A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, littafin “Muhawarori 101 Masu Ban Sha’awa da Ɗaukar Hankali”, wanda Muhammad Muhammadi Ishtihardi ya rubuta, ya tattara muhawarori daban-daban kan batutuwan aƙida da addini. Kamfanin Dillancin Labaran Hauza na ci gaba da wallafa waɗannan muhawarori a cikin jerin rahotanninsa.
Farkon Muhawarar Kan Hadisin Halifofi Goma Sha Biyu
Wani malami mai suna Dakta Khalid Nawfal ya kasance yana zuwa Jami’ar Shari’a ta Jordan domin koyarwa. Ni ɗaya ne daga cikin ɗalibansa, kuma ina bin mazhabar Shi’a. A wasu lokuta, saboda tsananin riƙo da mazhabarsa ta Ahlus-Sunna, malamin yakan yi wasu maganganu marasa tushe game da mazhabar Shi’a.
Wata rana, na zauna da shi domin tattaunawa kan magadan Manzon Allah (SAWA), waɗanda hadisi ya bayyana cewa su goma sha biyu ne. Ga yadda tattaunawar ta gudana, domin mai karatu ya ji sannan ya yi hukunci.
Malami: Ai babu wani hadisi a cikin littattafan hadisi da ya nuna cewa Annabi (SAWA) ya ce, “Halifofina goma sha biyu ne.” Wannan hadisi ƙirƙirarka ce kawai.
Ɗalibi: A’a, a zahiri, an kawo wannan hadisi a cikin ingantattun littattafan hadisi na Ahlus-Sunna, a wurare da dama kuma da lafuzza daban-daban. Misali, an ruwaito cewa Manzon Allah (SAW) ya ce:
«الْخُلَفَاءُ بَعْدِي اثْنَا عَشَرَ، بِعَدَدِ نُقَبَاءِ بَنِي إِسْرَائِيلَ، وَكُلُّهُمْ مِنْ قُرَيْشٍ.»
Ma’ana: “Halifofin da za su zo bayana goma sha biyu ne, daidai da yawan shugabannin Bani Isra’ila, kuma dukkaninsu daga Kuraishawa suke.” (1)
Saboda haka, wannan hadisi yana cikin littattafan da kuke ɗauka a matsayin amintattun madogara.
Malami: To, a ce mun yarda da ingancin wannan hadisi, a ganinku ku ’yan Shi’a, su wane ne waɗannan mutane goma sha biyun?
Ɗalibi: Bisa ɗimbin ruwayoyin da suka zo mana, waɗanda suka kai gomomi har ma da ɗaruruwa, sunayensu su ne:
* Amirul Muminin Ali bn Abi Ɗalib (AS).
* Hasan bn Ali (AS).
* Husaini bn Ali (AS).
* Ali bn Husaini Zainul Abidin (AS).
Haka dai har zuwa Imam na goma sha biyu, Hazrat Imam Mahdi (AF).
Shin Imam Mahdi (AF) Yana Raye?
Malami: Shin Imam Mahdi (AS) yana raye a yanzu?
Ɗalibi: Ƙwarai kuwa, yana raye, amma yana cikin gaiba saboda wasu dalilai. Idan yanayi mai kyau ya samu a duniya domin bayyanarsa, zai bayyana, ya karɓi jagorancin duniya.
Malami: To, yaushe aka haife shi?
Ɗalibi: An haife shi a shekara ta 255 bayan Hijira. Don haka, a lokacin da muke magana, wato shekara ta 1413 bayan Hijira, shekarunsa sun kai 1,158.
Malami: Ta yaya mutum zai rayu sama da shekaru dubu? Ai iyakar rayuwar mutum bisa dabi’a ita ce shekara ɗari.
Ɗalibi: Mu Musulmi ne, kuma mun yi imani da ikon Allah. Me zai hana Allah, bisa nufinsa, Ya sa wani mutum ya rayu na dubban shekaru?
Malami: Ikon Allah wani abu ne, amma irin wannan rayuwa ta saɓa wa tsarin da Allah Ya saba gudanar da al’amuransa a duniya.
Ɗalibi: Mu duka mun yarda da Alƙur’ani, kai da ni. A cikin Suratul Ankabut, aya ta 14, Allah Ya ce:
«وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوْمِهِ فَلَبِثَ فِيهِمْ أَلْفَ سَنَةٍ إِلَّا خَمْسِينَ عَامًا»
Ma’ana: “Lalle ne, Mun aika Nuhu zuwa ga mutanensa, sai ya zauna a cikinsu shekara dubu, in ban da shekaru hamsin.”
Bisa wannan aya, Annabi Nuhu (AS) ya zauna a cikin mutanensa tsawon shekaru 950 kafin ambaliyar ruwa. Saboda haka, idan Allah Ya so, zai iya sa wani mutum ya rayu tsawon wannan lokaci ko ma fiye da haka.
Bugu da ƙari, Manzon Allah (SAWA) ya yi bayani a wurare da dama game da zuwan Imam Mahdi (AF), wanda zai cika duniya da adalci bayan ta cika da zalunci. An ruwaito ɗaruruwan hadisai, har ma fiye da dubu, daga hanyoyin malaman Shi’a da Ahlus-Sunna dangane da wannan batu. Saboda haka, ba abu ne mai sauƙi a yi watsi da shi ba.
Misali, Manzon Allah (SAWA) ya ce:
«الْمَهْدِيُّ مِنْ أَهْلِ بَيْتِي، يَمْلَأُ الْأَرْضَ قِسْطًا وَعَدْلًا كَمَا مُلِئَتْ ظُلْمًا وَجَوْرًا.»
Ma’ana: “Mahdi yana daga cikin Ahlul Baitina. Zai cika duniya da adalci da gaskiya, kamar yadda ta cika da zalunci da danniya.” (2)
A wannan lokacin ne malamin ya fahimci cewa ɗalibin yana gabatar da hujjoji masu ma’ana, waɗanda ya danganta da madogaran da malaman Ahlus-Sunna suke amfani da su. Saboda haka, ya yi shiru.
Tambayar da Ta Sanya Malamin Cikin Ruɗani
Ɗalibi: Bari mu koma inda muka fara. Ka amince cewa Manzon Allah (SAWA) ya ce: “Halifofina goma sha biyu ne daga Kuraishawa.” Sannan ka tambaye ni su waye waɗannan halifofi goma sha biyun, sai na lissafa maka Imamai goma sha biyu, daga Ali (AS) har zuwa Imam Mahdi (AF).
Yanzu ni kuma ina tambayarka: A ganinka, su waye waɗannan halifofi goma sha biyun?
Malami: Daga cikin waɗannan mutane goma sha biyun, za mu iya lissafa halifofi huɗu na farko, wato Abubakar, Umar, Usman da Ali. Sannan Hasan (AS), Mu’awiya, Ibn Zubair da Umar bn Abdul Aziz. Waɗannan sun zama takwas.
Wataƙila za mu iya ƙara Mahdi Abbasiy, halifa na uku a daular Abbasiyawa. Haka kuma, watakila za mu ƙara Tahir Abbasiy.
A taƙaice, a fahimtarmu ba a fayyace waɗannan halifofi goma sha biyun dalla-dalla ba. Maganganun malamanmu a kan wannan batu sun bambanta, kuma akwai ruɗani a cikinsu.
Ɗalibi: Manzon Allah (SAWA) ya bayyana a cikin hadisin Thaqalain, wanda dukkan Musulmi suka amince da shi, cewa:
«إِنِّي تَارِكٌ فِيكُمُ الثَّقَلَيْنِ: كِتَابَ اللَّهِ وَعِتْرَتِي أَهْلَ بَيْتِي.»
Ma’ana: “Lalle ni zan bar muku abubuwa biyu masu nauyi: Littafin Allah, wato Alƙur’ani, da kuma zuriyata, Ahlul Baitina. Idan kuka yi riƙo da waɗannan biyun, ba za ku taɓa ɓacewa ba.” (3)
A bayyane yake cewa Abubakar, Umar, Usman, Ibn Zubair, Umar bn Abdul Aziz da Mahdi Abbasiy ba sa cikin zuriyar Manzon Allah da Ahlul Baitinsa ta fuskar nasabar da ake nufi a wannan hujja.
To, me ya sa za mu shiga ruɗani wajen tantance halifofi goma sha biyun Manzon Allah, alhali kuwa bisa hadisin Thaqalain, ya kamata su kasance daga Ahlul Baitinsa? Wannan kuwa ya yi daidai da aƙidar Shi’a game da Imamai goma sha biyu, daga Ali (AS) har zuwa Imam Mahdi (AF).
Malami: Ka ba ni lokaci domin in ƙara bincike a kan wannan batu. A yanzu, ban ga amsar da za ta gamsar da ni ba.
Ɗalibi: To, shikenan. Ina fatan binciken da za ka yi zai taimaka maka wajen gano su waye halifofi goma sha biyun Manzon Allah har zuwa Ranar Ƙiyama.
Bayan wani lokaci, malamin ya sake haɗuwa da ɗalibin. Duk da cewa ya yi bincike, bai samu amsar da ta fayyace halifofi goma sha biyun ba bisa fahimtar da yake da ita ta Ahlus-Sunna.
Madogaran Hadisan da Aka Ambata
1. Sahih Muslim, Kitabul Imara, juzu’i na 4, shafi na 482, bugun Darush Sha’ab; Musnad Ahmad, juzu’i na 5, shafuka na 86, 89, 90 da 92; Al-Mustadrak alas-Sahihain, juzu’i na 4, shafi na 501; da Majma’uz Zawa’id, juzu’i na 5, shafi na 190.
2. Musnad Ahmad, juzu’i na 3, shafi na 27.
3. Musnad Ahmad, juzu’i na 4, shafi na 367; Sahih Muslim, juzu’i na 2, shafi na 238; Sahih Tirmidhi, juzu’i na 7, shafi na 112; da Kanzul Ummal, juzu’i na 7, shafi na 112.
Ra'ayinka