya halin Husaini domin tsayar da gaskiya, gyaran al'umma, da fuskantar zalunci, shi ne kololuwar tarihi a fafatawa tsakanin gaskiya da karya, da kuma adalci da zalunci; sannan yana dauke da darussa masu kima da wadanda ba za a taba mancewa da su ba ga dukkan 'yan adam masu 'yanci a duniya.

Ana kiran jinin Sayyidush-Shuhada (A.S) da 'Jinin Allah' (Tharallah) wanda yake gudana a cikin jijiyoyin duniya kuma yake samar da rurrumar ayyukan jaruntaka masu ba da rai. Yunkuri da Juyin Juya Halin Musulunci na Iran, tunda yake reshe ne da aka samo shi daga wannan madogara mai haske, dole ne koyaushe ya kasance yana fafutukar cimma manufofin juyin juya halin Husaini. Bakwai ga watan Tir na kowace shekara yana tunatar da mu game da fitaccen mutum na juyin juya hali, kuma wanda, ta hanyar kasancewarsa a shugabancin ma'aikatar shari'a, ya yi kokari ba dare ba rana a wannan tafarki, har zuwa lokacin da shi da gungun sahabbai masu aminci na juyin juya hali suka sha zumar shahada, kuma zaluntar da aka yi masa da adadin shahidai saba'in da biyu da ke tare da shi sun kasance shaida kan tsarin Husaini na wannan gwamnati da masu gina ta.

Nasarar Ma'aikatar Shari'a Za Ta Karfafa Amincewar Jama'a Ga Gwamnati

Matasayin ma'aikatar shari'a a tsarin Jamhuriyar Musulunci ta Iran shi ne tsare hakkin jama'a da farfado da hakkokin bai-daya da 'yanci na halal, yaki da barna, aiwatar da adalci, tsayar da haddin Allah, da kuma sanya ido kan aiwatar da doka. Sakamakon samun nasara a wannan tafarki, bayan samun yardar Allah, zai kasance karfafa amincewar jama'a ga wannan jigo na gwamnati. Tsammani na gaskiya daga dukkan bangarorin gwamnati, hukumomi, da cibiyoyi masu alhakin hakan shi ne cewa koyaushe su rinka daidaitawa da sake fasalin ayyukansu daidai da ma'auni da ake bukata na tsari mai tsarki na Jamhuriyar Musulunci da kuma babban matsayi na al'umma. A wannan fanni, ma'aikatar shari'a tana da wuri na musamman face ma wanda ba shi da tamka domin gyara tafiyar abubuwa da kuma motsa sauran sassan gwamnati, wanda hakan yana bukatar ci gaba da tsarin gyara da sake gini a cikin gidan wannan ma'aikatar kanta. A yanzu haka, tsammanin jama'a na gari shi ne su shaida jaddadawa ta aiki a kan wannan lamari a cikin ayyukan ma'aikatar shari'a.

Ta yadda sauyin tsarin shari'a zai fita daga kalmomin da aka rubuta a cikin takardar canji da tsare-tsare da taswirorin hanya, ya koma ga aikatawa na hakika, kuma alamunsa su bayyana a dukkan fage da abin ya shafa; tun daga dakunan gine-ginen shari'a da zaman kotu har zuwa wuraren taruwar jama'a da sararin zamantakewa; ta yadda mutane za su ga sakamako mai kyau na hakan a rayuwarsu ta yau da kullum ta hanyar nuna tsayin daka wajen fuskantar kowane irin barna, rage danne hakki, saurin gudanar da shari'a, daukaka lafiyar aiki da ingancin hukunce-hukunce na alkalai, da kuma samun damar shiga cikin sauki ga ma'aunan adalci.

Bibiyar Cikakken Haƙƙin Al'ummar Iran a Laifukan Kasa da Kasa Na Shekarar 2025 da 2026 Shi Ne Mafi Muhimmancin Al'amuran Shari'a na Kasa

A cikin wannan hoton na ma'aikatar shari'a, dole ne aiwatar da adalci ya kai matakin da duk wanda aka zalunta zai dauke shi a matsayin mafakar sa, sannan musamman wadanda ke da wani irin iko ko dama kada su kuskura su keta hakkin wasu, kuma kofar alfarma da tsoma baki ta rufu baki daya, kuma samun sanayya ko aboki a sassan ma'aikatar kada ya zama wata fa'ida ko tagomashi. Hakika, kwato hakkokin al'umma bai takaituwa ga lamuran daidaikun mutane kadai ba, a'a, nau'o'in hakkokin jama'a da na zamantakewarsu, tun daga hakkin tsaron tattalin arziki da samun dama ta adalci ga guraben ayyuka da ci gaba, har zuwa hakkin cin gajiyar abubuwan da dabi'a ta tanada ta hanyar adalci, kyakkyawan muhalli, 'yanci na shari'a, da shugabanci nagari, duka suna daga cikin muhimman al'amura domin yada adalci. Daga cikin haka, daya daga cikin mafi muhimmancin al'amuran shari'a da suka shafi daukacin al'ummar Iran a wannan gaba na lokaci, shi ne bibiyar, daddale da kwato hakkokinsu da aka danne sakamakon laifukan miyagun mutane na kasa da kasa da masu girman kai da masu mamayar duniya musamman a shekarun 2026.

Dole Ne A Kama Wuya Kuma A Hukunta Wadanda Suka Aikata Laifin Yaki na Minab da Lamerd a Kotunan Shari'a na Cikin Gida da na Kasa da Kasa

Daga jinin shahidai wadanda aka zalunta a yakin danniya na biyu da na uku, har zuwa ga raunuka da asarar jiki, ta hankali, ta dukiya, da ta ruhi da aka yi wa kasarmu mai daraja da kowane mutum daya daga cikin al'ummar Iran da aka zalunta a ciki da ma wajen kasar; daga kisan yara da laifukan yaki da ba a taba ganin irinsu ba a Minab da Lamerd har zuwa harin da aka kai wa cibiyoyin lafiya da na hidima; daga kisan jarirai 'yan kwanaki kalilan a duniya har zuwa ga manyan tsofaffi masu daraja; kuma a saman dukkan wadannan, shahadar fitaccen shugaba, jauhari mara tamka kuma wanda ba shi da tsara a wannan zamani, jagoran mayaka mai girma (Allah Ya daukaka matsayinsa mai tsarki), kowannensu ya kafa fayil guda daya daga cikin daruruwan, face ma dubun-dubatar fayilolin shari'a masu muhimmanci wadanda dole ne a bi daddale su da dukkan gaskiya a kotunan shari'a na cikin gida da na kasa da kasa.

Abin da yake tabbatacce shi ne, dole ne a kama wuyan masu laifin sannan a kai su ga sakamakon ayyukansu na laifi. Muhimmin abu a wannan ma'ana shi ne; Na farko, ikirari da ma alfahari na rashin kunya da wasu daga cikin shugabannin makiya na Amurka da Sahayoniya suka yi a kan wadannan laifuka, wanda hakan tabbas ana daukarsa a matsayin ikirari na laifi kuma ya samar da rukunonin kwato hakkokin da aka danne na al'umma ta hanyar da ta dace. Na biyu, sharadin mayar da hankali da kulawa ga aiwatar da umarnin Jagoran Shahidai na Juyin Juya Hali a ganawarsa ta karshe da jami'an shari'a a watan Tir na shekarar da ta gabata game da binciken laifukan da aka tafka a yakin danniya na biyu, shi ne mika shi zuwa ga yakin danniya na uku da kuma ci gaba da bin diddiginsa har zuwa lokacin samun hukunci da mika aiwatar da shi ga kwararrun mutane na gari. Wannan mataki a nasa bangaren zai hana sake aukuwar irin wadannan laifuka.

Kula da Shawarwarin Jagoran Shahidai na Juyin Juya Hali Shi Ne Mabudin Nasarar Ma'aikatar Shari'a

Hakika, domin samun nasara a tafarkin sauyi na ko'ina da kuma kara sauri wajen cimma manufofin da aka ambata, ana bukatar shirye-shirye da sharuda daban-daban wadanda galibi an sha bayyana su a tarukan shekara-shekara na jami'an shari'a da shawarwari da jaddadawa filla-filla na Jagoran mai girma na shahidai (Allah Ya tsarkake ransa mai daraja) sau da yawa, kuma kula da su da gaske da kuma yin kokari domin ganin sun tabbata wanda hakan shi ne mabudin nasarar jami'ai masu daraja na ma'aikatar shari'a, abu ne da nake jaddadawa kuma nake bukata da gaske.

Tafarkin kaiwa ga adalci da yaki da zalunci da barna tafarki ne mai wahala wanda da ikhlasi da dogaro ga Allah, kiyaye takawa a matsayi madaukaki, kwarin gwiwa da nufi na gaske, kokari da himma ninki biyu, jajircewa da tsayin daka, kirkire-kirkire a aiki da kuma amfani da ya dace da fasahohin zamani da sanya fasaha a cikin ayyuka, zai zama mai sauki. Tabbatar dukkan wadannan, da izinin Allah da kuma karkashin inuwar kulawa ta Shugabanmu mai Adalci da ake jira (Al-Mahdi) (Allah Ya gaggauta bayyanarsa mai daraja) zai yiwu in sha Allah.

Sayyid Mujtaba Hussaini Khamenei

7 ga Tir 1405 (28 ga Yuni 2026)

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha