Laraba 7 Oktoba 2026 - 22:37
Ayoyin Rayuwa | Tsarin Alƙur’ani na Magance Matsin Tattalin Arziki da Samar da Sauƙi a Rayuwa

Hauza/ A wasu lokuta, al’umma da masu ruwa da tsaki a harkokin gudanarwa, waɗanda ke damuwa da yadda za a cimma manufofin zamantakewa, al’adu da tattalin arziki, kan ga kansu cikin ƙunci da matsewar hanyoyi sakamakon takunkumai da ƙiyayyar maƙiya. Wataƙila hakan ya sa su shiga cikin rashin tabbas wajen gudanar da al’amura; alhali kuwa Mahalicci kuma abin bautar wannan duniya ya gabatar da wata hanya mai warkarwa.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza | Allah Maɗaukakin Sarki yana cewa a cikin Alƙur’ani Mai Girma:

«وَلَوْ أَنَّ أَهْلَ الْقُرَیٰ آمَنُوا وَاتَّقَوْا لَفَتَحْنَا عَلَیْهِمْ بَرَکَاتٍ مِنَ السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ وَلَٰکِنْ کَذَّبُوا فَأَخَذْنَاهُمْ بِمَا کَانُوا یَکْسِبُونَ.»

“Da a ce mutanen garuruwa da ƙauyuka sun yi imani kuma suka yi ji tsoron Allah, da mun buɗe musu albarkatu daga sama da ƙasa. Amma sai suka ƙaryata, sai Muka kama su saboda abin da suka kasance suna aikatawa.” (Suratul A’araf, aya ta 96)

Bayani:

A wasu lokuta muna tunanin cewa, domin samun ci gaban al’umma, abin da ya kamata kawai shi ne mu mayar da hankali kan tattalin arziki, samar da kayayyaki, jari da abubuwan more rayuwa na zahiri. Amma a mahangar addini, tushen yawancin albarkatun rayuwa ya kamata a nemi shi wajen gyaran mutum da al’umma.

Al’ummar da aka ƙarfafa imani, taƙawa, kyawawan ɗabi’u da ruhaniya a cikinta, ba wai za ta samu ci gaba ne kawai ta fuskar ruhi da ma’anar rayuwa ba; a’a, wannan ci gaba na iya bayyana tasirinsa a rayuwar tattalin arziki da zamantakewar al’umma ma.

Wannan aya da ake magana a kanta na iya sauya yadda muke kallon al’amura da irin matakin da muke ɗauka, musamman masu gudanar da al’amuran al’umma, wajen ƙarfafa al’adun addini a rayuwar mutane, ta fuskar mutum ɗaya da kuma zamantakewa. Ya kamata kowa, musamman masu kula da harkokin al’adu a kowace al’umma, su fahimci cewa saka hannun jari wajen ƙarfafa imani da kyawawan ɗabi’un mutane ba wai saka hannun jari ne na lahira kawai ba; a’a, yana iya zama sanadin bunƙasa rayuwar duniya da kuma ci gaban al’umma.

Gwargwadon yadda mutane za su kasance masu riƙon amana, adalci, sauke nauyin da ke kansu, nisantar zalunci da ha’inci, kiyaye haƙƙin wasu da kuma tsoron Allah, haka al’umma za ta ƙara samun kariya daga matsalolin da ke haddasa ɓarnatar da dukiyarta da ƙarfin mutanenta. Saboda haka, al’ada da ruhaniya ba abubuwa ne da suke a gefe daga rayuwar al’umma ba; a’a, suna daga cikin muhimman ginshiƙan samun farin ciki, ci gaba da bunƙasar al’umma.

A wasu lokuta, al’umma da masu gudanar da al’amuranta, waɗanda ke damuwa da yadda za a cimma manufofin zamantakewa, al’adu da tattalin arziki, kan samu kansu cikin ƙunci da matsewar hanyoyi sakamakon takunkumai da ƙiyayyar maƙiya. Wataƙila hakan ya sa su shiga cikin rashin tabbas wajen gudanar da al’amura; alhali kuwa Mahalicci kuma abin bautar wannan duniya ya gabatar da wata hanya mai warkarwa; hanya mai suna “taƙawa”.

Saboda haka, maganar Amirul Muminina Ali (AS) game da wannan hanya ta ruhaniya ta shahara sosai. Ya ce:

«لَوْ أَنَّ اَلسَّمَوَاتِ وَ اَلْأَرْضَ کَانَتَا عَلَی عَبْدٍ رَتْقاً ثُمَّ اِتَّقَی اَللَّهَ لَجَعَلَ لَهُ مَخْرَجاً وَ یَرْزُقْهُ مِنْ حَیْثُ لاٰ یَحْتَسِبُ.»

“Da a ce sammai da ƙasa sun kasance a rufe ga wani bawa, sai ya ji tsoron Allah, to, lallai Allah zai samar masa da hanyar fita, kuma Ya azurta shi daga inda bai yi tsammani ba.” (Ghurarul-Hikam, juzu’i na 1, shafi na 568)

Saboda haka, mayar da hankali kan yaɗa koyarwar Allah da gina al’adun addini a cikin al’umma ba wai kawai zai samar da albarkatun lahira ba ne, har ma zai iya kawo sauƙi da buɗewar hanyoyin rayuwa ta duniya ga al’umma.

Hakika, rashin kulawar mutane da masu gudanar da al’umma wajen aiwatar da al’adun taƙawa a rayuwar mutum da kuma rayuwar zamantakewa zai iya jefa mutum da al’umma cikin matsaloli da ƙuntatawa masu yawa, na zahiri da na ruhaniya.

An shirya wannan bayani ne a Sashen Ilimi da Al’adu na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha