A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Hujjatul-Islam Maliki, mataimakin shugaban Hauza Ilmiyya ta Qum, ya yi bayani kan ma’anoni da saƙonnin Suratul-Kauthar a cikin jerin darussa da yake gudanarwa.
A cikin nazarin Suratul-Kauthar, an kawo bayanai sama da 25 daga malaman tafsiri. Amma wani lokaci, idan aka mai da hankali ga waɗannan ra’ayoyi daban-daban, ana iya mantawa da ainihin dalilin saukar surar. Wasu sun bayyana cewa Kauthar na nufin Alƙur’ani, hikima, hankali ko tafkin Kauthar. Sai dai Suratul-Kauthar da kanta ta bayyana ma’anar wannan kalma, inda Allah Maɗaukaki yake cewa: «إِنَّ شَانِئَكَ هُوَ الْأَبْتَرُ».
Wannan aya da ke ƙarshen surar tana da alaƙa da dalilin saukarta. Maƙiyan Annabi (S.A.W.W.) sun kasance suna cewa, saboda ba shi da ɗa namiji, shi mutum ne wanda zuriyarsa za ta yanke, kuma babu wanda zai ci gaba da tafarkinsa bayan rasuwarsa.
Allah Maɗaukaki ya saukar da wannan sura ne domin ya yi wa Manzonsa bushara guda biyu masu ɗauke da mu’ujiza: ta farko, Allah zai ba shi Kauthar; ta biyu kuma, maƙiyinsa ne zai zama wanda ba shi da ci gaba ko abin da zai bar wa tarihi.
Saboda haka, an ba Annabi (S.A.W.W.) Kauthar, yayin da maƙiyansa suka kasa ci gaba da riƙe matsayinsu da tasirinsu a tarihi. Banu Umayya da Banu Abbas, duk da yawan magoya bayansu, ƙarfin da suke da shi da ɗimbin dukiyoyin da suka mallaka, sun kasa barin gado na ruhi mai ɗorewa irin na Annabi (S.A.W.W.).
A yau, ba ma ganin irin wannan ci gaba na ruhi ko matsayi a duniyar Musulunci daga waɗannan dauloli, amma sunan Annabi (S.A.W.W.) da tafarkinsa sun bazu a duk faɗin duniya.
Wannan ci gaba da yaɗuwa ya samo asali ne daga Ahlulbaiti (A.S.), sannan ya ci gaba a tsawon tarihi ta hannun manyan malamai, maraji’ai da fitattun mutane masu tasiri a duniyar Musulunci. Daga cikinsu akwai Imam Khumaini, Imam Shahid, Sayyid Hassan Nasrullah da Shahid Sadr, [Sayyid Zakzaky], waɗanda kowannensu ya yi tasiri mai muhimmanci a duniyar Musulunci a zamaninsa. Wannan shi ne ma’anar alkawarin Allah ga Annabi (S.A.W.W.) cewa an ba shi Kauthar, yayin da maƙiyinsa zai zama wanda ba shi da ci gaba.
Daga nan ne za a fahimci cewa ɗaya daga cikin fitattun misalai mafi cika na Kauthar ita ce Sayyida Zahra (S.A.). Kamar dai Allah Maɗaukaki yana yi wa Manzonsa bushara ne da cewa: Kada ka damu, za Mu ba ka Sayyida Zahra (S.A.), wadda daga zuriyarta Imam Hassan (A.S.), Imam Husain (A.S.), sauran ’ya’yanta, sannan a ƙarshe Imam Hujjat (A.F.) za su fito. Haka kuma, manyan malamai da fitattun mutane da dama za su bayyana daga zuriyar Annabi (S.A.W.W.) a tsawon tarihi, waɗanda za su cika duniya da ruhi da ilimin Annabi mai girma da Ahlulbaitinsa (A.S.).
Suratul-Kauthar gajeriyar sura ce, amma mai girman matsayi da ma’anoni masu zurfi. Saboda haka, Allah Maɗaukaki ya ce: «إِنَّا أَعْطَيْنَاكَ الْكَوْثَرَ فَصَلِّ لِرَبِّكَ وَانْحَرْ». Ma’ana: “Lallai Mun ba ka Kauthar. Saboda haka, ka yi salla domin Ubangijinka, kuma ka yi yanka.”
Tun da wannan ni’ima alheri ne mai yawa, kuma Sayyida Fatima Zahra (S.A.) tana daga cikin fitattun misalanta, wajibi ne a gode wa Allah Maɗaukaki bisa wannan babbar ni’ima, ta hanyar yin salla, yanka da sauran hanyoyin nuna godiya ga wannan baiwar Allah.
Baya ga wannan bushara, Suratul-Kauthar tana ɗauke da wani alkawari kuma, wato maƙiyan Annabi (S.A.W.W.) za su zama waɗanda ba su da ci gaba. A yau ma muna ganin yadda zuriyar Annabi mai girma take haskaka duniya, duk da cewa zalunci da duhu sun mamaye sassa da dama na wannan duniya.
Imam Khumaini ne ya kafa Kungiyoyin Gwagwarmaya, wadda take fuskantar manyan ƙasashe masu zalunci da masu girman kai a wannan zamani. Waɗannan mutane ba su da tausayi ko mutunta ɗan’adam, kamar yadda abubuwan da suka shafi tsibirin Epstein suka bayyana wasu munanan ayyuka da suka saɓa wa mutuncin ɗan’adam.
Daya daga cikin waɗanda suka tsaya tsayin daka a kan waɗannan manufofi, tare da ƙalubalantar ƙarfin masu aikata su, ya kasance daga zuriyar Annabi (S.A.W.W.) da zuriyar Sayyida Zahra (S.A.).
Wannan shi ne ɗaya daga cikin bayyanar gaskiyar Kauthar; ni’ima ce da za ta ci gaba da kasancewa. A kowane zamani, zuriyar Sayyida Zahra (S.A.) za ta ci gaba da tsayawa a gaban zalunci da danniya, ta wargaza duhun zalunci, tare da samar da yanayin da zai share fagen bayyanar ɗanta, Imam Hujjat (A.F.).
Saboda haka, ya kamata dukkan al’umma su yi tunani a kan wannan gajeriyar sura mai cike da ilimi da hikima, domin su ci gaba da riƙe bege ga makoma, nasarar gaskiya da tabbatuwar alkawuran Allah.
Ɗaya daga cikin saƙonnin wannan sura shi ne cewa maƙiyan Annabi (S.A.W.W.) da masu adawa da tafarkin Sayyida Zahra (S.A.) a kowane zamani za su fuskanci gushewa da halaka. Ba za a bar sunansu ko tasirinsu mai ɗorewa ba, kuma a ƙarshe za su shiga taskar tarihi ta waɗanda aka manta da su. Wannan ma yana daga cikin alkawuran da za a iya fahimta daga Suratul-Kauthar.
Ra'ayinka