Talata 3 Nuwamba 2026 - 15:48
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Aika da Amsar Wasiƙar Wani Ɗalibi ɗan Shekara 10 Tare da Kyauta

Hauza/ Wasiƙar da wani ɗalibi mai suna Alireza Bakhshi Irj, ɗan shekara 10 da ke zaune a birnin Tehran, ya rubuta wa Jagoran juyin juya halin Musulunci, ta isa hannun Jagoran, inda shi ma ya mayar masa da amsa cikin saƙo mai cike ƙauna da kulawa tare da aika masa da kyauta.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, a ranar 23 ga watan Shahrivar na shekarar 1405 (14 ga Satumba, 2026), Alireza Bakhshi Irj, wani ɗalibiɗan shekara 10, ya rubuta wasiƙa ta musamman ga Jagoran juyin juya halin Musulunci.

A cikin wasiƙar, ɗalibin ya bayyana ƙaunarsa da godiyarsa ga Jagoran bisa shawarwari da jagorancin da yake bayarwa. Haka kuma, ya aika da wani kuɗi a matsayin gudummawar godiya gare shi da kuma taimakon mayaƙan Musulunci.

Ga abin da wasiƙar ɗalibin ta ƙunsa:

Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Ƙai.

Assalamu alaikum, ya Agha!

Sunana Alireza Bakhshi, ina da shekara 10, kuma ina zaune a birnin Tehran.

Gaskiya ban sani ba ko wannan wasiƙata za ta iya isa gare ku ba ko a'a. Da ma ace zan iya ganinku ido-da-ido, mu tattauna. Gaskiya kuna bin mu bashin godiya mai yawa saboda shawarwarin da kuke ba mu.

Wannan kuɗin kuwa na bayar da shi ne domin nuna godiya gare ku da kuma taimaka wa mayaƙan Musulunci.

Ina fatan samun damar ganinku.

Mai ƙaunar ganinku,

Alireza Bakhshi Irj

23/6/1405

Ƙarin bayani: Barka da zagayowar ranar haihuwarku, duk da cewa na yi jinkirin taya ku murna.

Bayan wasiƙar ta isa hannun Jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamene'i, shi ma ya rubuta masa amsa domin nuna godiya ga ƙauna da kulawar da ɗalibin ya nuna masa. Haka kuma, ya aika masa da kyauta.

Ga fassarar cikakken saƙon amsar Jagoran:

Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Ƙai.

Abokina, abin ƙaunata, Alireza Bakhshi!

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Ina godiya gare ka bisa kulawa da ƙaunar da ka nuna mini. Sai dai ina so in sanar da kai cewa ranar haihuwata tana cikin watan Esfand ne. Ni ma ina miƙa maka wata kyauta, duk da cewa ba ta kai girman karamci da kyautatawar da ka nuna mini ba.

Ka isar da gaisuwata ga sauran 'yan uwa na iyalinka.

Sayyid Mujtaba Khamenei

19/Mehr/1405 (11 Oktoba 2026)

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha