Talata 28 Afirilu 2026 - 00:34
Sake Nazarin Jawaban Shahidin Jagoran Juyin Juya Hali game da Matsayin ’Ya’ya Mata a Al’umma ta Musulunci

Hauza/ Shahidin Jagoran Juyin Juya Hali a cikin wannan bayani ya jaddada muhimmancin shigar matan Musulmi, musamman ’yan mata, a fannoni na ilimi, zamantakewa, da al’adu, tare da kiyaye kunya da hijabi, ƙarfafa asalin musulmancinsu (ƙimarsu ta addini), gyaran kai (tarbiyya da haɓakar ruhaniya), da kuma nuna alhakin da suke da shi wajen lamurran al’umma.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa sashen Mata, Iyali da Salon Rayuwa na shafin KHAMENEI.IR (Rayhana), a cikin zaben “’Yar Ginin Al’ada”, ya sake duba kalaman Shahidin Jagoran Juyin Juya Hali game da rawar ’ya’ya mata a al’ummar Musulunci ta Iran.

1. Damammakin aiki a buɗe suke ga ’ya’ya mata muddin sun kiyaye kunya da nisantar cuɗanya da maza

A fannoni na zamantakewa, siyasa, ilimi da sauran nau’o’in ayyukan jama’a… mace Musulma kamar namiji tana da hakkin yin abin da take ganin wajibi ne, abin da ake buƙata a zamaninta, ko abin da take ji ya rataya a wuyanta. Idan mace matashiya tana son ta zama likita, ko ta yi aikin tattalin arziƙi, ko ta shiga fannin kimiyya, ko ta koyar a jami’a, ko ta shiga siyasa, ko ta zama ’yar jarida — kofofi a buɗe suke. Sai dai a kiyaye kunya, hijabi da nisantar gauraya da maza. A cikin al’umma ta Musulunci, damammakin aiki ga maza da mata duka a buɗe suke. Shaida a kan haka ita ce koyarwar Musulunci da nauyin da addini ya dora kan maza da mata duka. Hadisin “Duk wanda ya tashi bai yi damu da damuwar Musulmai ba, ba Musulmi ba ne” ba na maza kaɗai ba ne — mata ma wajibi ne su damu da damuwoyin Musulmai, al’umma, da duniyar Musulunci.

(Jawabin a wajen taron matan Khuzestan – 1375/12/20 (10/03/1997))

2. Ku ɗauki Zainabul Kubra a matsayin abin koyi don gina shaksiyyarku

Muna fata matasa mata su kalli Zainabul Kubra a matsayin abin koyi, su gina asalinsu da halayyarsu daga gare ta; sauran abubuwa duk ƙananan lamurra ne. Idan asalin zuciyar mutum ta tsarkaka ta ɗaukaka, komai ya kan yi masa ƙanƙanta, kuma hakan yana ba shi ƙarfin gwiwar aiwatar da dukkan ayyuka.

(Jawabi a taron jama’a mabambanta – 1384/03/25 (15/06/2005))

3. Ku ja hankalin duniya ta hanyar farfaɗo da darajar mace Musulma

Mace Musulma yar Iran ya kamata ta yi ƙoƙari ta farfaɗo da girma da darajar mace Musulma ta yadda duniya za ta kalle ta da girmamawa. Wannan aikin a yau wajibi ne akan mata Musulmi — musamman matasa mata ’yan makaranta da jami’a.

(Jawabi a taron mata – 1379/06/30 (20/09/2000))

4. Ku bayyana rawar mace a mahangar Musulunci ku mai da ita fili

Ku mata masu baiwa, ‘yan mata masu hazaka, matasa masu hikima — ɗaya daga manyan nauyukan da ke wuyanku a yau shi ne bayyana matsayin mace a Musulunci, ku haskaka shi ku bayyana shi. Tarbiyar mace mai tsafta, mafi girman hidima ce ga al’ummar Musulmai da dan Adam gaba ɗaya. Wannan tafarki ya riga ya fara, amma ya kamata ya ƙara ƙarfi kuma ya yadu. Kuma tabbas za ku yi nasara a wannan tafarki.

(Jawabi a taron kasa da kasa na “Mata da Farkawar Musulunci” – 1391/04/21 (11/07/2012))

5. Karatu, gyaran hali, wayewar siyasa da ƙoƙarin juyin juya hali — wajiban ku ne

’Yata! Shigarki cikin duniyar taklif na Allah albarka ce gare ki. Yanzu kina magana ne da Ubangiji Mai girma da jinƙai — wannan babbar daraja ce. Ki koyi umarnin Allah ki yi aiki da su, hakan zai sa ki zama mai daraja kuma mai amfani ga wasu. Annabi da Imamai shine jagorori mafi kyawu — ku koyi sanin su ku bi su. Karatu, gyaran halayya, wayewar siyasa tare da ƙoƙarin juyin juya hali, wajibi ne kan matasan wannan zamanin — mata da maza. Ina taya ki murna da ranar balagarki, kuma ina yi miki addu’a.

(Amsar Jagora ga wata yarinya kan balaga – 1398/09/24 (15/12/2019))

6. Ku yaɗa ruhin Musulunci a cikin jami’o'i

Muhallin jami’o’i yana da matuƙar muhimmanci. Mata dalibai da malamai su yi ƙoƙari su yada ruhin Musulunci. Kada ku bar wani — idan har akwai — ya yi wulakanci ga hijabi ko ga matan Musulmai a jami’a. Kada ku bari su yada tunanin fasadi. Jami’a wajibi ne ta zama muhalli na tarbiyyar mutum irin wanda Musulunci ke so — Sayyida Fatimatuz Zahra ita ce abin koyi. Wannan abu ne mai matuƙar muhimmanci ga makomar ƙasa.

(Jawabi a taron wasu mata – 1371/09/25 (16/12/1992))

7. Karatu, Bincike, da Tsunduma cikin Matsalolin Zamani Wajibi ne ga Mata

Shawara ta ga 'yan uwana mata da 'yammata ita ce: ku ƙara ilimi da wayewarku. Karatu, lura daki-daki, bincike, koyon darussa, shiga cikin matsalolin zamani, da himma ga ayyukan addini, dukkansu wajibi ne kuma ina tabbatarwa cewa a wannan zamani, mata kamar maza, wajibi ne su sani tare da aikatawa.

(Jawabin Jagora a taron matan Armiya – 1375/06/28 (18/09/1996))

8. Jami'a Muhalli Ne Mai Kyau domin Bunƙasa Ilimi ga Mata

Samun damar shiga jami’a – musamman a zamaninmu, damar shiga jami’a ga ’yam mata – lamari ne mai kyau. Domin wurin da mutum zai yi karatu, ya ƙara ilimi, ya bunƙasa, yawanci jami’a ne. Gaskiya ne a wajen jami’a mutum na iya karanta littafi, ya zama masanin ilimi, amma hakan ba safai ke faruwa ba. Matasa mata a cikin jami’a, mafi yawan lokaci, suna samun ƙarfin kwazo, ƙarfin hali wajen fahimtar ilimin zamani, kuma kwakwalwarsu tana buɗewa sosai. Haka a kan samari ma, ba za a ce ya ne ga ’yammata kawai ba.

(Jawabin Jagora a taron wasu mata masu tunani – 1377/07/18 (09/11/1998))

9. Ku Saurari Nasiha da Kulawar Iyaye

Ayyuka daban-daban suna gina halayya da kuma tabbatar da makomar matasa. Shawarata ga iyalai ita ce su taimaki ‘ya‘yansu su shiga ayyuka masu ma’ana. Ina ba da shawara ga ’yam mata su daina ganin bukatun iyaye a matsayin wani abu mai hana su ci gaba. Ni ina kallonku ne a matsayin 'ya'yana, kuma nasihata ta fito ne a matsayin uba. Ku yarda da ni, mafi yawancin lokuta, iyaye sun fi sanin abinda yafi dacewa da ’ya’yansu fiye da yadda su kansu ke gani. Ku sani iyayenku masu kula da ku ne.

(Jawabin Jagora a taron tambayoyi da matasa a ranar 13 ga Bahman, rana ta biyu ta daular juyin-juya hali – 1377/11/13 (02/02/1999))

10. Ku Yi Hattara Kada Maƙiya su Yi Amfani da Raunin ku

Mutum, ko mace ko namiji, matashi ko tsoho, masani ko maras sani, duk suna cikin hadari. An ce "mukhlisun fi khatarin azim" (Mukhlisai na cikin babban hatsari). Komai irin matsayinku, dole a kula. Maƙiyan duniya da lahirar mu, maƙiyan mutunci da addininmu, suna kokarin amfani da rauninmu: son sha’awa, fushi, son mulki, sha’awar nuna kai. Yakamata mu kiyaye, haka ma ‘yan mata da matasa mata.

(Jawabin Jagora a taron mawaƙa na ƙasa – 1391/02/23 12/05/2012)

11. Nuna Kai Neman Suna yana da Illa Mai Dorewa a Jama'a

Domin samun nasara a lahira da kuma kare mutunci da cigaban ƙasa, mata su kula da batun hijabi da kunya da bin dokokin addini. Nuna kai da so a rika haskakawa, haske ne cikin minti daya amma illarsa tana dashi akai-akai a rayuwar al’umma, al’ada da ma siyasa ma. Idan kula da kunya da dokokin addini yana da wuya, wannan wuya na dan lokaci ne amma amfani da shi mai dorewa ne ga mutum. Matanmu su dage da batun hijabi da kunya: wannan ne aikin su, girman su da kima su.

(Bayanan shugaba a gaban wasu mawaƙa na ƙasa – 1391/02/23 (12/05/2012))

12. Ku Yi Tunani da Bincike kan Ƙananan Lamurran Siyasar Duniya

Ina son matasamu, maza da mata, har da daliban makaranta, suyi tunani akan ƙananan al’amurran siyasa ta duniya kuma su nazarcesu. Ko da tafiyarku a bincike ba daidai bane, duk da haka! Tsoffin hannu ne suke so matasa da jami’a su zama marasa hulda da siyasa. Ƙasar da matasanta ba sa cikin harkokin siyasa, ba za su fahimci siyasar duniya da abubuwan da ke gudana ba. Ta yaya irinsu zasu ci gaba da kawo gagarumin sauyi a ƙasa? A kasashen da ake mulkin kama-karya, suna son jama’arsu su dinga zama shiru, ba su da ilimi kan siyasa.

(Jawabin Jagora a taron wasu dalibai – 1372/08/12 (03/11/1993))

13. Maƙiya Basu Son Samun Matasa Masu Kishin Addini da Musulunci 

Maƙiya basu son matasa maza ko mata da ke tafiya a kan tafarki mai tsarki da addini, da niyyar ƙarfafa duniyar Musulunci. Su na so ne a samu matasa marasa tsari, masu sha’awa da bin duniya. Saboda haka, matasanmu su dage su tsare kansu da tsarkin zuciya da ƙarfafa matakin su. Masa'ulai su dogara da wannan matasa masu imani. Tsayin daka na al’umma, alama ce ta ƙudurin Allah. Jami’an gwamnati kada su lura da hayaniyar maƙiya. Garin nasu ne, su mafita ne. Dukkan mutane, musamman matasa, su san kimarsu su dage wajen gyara kansu.

(Jawabin Jagora a taron matasan Ahwaz – 1382/05/08 (30/07/2003))

14. Ku Fuskanci  Muhimman Batutuwan Ƙasa da Mahimmanci

Muna da fata a kan matasanmu, maza da mata, cewa su kasance masu maida hankali da tsanaki kan muhimman batutuwan ƙasa. Ina ba da shawara kuyi tunani sosai kan wannan batun duka da muhimmanci, za ku ga ayyukan da ba su da amfani yawanci suna fitowa ne daga rashin muhimmanci da gaggawa.

(Jawabin Jagora ga ƙungiyoyin dalibai da fitattun dalibai – 1382/08/15 (06/11/2003))

15. Imani tare da aiki nagari shi ne mafi muhimmancin ginshiƙin ci gaba

Hakika, masoyana! Samari! ’Yan mata! Ku sani cewa imani tare da aiki nagari shi ne mafi muhimmancin ginshiƙi don samun ci gaba a wannan fage. Imani mai tsabta, mai haske, bayyananne, mai hujja da ma’ana — wanda albarkacin Allah, abubuwansa suna da yawa a cikin ilimin Musulunci — idan ya kasance tare da aiki, zai iya taimaka muku. Imani kaɗai ba tare da aiki ba, ba ya kai mutum ga nasara. Imanin da ke haifar da aiki, ladabi, da bin ƙa’ida; imanin da ba ya haɗuwa da sakaci da lalaci — irin wannan imani zai taimaka muku a rayuwar duniya, kuma ya taimaka wa makomar ƙasarku. Ku mai da hankali a kan wannan.

(Jawabin ganawa da dalibai da masu hazaka daga sassan ƙasa — 1384/07/03 (25/09/2005))

16. Muhimman shawarwari ga ’yar makarantar firamare

’Yata! Ki saurari iyayenki. Ki yi sallah da kyau. Ki dage wajen karatu.

(Amsar Shahidin Jagoran Juyin Juya Hali ga wasiƙar wata yarinya — 1377/06/30 (21/09/1998))

17. Ku taka rawa wajen kare mutunci da asalin ƙasa

Gaskiya ne cewa a yau ba batun kare iyakokin ƙasa da makami ba ne kamar da, ba lokacin yaƙin soja kai tsaye ba ne. Amma kare iyakokin identitin ƙasa yana nan; kare iyakokin mutuncin addini da Musulunci yana nan; kare iyakokin akida yana nan. Dukkanmu muna da alhaki. Matashin yau, ko da bai kasance a lokacin da ake tsaye gaban maƙiyi don kare gida da gari ba, a yau zai iya taka rawa a filin girmamawa da ɗaukaka — wajen kare mutuncin ƙasa, darajar ƙasa, identitin ƙasa, da tsayayyen imanin Musulunci. Samari da ’yan mata, mata da maza masu imani, a wannan fagen kariya mai matuƙar muhimmanci na yau, kowa na iya taka rawa. Dole ne a kiyaye wannan ruhi. Masu alhakin wannan yanki su lura cewa akwai irin wannan arziki na ɗan Adam, na ruhaniya da na ƙima a wannan yanki — kamar yadda akwai albarkatun zahiri.

(Jawabi a taron jama’ar Gilan ta Yamma — 1390/07/23 (15/10/2011))

18. Ku tsaya tsayin daka a gaban ruɗu da tallan sha’awa na maƙiyi

Daya daga cikin dabarun maƙiya shi ne ƙoƙarin lalata waɗannan matasan namu masu tsabta, nagari, kuma masu kyakkyawar tarbiyya. Suna yin dubban ƙoƙari domin su lalata matasanmu — samari da ’yan mata. Ya wajaba matasan kansu su zama na farko wajen tsayawa tsayin daka a gaban ruɗu, rikitarwa da sharri na maƙiyi; su yi ƙarfi a gaban tallan sha’awa na maƙiyi da ke ruɗar da matasa.

(Jawabin ganawa da wasu ’yan sa-kai — 1372/08/30 (21/11/1993))

19. Ku kasance masu kuzari da ƙarfi a dukkan fannoni na rayuwa

Shawarata gare ku matasa — ’yan mata da samari — ita ce ku kasance a sahun gaba a dukkan fannoni na ayyukan matasa; a harkokin ilimi, karatu, bincike, siyasa, zamantakewa, al’adu, jarida, fasaha, wasanni da makamantansu, tare da cikakken kuzari da ƙarfi. Kuma ku kiyaye tsarkin hali, tsoron Allah, imani, ikhlasi da gaskiya — waɗanda hakika, cikin matasan duniya baki ɗaya, ku na daga cikin abin koyi ta wannan fuskar. Idan wannan ƙoƙari na imani, na ikhlasi da tsarkin zuciya ya yadu a tsakanin matasanmu, da kuma a tsakanin sauran jama’a — kowa gwargwadon matsayinsa — to lallai, ba shakka, masu girman kai da zalunci za su rushe ba sau ɗaya ba kawai, sai dai sau da dama, a gaban wannan al’umma. Babu wata shakka a kan haka.

(Jawabi a ganawa da daliban jami'a da ɗaliban makarantun sakandare— 1375/08/09 (30/10/1996))

20. Ku shirya kanku don gudanar da harkokin ƙasa

Matasa — maza da mata — dole ne su yi karatu kuma su kammala darussansu na makaranta. Wannan juyin juya hali da wannan ƙasa, naku ne; dole ne ku shirya kanku don gudanar da harkokin ƙasar. Wataƙila, in sha Allahu, nan gaba a cikinku za a samu maza da mata waɗanda za su ɗauki nauyi mai girma da nauyi a wannan ƙasa. Yaushe hakan zai yiwu? Lokacin da kuka yi karatu kuma kuka yi aiki. Kada a bari rashin aikin yi ya mamaye matasa. Kowa ya kamata ya yi aiki, ya yi ƙoƙari, kuma ya sha wahala; in sha Allahu ƙasar za ta bunƙasa.

(Jawabin ganawa da jama’ar yankin Delvar, Bushehr — 1370/10/13 (03/01/1992))

21. Ku mayar da muhallin jami’o’i da makarantu wurare na juyin juya hali da Musulunci

Ku ɗalibai — maza da mata — kuna ɗauke da nauyi mai girma. Bayan nauyin yin karatu, wanda shi ne aikin ɗalibi, kuna ɗauke da nauyin juyin juya hali, sannan kuma kuna ɗauke da nauyin addini da Musulunci. Ko a jami’o’i ko a makarantu. Wannan gwagwarmaya, ba ta yau ba ce, ba ta kwana ɗaya ko biyu ba ce, ba na shekara ɗaya ko biyu ba ce; gwagwarmayar tsararraki ce.

Wannan tsara da ta yi nisa da farkon juyin juya hali, idan tana son ta kai Iran ga ɗaukaka, ta gina ta, ta ba ta girma, ta kuma zama abin koyi mai rai ga sauran al’ummai, sannan ta wulakanta masu girman kai, to dole ne ta zama tsara mai juyin juya hali, mai Musulunci, kuma mai tsoron Allah; kuma wannan tsara ku ne. A yau kuna ɗalibai, kuma gobe ku ne za ku juyar da ƙafafun gudanar da wannan ƙasa. Ku gina kanku a yau. Ku gina jami’o’i. Ku mayar da muhallin jami’a muhallin juyin juya hali da Musulunci. Haka ma makarantun sakandare.

(Jawabin ganawa da ɗalibai, malamai, da ma’aikatan jinya — 1371/08/13 (12/11/1992))

 22. Ku rama koma-bayan da ƙasar ta yi kafin juyin juya hali da ilimi da kuma imani 

Ina fada muku matasa masoyana, maza da mata ’yan sa-kai (Basiji) masu imani, kowace ƙungiya kuke ciki: Masoyana! Ƙasar taku ce; ƙasar mallakar matasa ce; ku ne ya kamata ku gina wannan ƙasa; ku ne ya kamata ku kiyaye tushen ɗaukaka da girman da wannan juyin juya hali da hannun ginin juyin juya hali ya kafa, kuma ku ɗaukaka shi; ku ne ya kamata da ƙarfinku, da ƙudurinku, da iliminku, da imaninku, ku rama koma-bayan shekaru da dama na lokacin kafin juyin juya hali.

(Jawabi a taron ’yan sa-kai (Basiji) a sansanin horon al’adu da yaƙi na Yaran Imam Ali (AS) — 1379/07/29 (20/10/2000))

23. Ta hanyar shiga fagen bautar Allah, ku koyi sallah da dukkan hukunce-hukunce yadda ya kamata

A yau, ku ’yan mata masoyana kun fita daga duniyar ƙuruciya kuma ana ƙirga ku a cikin manya; domin sallah ta wajaba a kanku kuma dole ne ku yi sallah, ku bauta wa Allah, kuma ku yi magana da Allah Maɗaukakin Sarki. Ku daraja wannan lokaci mai daɗi na rayuwa kuma, in sha Allahu, ku koyi sallarku yadda ya kamata. Kada a samu yara mata masoyanmu waɗanda suka kai lokacin balaga, amma ba su iya sallah ba. Tabbas, na san kun iya sallah; amma dole ne ku koyi cikakkun bayanai na sallah ma. Dukkan ku ya kamata ku koyi kalmomin sallah, da addu’o’in da kuke faɗa a sallah, da motsin da kuke yi, da alwala, da tsarki, da ayyukan da suka wajaba don sallah, in sha Allahu.

(Jawabin bikin ranar Taklif na ɗaliban Bushehr — 1370/10/12 (02/01/1992))

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha