Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito, tare da zuwan watan Muharram, mun yi wata tattaunawa da Hujjatul Islam wal Muslimin Wahid Pour, wanda kwararre ne a fannin hukunce-hukuncen addini, domin tattauna ka'idoji da ladubban zaman makokin Sayyidush-Shuhada (AS) a wannan wata mai albarka. Ga fassarar cikakken bayanin tattaunawar:
Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alal Hussain wa ala Aliyi bnil Hussain wa ala awladil Hussain wa as-habil Hussain.
Ina mika gaisuwa da girmamawa, tare da ta'aziyya kan wadannan kwanakin makoki da kuma bakin ciki.
To, bisa ga al'ada, bayan mun wuce matakin gabatarwa, yanzu za mu shiga babban batunmu, wato mene ne ya kamata a yi, kuma mene ne bai kamata a yi ba a lokacin zaman makoki?
Dole ne mu lura da kowane aiki da ake yi a lokacin makoki, mu kuma kididdige su; kamar dukan kirji, dukan sarƙa, mawaƙa (madhah), karanta musiba, wanne irin waƙoƙi ya kamata a karanta, wanne bai kamata a karanta ba? Shin ana iya amfani da kayan kida a lokacin makoki ko a'a?
Ko kuma 'Tamsiliyya' (wasan kwaikwayo na nuna abin da ya faru) wanda yake al'ada a wurare da dama, kuma a yanzu yake daya daga cikin muhimman fasahohin al'ummar Iran; duk wadannan abubuwa ne da ake tattauna hukuncin su a zaman makoki.
Akwai abubuwa da dama da za su iya shigowa cikin wannan tattaunawa; kamar batun waƙoƙi, yadda ake rera su, ingancin baitocin waƙoƙin, da sauransu. Abin da nake so in bayyana shi ne, ba za mu iya cewa "makoki yana da kyau" a matsayin wani abu na gama-gari kawai ba.
Eh, hakika makoki yana da kyau, amma dole ne a binciki cikakkun bayanai na yadda ake gudanar da makokin domin gani ko yana da kyau ko a'a. A lokacin da muke son gudanar da makoki, makokin yana da bangare na ciki (zuciya) da kuma bangare na waje (ayyuka).
Bangaren ciki shi ne bakin ciki. Daga lokacin da watan Muharram ya fara, Imami na takwas (AS) ya ce: "Babu wanda yake ganin murmushi a fuskar mahaifina Musa al-Kazim (AS) har zuwa ranar Ashura; ranar Ashura kuma ta kasance ranar musiba ga mahaifina." To, wannan bakin ciki ne na cikin zuciya. Shi musulmi (shi'a) ya kamata ya kasance mai bakin ciki a cikin zuciyarsa da wannan babbar musiba.
Amma mene ne bangaren waje?
Bangaren waje shi ne kuka, nuna damuwa da kuka mai karfi, dukan kirji, dukan sarƙa, da kuma shiga cikin jerin gwanon makoki.
Shin ya kamata makokinmu ya kunshi jarumtaka? E, ya kamata ya kunshi jarumtaka. Makokinmu ya kamata ya zama alamar abin da ya faru a Karbala. Abin da ya faru a Karbala yana dauke da tausayi, yana dauke da jarumtaka, yana kuma dauke da musiba.
Abin da ya faru a Karbala yana dauke da falala; ya kamata a ce akwai falala a cikin makokinmu. Makokin mai falala shi ne wanda babu wulakanci a cikinsa, da makamantan hakan.
Don haka, muna bukatar mu lura da kowane aiki da ake yi a makoki, mu kuma koma ga hukunce-hukuncen Shari'a da Maraji'ai (Malamai) suka bayar, domin mu ga menene hukuncin kowane aiki. Wanne ne halas, wanne ne haram? Wanne ne abin ki, wanne ne abin so?
Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh.
Ra'ayinka