Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamenei, jagoran juyin juya halin Musulunci, ya fitar da wannan saƙo ne a lokacin tunawa da cika shekaranbiyu da shahadar Ayatullah Ra'isi da kuma girmama shahidan hidima.
Ga cikakken saƙon:
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin ƙai.
Tuna shahidan hadarin jirgin watan Ordibehesht, musamman shugaban ƙasa shahid Hujjatul Islam wal Muslimin Ra'isi, yana tunatar da mu shahadar dimbin shahidan hidima a Jamhuriyar Musulunci ta Iran; daga Mutahhari, Beheshti, Raja'i da Bahonar, har zuwa Ra'isi, Al‑Hashem, Amir‑Abdollahian da Larijani—daruruwan manyan mutane da aka tarbiyyantar a makarantar Imam Khumaini da Khamenei, Allah Ya ɗaukaka matsayinsu. Su ne wadanda suka kawata tarihin hidima ta gaskiya da jajircewar jami’an Jamhuriyar Musulunci da sa hannun jininsu.
Daga cikin fitattun siffofin Shahid Ra'isi akwai: karɓar mas'uliyya, bai wa matasa dama, kula da adalci, diflomasiyya mai aiki da amfani, da kuma musamman kasancewa kusa da jama’a.
Waɗannan siffofi sun kasance suna ƙarfafa abokan Iran, ciki har da mayakan kungiyoyin muƙawama masu ƙarfi da kuma masu kishin tsarin ƙasa. Duk wannan ya kasance ne tare da ruhaniya mai zurfi da ke cikin zuciyarsa.
A cikin dangantakar da ke tsakanin gwamnati da jama’a, irin waɗannan kyawawan halaye suna haifar da girmamawa da godiya daga ɓangarorin biyu. Saboda haka ne aka yi masa rakiyar jana’iza zuwa makwancin ubangidansa, Imam Ali ibn Musa al‑Ridha (AS), cikin wani gagarumin yanayi na musamman. Lokacin shugabancinsa da bai cika ba ya zama ma’auni na ƙoƙari da kulawa ga al’umma da ƙasa tare da kiyaye ‘yancinta.
Yanzu muna fuskantar wani yanayi na jarumtaka da al’ummar Iran ke nunawa a cikin tsayin daka na tarihi a gaban rundunonin ta’addanci biyu na duniya. Wannan yana ƙara nauyin alhaki a kan jami’an Jamhuriyar Musulunci—daga Jagora da shugabannin ɓangarori uku na gwamnati zuwa dukkan matakan gudanarwa.
A yau, godiya ga ni’imar haɗin kai tsakanin al’umma da gwamnati da dukkanin hukumomin Jamhuriyar Musulunci, ya zama wajibi a ƙarfafa ƙwazo da hidima mai yawa da jajircewa daga jami’ai, warware matsaloli da damuwar jama’a musamman a fannin tattalin arziki da rayuwa, kasancewa a cikin jama’a kai tsaye, da kuma ba wa jama’a damar rawar gani a cikin ci gaban ƙasa tare da tafiya da fata zuwa makoma mai haske.
Rahamar Allah da yardarsa su tabbata ga shahidan hanyar hidima, kuma taimakon Allah da addu’ar ubangidanmu (Allah Ya gaggauta bayyanarsa) su kasance goyon baya ga masu hidima ga al’ummar Musulmin Iran.
Sayyid Mujtaba Hussaini Khamenei
30 Ordibehesht 1405 (20 ga Mayu 2026)
Ra'ayinka