Alhamis 23 Afirilu 2026 - 23:46
Ƙarfin Iran Haɗin Gwiwa ne na Goyon Bayan Jama’a, Al’adar Ashura da Kuma Sauya Barazana Zuwa Dama

Hauza/ Hujjatul Islam Ahmad Yaghmaeiya bayyana cewa duk da matsin lamba mara misali daga manyan ƙasashen duniya, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta rikide zuwa mai tasiri a matakin yanki da duniya. Ya ce: "Asalin wannan ƙarfi shi ne hadin kan ƙasa, shigar da al’adun Ashura da kuma dogaro da matasa wajen sauya takunkumi zuwa damar ci gaba a fannin kimiyya da tsaro."

Hujjatul Islam Yaghmaei, Shugaban Makarantar Hauzar Waliyul Asr (AJ) a Tabriz, yayin hira da wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Hauza a Tabriz, ya jaddada rawar Iran a cikin tsare‑tsaren duniya cikin shekaru 47 da suka gabata, yana mai cewa: "Duk da matsanancin matsin tattalin arziki, takunkumi iri‑iri da barazanar soja daga manyan ƙasashen duniya, Iran ba ta karye ba, sai ma ta zama mai tasiri a harkokin yankin gabas ta tsakiya da duniya gaba ɗaya."

Ya ƙara da cewa: "Wannan ƙarfi ba kawai na soja ko tattalin arziki ba ne, yana da tushe mai zurfi a haɗin kan jama’a a lokutan tarihi masu muhimmanci. Daga lokacin yaƙin kariyar kai (Difa'e Muƙaddas), lokacin da matasan ƙasar suka tsaya tsayin daka duk da ƙarancin kayan aiki a gaban rundunar Iraki wacce manyan ƙasashe suka tallafawa, zuwa yau da ake cikin takunkumin tattalin arziki da yaƙe‑yaƙe ba su karya ruhin juriya (gwagwarmaya) na jama’a ba."

Ya bayyana halartar jama’a a gangamun jama’a, taron jana’izar shahidan gwagwarmaya da kuma dangantakar da mutane ke ji kan tsaron ƙasa a matsayin alamu na goyon bayan cikin gida. Ya kuma ce: "Al’adun Iran — musamman koyarwar Ahlul Bayt (AS) game da tsayuwa gaban zalunci da neman shahada — na ɗaya daga cikin ginshiƙan ƙarfinsu na ruhaniya."

Shugaban Hauzar Waliyul Asr ya ƙara da cewa: "Ma’anoni irin su adawa da zalunci da jihadi fi sabilillah — waɗanda tushensu daga Ashura ne — sun zama dabarun tsayuwa a gaban zalunci. Ya ce: "Shugabannin juyin juya halin Iran sau da dama sun jaddada cewa nasara tana cikin dogaro da ƙarfin Allah da al’adun addini. Kafuwar Ashura da juyin Imam Hussain (AS) ta zama jagorar juriya da aka sanya a cikin zukatan al’umma, kuma ta rikide zuwa dabarar rayuwa."

Ya jaddada cewa takunkumi maimakon raunana ƙasa, sun ƙarfafa dogaro da kai, yana mai cewa: "Abokan gaba sun yi zaton takunkumai za su karya Iran, amma sun zama dalilin ƙarfafa hazakar cikin gida da ci gaban kimiyya. A yau Iran ta kai ga babban ci gaba a fasahar makamai, jirage marasa matuki, nano‑technology da likitancin nukiliya."

Hujjatul Islam Yaghmaei ya ƙara da cewa: "Waɗannan ci gaban sun zama garkuwa gaban duk wata barazanar soja kai tsaye daga manyan ƙasashe, kuma Iran ta wuce iyakarta wajen yada akidar muƙawama (gwagwarmaya). A cikin wannan tsarin, matasan wannan zamani — da kwarin gwiwa daga matasan lokacin yaƙin kariyar kai — sun zama jagorori a fannin kimiyya, fasaha da al’adu."

Ya bayyana haɗin kan ƙasa a matsayin babban jarin Iran a gaban barazanar waje. Ya ce: "Abubuwan da makiya ke ƙoƙarin karya su, sune wannan ɗorewar haɗin kai, amma jama’ar Iran sun nuna cewa a lokutan ƙalubale, suna zama tsintsiya madaurinki ɗaya kan manufofin ƙasa". Ya ce: "Kafofin watsa labarai na abokan gaba na ƙoƙarin tayar da husuma, amma wayar da kan jama’a da fahimtar addini sun zama garkuwa mai ƙarfi."

Daraktan ya bayyana faɗaɗa tasirin Iran a yankin da kuma rikidewar kungiyoyin muƙawama zuwa ƙarfin tasiri a yammacin Asiya, yana mai cewa: "A nan gaba Iran za ta zama ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin kimiyya da fasaha a yankin da duniya."

Ya ƙara da cewa: "Ƙarfin Iran a gaban manyan ƙasashe sakamakon haɗin gwiwar goyon bayan jama’a, jagoranci mai dogaro da koyarwar Musulunci (Wilayatul Faƙih), da kuma mayar da barazana zuwa dama. Kwarewar Iran cikin shekara 47 ta nuna cewa al’umma idan ta tsaya kan ƙimomin ta, ta dogara ga kanta, za ta iya samun manyan ci gaba a mafi wahalar yanayi kuma ta zama abin koyi ga sauran al’umma. Wannan ƙarfin ba wai na soja kaɗai ba ne, haɗin gwiwar ƙarfi ne na al’adu da ruhaniya wanda ya kalubalanci tsarin siyasar duniya."

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha