Asabar 27 Yuni 2026 - 18:42
Addu’o’in Imam Sajjad (AS); Makami Mai Tasiri A Jihadut-Tabyeen 

Hauza/ Addu’a da munajati sun kasance makami mai tasiri na Imam Zainul Abidin (AS) a fagen Jihadut-Tabyeen da kuma jagorantar al’umma zuwa ga gaskiya da haske.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa jagoranmu shahidi Ayatullah al-Uzma Imam Sayyid Ali Khamenei a wani jawabinsa game da muhimmancin jihadin al’adu da siyasa na Imam Zainul Abidin (AS) ya bayyana cewa: “Imam Sajjad (AS) ya rike matsayin Imama na kusan shekaru 35, kuma a cikin wadannan shekaru 35 daga farko har ƙarshe yana cikin gwagwarmaya ne. A cikin wadannan shekaru 35, Imam Sajjad (AS) ya bi manyan layuka uku. Duk wanda yake son yin nazari a wannan fage, to ya bi wadannan ginshiƙai uku.”

Sannan ya ambaci muhimman ginshiƙan guda uku kamar haka:

1. Bayyana batun Imama a zamanin tsananin danniyar Umawiyya,  

2. Ƙarfafa tunani da aƙidar al’umma ta hanyar addu’a,  

3. Aikin gwagwarmaya da tsari da kuma haɗa kan mabiya Shi’a.

Ya kuma yi bayani dalla‑dalla kan kowane ɗaya daga cikinsu a matsayin muhimman ginshiƙai na tafiyar Imam Sajjad (AS) a ɗaya daga cikin mafi tsananin lokutan tarihi a Musulunci.

Sauyin salon gwagwarmaya da zaluncin dagutu

Bayan aukuwar Karbala, fili da yanayin gwagwarmaya da zalunci ya sauya sosai. Bisa yanayin zamani, takobi ba shi ne mai yanke hukunci ba; abin da ya zama mai tasiri shi ne riwaya da kuma bayani. Domin abokin gaba ba wai kawai ya tsaya gaban sansanin yaƙi ba ne, har ma ya tsaya gaban tarihin al’umma. Saboda haka, gwagwarmayar al’adu, ɗabi’a da siyasa ta Imam Sajjad (AS) a kan Yazidawa da dagutun wancan lokaci ta samu ma’ana ta musamman.

Hanyoyi daban‑daban na Imam Zainul Abidin (AS) wajen shiryar da zukata

Hujjatul Islam wal Muslimin Husain Bonyadi, malamin manyan darussa a Hauzar Ilimi ta Qum, ya bayyana cewa addu’a da munajati su ne makamin Imam Zainul Abidin (AS) a jihadut-tabyin da shiryar da al’umma zuwa ga gaskiya da haske.

Ya ce Imam Sajjad (AS) ya shahara a tarihin Shi’a da Musulunci ta hanyar addu’o’insa da Sahifa Sajjadiyya, domin ta wannan hanya yake hulɗa da mutane yana tarbiyantar da zukatansu da rayukansu.

Ya ƙara da cewa Imam (AS) ya yi amfani da hanyoyi daban‑daban wajen tarbiyyar mutane: wani lokaci ta hanyar wa’azi a fili, wani lokaci kuma a ɓoye. Misali, an ruwaito cewa ya kan sayi bawa, ya riƙe shi har zuwa watan Ramadan, sannan ya ‘yantar da shi saboda Allah, domin ya zama mai yaɗa addini a cikin al’umma. Haka kuma, a wasu lokuta ya kan karanta addu’o’i da murya mai sauti domin samar da yanayin tarbiyya, wanda hakan ke kawo tsarkin zuciya, kusanci da haske a zukata.

Ya jaddada cewa wanda yake da kyakkyawar alaƙa da Allah, yana da kyakkyawar alaƙa da mutane. Daga cikin siffofin addu’a kuwa shi ne kawo natsuwar rai, haskaka zuciya, da kawar da zunubi da kuskure. Haka kuma wasu daga cikin addu’o’in Imam suna magana kan kammala Alƙur’ani, waɗanda suke da matuƙar daraja domin suna haɗa ruhin mutum da Allah da buɗe masa ƙofofin ci gaba da kamala.

Yaɗa tsantsar ma’arifar addini ta hanyar addu’a

Malamin ya ci gaba da cewa Imam (AS) ta hanyar addu’a da munajati a lokacin tsananin danniya, ya yaɗa ma’arifofin addini, ya kuma sanar da mutane game da tauhidi, Annabci, Imama da kuma yaƙi da zalunci. Ta wannan hanya ne ya ci gaba da raya al’adun Ashura da tafarkin Husaini, har al’umma suka fara fahimtar zurfin zaluncin da gwamnatin Banu Umayya ke aikatawa.

Jihadin al’adu da aƙida na Imam Sajjad (AS)

Hujjatul Islam Habib Baba'i, mai bincike kuma marubuci a fagen ilimin Hauza, ya bayyana cewa neman gaskiya da umarni da kyakkyawa da hani da mummuna a zamanin Imam Sajjad (AS) ya kasance cikin tsanani da wahala. Don haka Imam (AS) ya ɗauki hanyar jihadin aƙida da al’adu a matsayin mafi inganci wajen tunkarar maƙiyi, duk da cewa maƙiyin yana da rinjaye a zahiri.

Ya ce cigaban jihadin al’adu, ilimi da aƙida da Imam (AS) ya gudanar ya yi tasiri mai girma a cikin al’umma. Ya kuma yi amfani da addu’a a matsayin makami mai ƙarfi wajen fuskantar girman kai da mamayar al’adu ta Banu Umayya, wanda hakan ya ƙarfafa bangaren imani da ruhin al’umma.

Ya ƙara da cewa addu’o’in da Imam (AS) ya fitar a lokutan sauƙi da wahala sun zama wata babbar taska ta ƙarfafa gwiwa da fatan alheri, kuma a lokaci guda suna jefa tsoro a zukatan maƙiya.

Har ila yau, ya jaddada cewa ƙiyam na ma’arifa da irfanin Imam Sajjad (AS) bayan Karbala ya zama ginshiƙi mai daraja wanda amfaninsa ya bayyana a zamanin Imam Baƙir (AS) da Imam Sadiƙ (AS), wanda nazarin hakan na buƙatar dogon bayani.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha